Me ya sa mutane suke sumbatar juna?

Hakkin mallakar hoto thinkstock

Wani sabon bincike ya gano cewa kusan rabin yawan al'ummar duniya ba sa sumbatar junansu ta lebe da lebe. Dabbobi ma ba kasafai suka damu da abin ba. To ta yaya abin ya samo asali?

Melissa Hogenboom ta bincika.

Idan ka yi tunani a kansa za ka ga sumba wani bakon abu ne, kuma yana da dan rashin dadi. Kana shan yawun wani, har tsawon lokaci a wani sa'in. Sumba daya ka iya sa mutum ya dauki kwayoyin bakteriya (bacteria) miliyan 80, kuma ba dukkansu ne ke da kyau ba.

Amma duk da wannan, kusan kowa yana iya tuna sumbarsa ta farko, yadda ya ji kunya da bai iya ba, da dadin da ya ji, kuma har yanzu sumba na cigaba da taka babbar rawa a tsakanin sabbin masoya.

Ko ba a ko ina ba dai, akalla a tsakanin wasu al'ummomin, sumba na taka wannan rawa.

Al'ummar kasashen Turai za su iya dauka cewa sumba ta soyayya wata dabi'a ce ta mutanen duniya baki daya, amma wani sabon nazari ya nuna kusan kasa da rabin yawan al'ummar duniya ne kawai su ke yi. Haka kuma abu ne ma da kusan yawancin dabbobi ba sa yi, ba su san shi ba.

To idan haka ne me ya jawo wannan dabi'a ta daban? Idan tana da amfani, me ya sa dukkanin dabbobi ba sa yinta, da kuma dukkanin mutane su ma?

Kasancewar yawancin dabbobi ba sa yin dabi'ar, hakan ya taimaka wajen sanin abin da ya sa wasu ke yi.

Hakkin mallakar hoto Getty

Kamar yadda wani sabon bincike kan son dabi'ar ta sumba, wanda ya duba al'adun al'ummomi 168 a fadin duniya ya nuna, kashi 46 ne kawai su ke al'adar kamar yadda aka san ta.

Binciken ya kawar da yaddar da aka yi a baya cewa, dabi'a ce kusan ta mutanen duniya baki daya.

A baya an yi kiyasin cewa kashi 90 cikin dari na al'ummar duniya na yinta.

Wannan sabon binciken ya fitar da sumbar da iyaye ke yi wa 'ya'yansu daga ciki, inda ya mayar da hankali kan sumbar da masoya ke yi wa juna ta lebe da lebe.

Rayuwar al'ummomi da dama da suka dogara ga sana'ar farauta ba ta nuna alamar sanin sumba ba ko ma son yinta ba.

Hasali wasu ma sun dauke ta alama ta bijirewa al'ada, kamar yadda aka ruwaito cewa 'yan kabilar Mehinaku na Brazil sun dauke dabi'ar a matsayin batsa.

Mutane sun rayu a gamayyar taron mafarauta a yawancin zamanin rayuwar dan adam, kafin a kirkiro noma a kusan shekara 10,000 da suka wuce.

Idan har al'ummomi da suka yi rayuwar yawon farauta a zamanin kusa-kusan nan ba su yi dabi'ar sumba ba, ba zai yuwu ba a ce kakanninmu na zamanin da sun rika sumbatar junansu ba su ma.

Sai dai ba za mu iya tabbatar da hakan ba domin al'ummomi mafarauta na zamanin kusa-kusan nan ba su yi rayuwa kamar ta kananinsu ba, saboda rayuwarsu ta sauya tare da daukar sabbin dabi'u a yanzu.

Duk da haka, nazarin ya yi watsi da daukar da aka yi cewa sumba kusan dabi'a ce ta al'ummar duniya, kamar yadda jagoran masu binciken William Jankowiak na jami'ar Nevada da ke Las Vegas ya ce.

Ya ce a maimakon haka dabi'a ce da ta samo asali daga kasashen yammacin duniya na Turawa, ta wadda ta kawo har zuwa yau.

Akwai alamu na tarihi da za su tabbatar da hakan.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Sumba kamar yadda mu ke yinta a yau, ga alama kirkira ce ta zamanin nan in ji Rafeal Wlodarski, na jami'ar Oxford a Biritaniya.

Ya yi bincike mai zurfi domin gano shedar yadda dabi'ar ta sauya.

Dadaddiyar alama ko shedar dabi'a mai kama da sumba ta fito ne daga rubuce-rubucen Indiya na da (Hindu Vedic Sanskrit ) daga shekara 3,500 da ta gabata.

An bayyana sumba a matsayin hanya ta shakar ran juna.

Sabanin haka kuma a zane-zanen tarihi na kasar Masar abin da aka gani shi ne mutane kan tsaya kusa da junansu maimakon hada lebansu.

To me ya ke faruwa ne? Sumba aba ce da daman aka halicce mu da ita tun asali, amma wasu al'ummomin su ka yi watsi da ita? Ko kuma wata aba ce da mutanen zamanin nan suka kirkiro?

Za mu iya gano wasu bayanai idan muka kalli dabbobi.

'Yan uwanmu na kusa wato birai suna sumbatar juna. Masanin ilimin birai Frans de Waal na jami'ar Emory a Atlanta da ke Georgia a Amurka ya ga wurare da dama inda birai ke sumbata da rungumar junansu bayan sun yi rikici.

A iya saninmu sauran dabbobi ba sa sumbata sam-sam.

A wurin gwaggon biri da sauran birai sumbata wata hanya ce ta sasantawa bayan rigima. An fi yi tsakanin maza ban da mata. Ma'ana wannan ba dabi'a ba ce tsakanin masoya.

Akwai kuma wani jinsin birin (bonobos) wanda su kuma a tsakaninsu su ke yawan sumbatar juna, kuma suna amfani da harshe a sumbatar.

Wannan kila ba abin mamaki ba ne idan muka duba cewa shi wannan jinsin biri na da matukar sha'awa ta jima'i.

Idan mutane biyu suka hadu mu kan iya gaisawa ta musabaha (da hannu). Su kuwa wadannan birai (bonobo) su kan yi jima'i ne; kusan a ce gaisuwarsu ke nan.

Haka kuma suna amfani da jima'i domin kulla dangantaka ta wasu abubuwan da dama.

Saboda haka sumbatar da su ke yi wa juna ba lalle ta shafi soyayya ba ne su ma.

Wadannan nau'ukan biran biyu da muka bayyana kusan su kadai ne muka san suna sumbatar juna a iya saninmu, sauran dabbobi ba sa yi ko kadan.

Za dai su iya hada jiki ko gama fuska, to amma ko su wadanda su ke da lebba ba sa tsotsar lebe ko yawun juna. Ba sa bukatar yin hakan.

Hakkin mallakar hoto Blickwinkelalamy
Image caption Macen aladen dawa za ta iya sanin namijin da za ta fi jin dadin saduwa da shi daga sumbatarsa

Dauki misalin aladen dawa, mazan sukan fitar da wani wari ko kanshi da ke matan su ke matukar so, wanda ya ke jan hankalinsu.

Sinadarin (pheromone) da ke haifar da wannan wari ko kanshi (androstenone) ya kan sa mata su ji sha'awar jima'i da mazan.

Yawanci dabbobi su kan fitar da wannan sinadari mai sa sha'awar saduwa (pheromone) a fitsarinsu.

Ita mace (dabba) tana iya jin wannan wari ko kanshi sosai, saboda haka ba ta bukatar har sai ta je kusa da namiji ta sumbace shi.

Haka wannan abu ya ke a wurin dabbobi da yawa da su ke shayarwa (mammals).

Misali, tamatar wani nau'in bera (hamsters) da a ke samu a Turai da arewacin Asiya, ta kan fitar da wannan sinadari da ke jawo hankalin maza.

Haka shi ma bera yana amfani da wannan hanya ta fitar ta wannan sinadari domin ya taimaka masa gano tamatar da ba shi da dangantaka ta jini da ita domin rage hadarin saduwa da wata 'yar uwarsa ko wadda su ke da dangantaka ta kut da kut, kamar kanwa ko 'ya ko uwa.

Yawanci dabbobi suna fitar da wannan sinadari a fitsarinsu. ''Fitsarinsu yana da zarni sosai,'' in ji Wlodarski. ''idan akwai fitsari a wuri za su iya gane wadda ko wanda ya da ce su sadu da juna.''

Ba dabbobi masu haihuwa da shayar da 'ya'yansu nono ba ne kadai su ke da karfin zarnin fitsari na fitar da wannan sinadari ba.

Namijin wani nau'in gizo-gizo (black widow spider) yana iya jin zarnin wannan sinadari da tamatarsa ke fitarwa.

Wanda ta hakan yakan iya gane idan ta ci abinci a nan kusa ko ba ta ci ba, domin rage masa hadarin fadawa hannunta ta cinye shi, zai sadu da ita ne kawai idan ba ta jin yunwa.

Hakkin mallakar hoto Visuals UnlimitedNPL
Image caption Bakin gizo-gizo na iya jin kanshin matarsa daga nesa idan tana bukatar saduwa

Abin da a vke kokarin nunawa a nan shi ne cewa, dabbobi ba sa bukatar su kusanci junansu (sumbatar juna) su ji kanshin aboki ko abokiyar saduwa.

Amma su kuwa mutane suna da wata dabara ta son jin kanshi( don sanin juna), saboda haka mukan amfani juna ta hanyar kusantar junanmu.

Ba ta hanyar jin kanshi ba ne kadai mu ke iya sanin dacewa da junanmu ba, amma dai bincike ya nuna hakan na taka muhimmiyar rawa wajen zabar aboki ko matar da za ku sadu.

Su ma maza (mutane) suna da yanayi irin na fitar da wari ko kanshin wannan sinadari da alade kan yi domin jawo hankalin matar da ya ke so ya sadu da ita.

Wani bincike da aka wallafa a 1995 ya nuna cewa mata su ma kamar beraye sun fi son kanshin mazan da ba danginsu ba.

Wannan na nufin cewa saduwa da wanda ba ku da dangantaka da ita zai fi haifar da 'ya'ya masu lafiya.

Saboda haka sumba wata hanya ce babba ta kusantar juna domin sanin kanshin kwayoyin halittar abokin saduwa.

A shekara ta 2013 Wlodarski ya yti nazarin hanyoyin daban-daban na sumbata.

Ya tambayi daruruwan mutane abin da ya ke da muhimmanci a wurinsu a lokacin sumbatar wani ko wata.

Sanin yadda wari ko kanshin mutum ya ke shi ne abin da mutane suka fi son su ji yayin wannan sumba kamar yadda binciken ya nuna, kuma amfanin hakan ya fi bayyana lokacin da mace ta ke daidai da daukar ciki.

Binciken ya gano cewa maza su ma suna da irin yanayin fitar da wannan sinadari na wari ko kanshin jiki wanda ke jan hankalin matar aladen daji zuwa namiji.

Wannan yana cikin zufar maza kuma idan mata suka ji shi ya kan dan kara tayar musu da sha'awa.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Giwaye suna nuna wa juna kauna ta sumba da hannunsu.

Fitar da wannan sinadari (pheromone) wata hanya ce mai muhimmanci da dabbobi masu shayarwa su ke amfani da ita wajen zabar abokan saduwarsu, in ji Wlodarski, kuma mu ma muna amfani da wannan dabi'a.

Ya ce, ''mun gaji dukkanin dabi'unmu ne daga wadannan dabbobi, mun dai kara wasu ne kawai sakamakon sauyin yanayin rayuwar halitta na yau da gobe.''

A bisa wannan dalili sumba sai a ce wata karbabbiyar al'ada ko dabi'a ce kawai ta kusantar mutum domin sanin yadda wari ko kanshin wannan sinadari na jikinsa ya ke.

A tsakanin wasu al'ummomin, wannan al'ada ta sansanar juna ita ce ta ke kaiwa ga hada lebe.

Abu ne mai wuya ka ce ga lokacin da aka fara hakan, amma dukkanin hanyoyin biyu amfaninsu daya, in ji Wlodarski.

Saboda haka idan mutum na son samun matar da ta fi dacewa da shi ko mace tana son samun wanda ya fi dacewa da ita, za ku iya barin sumba kawai ku fara sansana jiki.

Ta haka za ka samu matar da ta dace sosai da kai ko namijin da ya fi dacewa sosai da ke, kuma ba tare da kun samu ko da rabin kwayoyin cutar da ke ke iya samu ba ta sumbatar juna.

Sai dai ka kwana da sanin irin kallo ko hararar da za a rika yi maka ko a yi miki.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Why do humans kiss each other when most animals don't?