Me ya sa dabbobi suke son yin wasa?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Za a iya ganin kamar yin wasa ba wani abu ne mai wani dalili ko muhimmanci na zahiri ba, to amma idan karnuka da sauran dabbobi suna wasa, to akwai darassu masu muhimmanci da suke koyo.

Jason G Goldman ya yi mana nazari

Mu kaddara kana dan tattaki da karenka a wani dan wurin shakatawa ko lambu, sai ya hadu da wani karen.

Nan da nan za ka ga sun dan fara 'yar wata rawa da dan wani kwance-kwance, kamar na neman makwantar juna, ko kuma kai wa juna hari.

Za ka ga suna shinshina juna, suna duba jikin juna, suna kuma kewaya juna.

Daga nan sai kawai a fara fada. To wannan fada ne na gaske ko kuma dai fadan wasa ne?

Yana da muhimmanci ga karen da shi ma mai karen sanin cewa ko karen na cikin wani hadari na gaske.

Yawanci masu ajiye karnuka a gidaje suna sha'awar fita tattaki na motsa jiki da karnukansu a lambu ko wani dandali domin su yi wasa.

To amma abin da karnukan ke yi wasa ne idan aka duba ko kuma wani abu ne daban?

Masana kimiyya kamar su James L. Gould da Carol Grant Gould sun yi amfani da kalmar wasa ne domin su bayyana duk wata dabi'a da ba ta da wani dalili na musamman na aikata ta.

Duniya na cike da irin wadannan misalai na aikin da ga alama ba shi da wani dalili akalla mu dai a fahimtarmu 'yan adam.

Masanan kimiyya na jami'ar Vermont Bernd Heinrich da Rachel Smolker sun kwatanta irin wannan dabi'a da wata tsuntsuwa (raven) mai kama da hankaka ke yi, inda za ka ga a yawancin lokaci suna sulu a dusara kanakara.

Wadannan tsuntsaye a Alaska da arewacin Canada sun yi fice wajen yin wannan sulu a kan rufin dakuna da ke da dusar kankara.

Za ka ga suna ta yin wannan abu, idan suka fado fado kasa, sai su sake tashi su hau kan rufin dakin su sake sulalowa.

Masana kimiyyar suka ce duk wanda ya je filin wasan na makaranta a irin wuraren da wadannan tsuntsaye suke zai gane cewa su da yara suna jin dadin wannan sulu da suke ta maimaitawa.

Akwai wani nau'in tsuntsun ma (herring gull), wanda shi ma yake son yin wannan wasa.

To amma su wadannan tsuntsaye na bakin teku suna cin wata kwara ce da ke cikin wani kwallo da suke yin wata dabara wajen fasa shi.

A dabararsu sukan dauki wannan kwallo ne su tashi sama da shi sai su sako shi daga sama ya fado kan wani fale-fale ko dutse, idan ya fashe sai su cinye abin da ke ciki.

A wani lokacin maimakon su wadannan tsuntsaye su bar wannan kawara ta fado ta fashe idan suka sako ta daga sama, sai su biyo su cafe ta.

Sauran tsuntsayen akin teku da yawa su ma suna yin wannan wasa.

Bayan da suka yi nazarin wannan tsuntsu (Herriing gulls) na kusan sa'o'i tamanin, masu binciken kimiyya, Jennifer R. Gamble da Daniel A. Cristol daga kwalejin William and Mary a Williamsburg, a Virginia, sun kirkiro wasu dokoki na wasa.

Masanan sun gano cewa kanana daga cikin wadannan tsuntsaye sun fi manya iya cafe kwarar.

Kuma sun gano cewa tsuntsayen sun fi yin wannan wasa a wuri maras tsandauri, mai taushi, wanda ba dutse ba, ko da kwarar ta fado ba za ta fashe ba.

Sannan masu binciken sun gano cewa tsuntsayen sun fi yin wannan wasa ko dabi'a idan ba wannan kwara mai fashewa suke dauke da ita ba.

Sun kuma lura cewa sukan yi wannan wasa ne na cafe,idan abin da suke dauke da shi ba kwarar ba ce.

Kuma kwarar da ake wasan cafen da ita ba lalle ba ne wadda za su ci ce.

Abu mafi ban sha'awa kuma shi ne, tsuntsayen suna yin wannan wasa ne, a lokacin da iska take kadawa sosai, wanda ya sa suke ganin kamar sun fi jin dadin wasan a wannan lokaci da ake ganin zai fi zama mai wuya.

Wannan ya sa masana kimiyyar ke ganin wannan wasa ne da tsuntsayen ke matukar jin dadinsa.

Dukkanin wadannan wasanni da tsuntsayen ke yi na sulu a kankara da kuma na cafe kwara, misali ne na wasan daidai (tsuntsu shi kadai), ba na tare ba, amma kuma duk da hakan akwai wasan da sukan yi a kungiyance.

Wannan ya sa muka dawo kan maganar fadan wasan da karnuka kan yi, idan suka hadu a wuri daya, wanda wannan wani nau'i ne na wasa mai muhimmanci da masanin dabi'ar dabbobi Robert Fagen ya bayyana da cewa, wata hanya ce ta sadarwa ta musamman.

Karnuka da danginsu na yanyawa sukan kwantar da kansu kasa (idan za su yi wannan karawa), wanda wannan wata alama ce da masanin tunanin dan adam Marc Bekoff ya kira kwanton wasa.

Wannan dukawa da dabbobin kan yi kamar sauran alamomi, na matsayin wata alama ce ta nuna cewa, ''e ina son mu yi wasa!''

Bayan haka kuma, wannan alama ce da har wa yau take nuna alamun cigaba da wasa.

Bekoff ya bayyana ya gano cewa suna wannan dukar da kai sosai kafin haduwa da kuma bayan an yi wani turmi ko zagaye na haduwar ko karawar wadda za a iya dauka kamar ba ta wasa ba ce.

Kanana da manyan karnuka sukan yi wannan dukawa ta wasa kafin da kuma bayan sun yi wasan cizo na bogi sau kashi 74 cikin dari.

Matasan yanyawa sukan yi hakan sau kashi 79 cikin dari, yayin da kananan kerkeci ke yin hakan sau kashi 92 cikin dari.

Abu ne mai sauki a ga cewa wani lokaci wasa yana da wata boyayyar manufa ko amfani.

Idan aka duba cewa kananan dabbobi sukan yi kwaikwayon abin da suka koya na fada da farauta ko kuma jima'i a yayin da ainahin bukatar hakan ta taso.

Wasa ya kan iya taimaka wa dabbobi su zama masu saukin kai da sassauci, kamar yadda Fagen ya nuna.

Inda ya ce, ''yana ganin kila yanayin yadda wasa yake, kamar yana shirya dabba ne ta san yadda za ta tunkari lamari idan ta samu kanta a wata rigima ko saduwa.

Saboda haka daga yanzu a duk lokacin da za ka wuce kusa da filin wasa ko harabara makaranta ka tsaya ka lura sosai.

Za ka ga kusan irin wasannin da yara ke yi sun yi kusan daidai da wadanda dabbobi ke yi, wato suna nishadi.

To amma wasu wasannin za su iya kasancewa da wata ma'ana ko dalili, kamar taimaka yara su san matsayinsu a cikin al'ummar da suke rayuwa.

Hakan kamar wani horo ne na samun kwarewa, idan bukatar hakan ta taso nan gaba a rayuwarsu, duk da cewa yaran ba su san da hakan ba.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Why do animals like to play?