Hanyar samun farin ciki a kwana bakwai

Hakkin mallakar hoto olivia howitt

A cikin 'yan mintina kadan za ka iya kawar da wani bacin rai da ke damunka idan har ka san dabarar yin hakan. Ga wasu daga cikin dabarun da aka jarraba a kimiyyance da za su iya taimaka maka magance damuwa.

Ga nazarin David Robson

A Cikin harkokin rayuwar yau da kullum, abu ne mai sauki ka samu kanka cikin damuwa da gundura da takaici.

Amma kuma duk da haka wasu mutane suna da karfin hali na juriya da kuma saurin bin wasu hanyoyin na rayuwa ka ga hatta a lokacin da ake tsammaninsu cikin wata damuwa za ka ga alamar ba abin da ya dame su.

Ta yaya mutanen ke yin haka? Yadda wasu mutanen ke da saurin bacin rai, akwai wasu hanyoyi da aka jarraba wadanda za su taimaka wa duk wani mutum ya yi maganin wata damuwa.

Yawanci wadannan dabaru ba sa daukar wani dogon lokaci, hasali ma 'yan mintina kadan kake bukata na jarraba su.

Kuma su yi maka amfani maras iyaka wajen inganta rayuwarka gaba daya da kuma jin dadinka.

A kwanan nan jami'ar California, Berkely ta sake tsarin wasu daga cikin fitattun wadannan dabaru a shafinsu na intanet (Greater Good in Action).

Mun zabi wasu daga cikinsu da muka fi so domin ka jarraba su a cikin mako daya kacal, don su taimaka maka kawar da damuwa.

LITININ

Hakkin mallakar hoto olivia howitt

Masu rubuta bayanan abubuwan da suka yi ko suka aiwatar ko suka faru da su ko wasu a duk rana ko kuma cikin wani lokaci,a wani dan littafi domin tarihi ko makancin haka, sun dade da sanin cewa rubuta wani abu da ya shafi rayuwarka zai iya sa ka yi maganin damuwar da abin ya haifar maka.

Sai dai a baya-bayan nan ne masana kimiyya suka gano muhimmancin wannan dan abu.

Daukar minti 15 kana nazarin wannan dan littafi naka zai iya rage maka damuwa da bacin rai, tare da karfafa garjuwar jikinka, da kuma bunkasa kokarinka a wurin aiki.

Za ka iya cin moriyar amfanin hakan har tsawon watanni. Kuma yin hakan ya fi ka bar abu a cikin ranka yana ta tafarfasa da ci maka rai.

Kamar yadda a wata kasida da Claudia Hammond ta BBC ta rubuta a baya bayan nan inda ta ce huce fushinka cikin fushi ba abin da yake haifarwa sai dai ya kara maka damuwa (Journal of Consulting and Clinical Psychology).

TALATA

Hakkin mallakar hoto olivia howitt

Za ka ga wannan kamar ba wani abu ba ne, ka rena shi, amma kuma yana tasiri; mutanen da suka jure wa yin wasu abubuwa na dan alheri guda biyar, akalla a rana daya a cikin mako daya, suna bayyana irin jin dadin da suke samu a sanadiyyar hakan a karshen gwaji na mako shida.

Yana daga cikin abin da ake gwaji da bincike akai wanda ke nuna cewa mutanen da suke da alheri da taimako sun fi samun farin ciki da lafiya (review of General Psychology).

WEDNESDAY

Hakkin mallakar hoto olivia howitt

Ka yi tunanin yadda rayuwarka za ta kasance ba tare da wani babban abokinka ba, (ko miji ko mata). Abu ne mai ciwo ko?

Amma duk da haka a wata kasida da aka wallafa a shekara ta 2008, an gano cewa mutanen da suke jarraba irin wannan rashi (su dauka kamar su riga sun rasa wannan aboki ko danuwa), can gaba su kan ji karin karfin zuciya.

Watakila hakan na sa su daina rena muhimmancin abokan nasu; tarin bincike da aka yi sun nuna cewa yawan godiya da wadatar zuci suna inganta rayuwa (wadata) (Journal of Personality and Social Psychology).

THURSDAY

Hakkin mallakar hoto olivia howitt

Masana kimiyya sun fara fahimtar amfanin ka samu wani buri ko dalili a rayuwarka, domin mutanen da suka dauki rayuwarsu a matsayin wadda take da wata ma'ana sun fi juriya da saurin daukar mataki idan wata matsala ta dan lokaci ta same su.

Bincike ya nuna cewa duba tsoffin hotunanka na baya, na daya daga cikin hanyoyin da za ka iya tunawa kanka irin muhimmancin da rayuwarka ke da shi.

Muhimmancin na iyalinka ne ko abokanka ko wani aikin jin kai ko kuma wani matsayi ka kai a rayuwarka.

Tunato da wasu tsoffin abubuwa na baya na iya taimaka maka ka fahimci abubuwa ko halin da kake ciki da kyau, wanda hakan zai iya kawar maka damuwar da kake ciki, idan ka yi waiwayen.

FRIDAY

Hakkin mallakar hoto olivia howitt

Idan harkokin yau da kullum suna dankwafe ka, abu ne mai sauki ka samu kanka cikin damuwa ta yau da kullum.

Wannan ne ma ya sa masana kimiyya suka fi mayar da hankali kan nazarin tasirin amfanin al'ajabi ko matukar tsoro.

Ko da kallon sararin samaniya ne cike da taurari ko halattar coci, jin matukar mamakin abun da ya fi ka girma sosai na fadada tunaninka.

Masana kimiyya sun gano cewa wannan yana sa mutane cikin farin ciki da rage zakuwa da ci da zuci, ya kuma sa mutum ya zama mai kaunar taimakon wani da rashin son kai.

Ko da daukar wasu 'yan mintina ka rubuta wani abu ko yana yi da ka shiga na ban al'ajabi zai iya taimakawa.

ASABAR

Hakkin mallakar hoto olivia howitt

Abubuwan da a da suke samu nishadi da ban sha'awa da jin dadi za su iya rasa wannan karsashi ko tasiri nasu a kanmu bayan wani lokaci, kamar mi ji sun gundure mu.

To za ka iya magance hakan, sannan kuma ka dawo da wannan dadi ko tasiri da abin ya ke yi a kanka, idan ka dakatar da amfani da abin, kamar abinci ko abin shan da ka fi so, na tsawon mako daya.

Bayan sati dayan za ka ga cewa ka dawo da wannan jin dadi kamar da lokacin ma abin yana sabo.

Amma a yanzu tsarin zai iya karfafa maka gwiwa ka jarraba wani abin daban da zai sa maka wannan nishadi da jin dadi (maimakon ka koma wancan na baya).

Idan kana ganin kaurace wa abin na mako daya, jan aiki ne da ba za ka iya ba, to sai ka jarraba wani matakin, na natsuwa sosai a lokacin da akke yin abin da yake sa ka nishadin.

Misalin idan kana shan gahawa ne, sai ka mayar da hankali kan dandanon da kake ji a harshenka.

Wannan ma an an gano cewa, yana iya taimaka maka ka san muhimmancin 'yan abubuwan da ke da dadi a rayuwa, da kuma kawar da damuwa.

LAHADI

Hakkin mallakar hoto olivia howitt

Akwai karin maganar Italiya da ke cewa, ''harshe na bugun inda hakori ke ciwo ne.''

Wannan maganar ta da ce da yadda zuciyarmu za ta iya mayar da hankali da tunani kan abin da ya yi mana ciwo ko bata mana rai a baya.

Sai dai abin takaici shi ne, masana tunanin dan adam sun nuna cewa damuwa ko jin da mutum ke yi, na wani laifi da ya aikata a baya, zai iya haifar masa da matsala.

Ba kawai zai zama wani sanadi na damuwa ba kadai da bacin rai, yanayi na rashin wani kyakkyawan fata da kwarin gwiwa, zai iya sa mu aikata wani abu maras kyau a gaba.

A bisa wannan dalili idan za ka yi kokarin daukar wasu 'yan mintina kana yi wa kanka tunani mai kyau, to wannan zai iya bunkasa farin cikinka ya kuma ba ka kudiri na yin abu.

Wasu za su ga kamar wadannan matakai romon baka ne kawai, amma idan za ka jarraba, za ka ga alfanun da ke tattare da su.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. A 7-day guide to the pursuit of happiness