Za ka zama likitan kanka nan gaba kadan

Hakkin mallakar hoto AP

Yadda ake samun cigaba a yau, za a kai ga likitanci ya zama kai da kanka ne za ka rika gwajin jini da yawu da sauran abubuwan jikinka, domin sanin halin da kake ciki, da abin da za ka yi.

Daga daudar kunne zuwa bayan-gida, abubuwan da jikinka ke fitarwa na dauke da sirri mai yawa

Linda Geddes ta yi mana nazari

Jini da zufa da hawaye: Me wadannan abubuwa suke bayyanawa game da kai? Tun tuni masana kimiyya da likitoci suka koma bincike a kan abubuwa dangin ruwa na jikin mutum domin sanin wasu abubuwa da suka shafi lafiyarmu.

To a yanzu dai masanan sun fara sanin cewa za su gano abubuwa da dama da suka danganci sirrin yadda jikinmu ke aiki fiye da yadda a da suka gano, kuma dadin dadawa ma abin yana kara sauki yadda kai da kanka za ka iya gwajin.

A wani lokaci BBC ta gabatar da labarain wata na'ura wadda za a iya amfani da ita nan gaba wajen gano alamar cutuka masu hadarin gaske kamar Ebola, tun kafin mutane su ma san sun kamu da kwayoyin cutar, kuma ba sai sun yi tafiya mai nisa ba kafin su samu na'urar.

Wannan ba ita kadai ba ce na'urar da za a iya amfani da ita wajen yin gwaje-gwaje masu wuya a wajen asibiti ba.

Akwai wasu na'urorin kamar wadanda ake kira ''Cue'' da Ingilishi, wadanda ake tallarsu yanzu, inda mutum da kansa zai iya yin amfani da su wajen yin gwajin ko yana da kwayoyin haihuwa da gwajin masassara da kuma alamun wasu cutukan.

Kuma akwai asusun X-Prize Foundation, wanda a yanzu ya sanya kyautuka domin samun wanda zai kirkiro na'urorin zamani na gwajin cutuka.

Ana sa ran a shekaru biyar zuwa goma masu zuwa za a samu karin irin wadannan na'urori da yawa, da kuma gano wasu sabbin hanyoyin samun bayanai a kan abubuwan da jikin mutum ke fitarwa.

Kamar yadda za ka yi tsammani da yawa daga cikin wadannan na'urori za su kunshi gwajin jini.

''A cikin jini kusan za ka iya gano duk wani abu da ka ci ko kuma bin da jikinka ke yi.'' In ji Guy Carpenter masanin kimiyyar halittu a kwalejin Kings da ke Landan.

George Preti masani a cibiyar nazarin kimiyya ta Philadelphia (monell Chemical Centre) cewa ya yi abu ne ma da zai iya yuwuwa a gano wasu hanyoyin na gwajin wasu abubuwan na jikin mutum ma.

A yanzu yana nazari a kan abin da daudar kunnenka za ta iya bayyanawa game da kai.

Ba kamar jini ba, daudar kunne tana da kauri, wanda saboda hakan wasu kwayoyin halittar za su iya kasancewa da yawa a nan, kuma da hakan za a fi saurin gano su fiye da a ce suna cikin wani ruwa maras kauri kamr jini.

Preti ya ce, ''idan akwai wasu rukunan kwayoyin da ke aiki a jikin mutum, wadanda ke narkewa a maiko za mu iya ganinsu a ruwa mai kauri kamar daudar kunne.''

Hakkin mallakar hoto Getty

Misali akwai wata matsala ta fitsari, wadda jikin mutane ba ya iya sarrafa wasu kwayoyin sinadari mai gina jiki (protein), wadda za a iya gano cutar ta hanyar shinshina daudar ta kunne.

A kwanan nan Pretin ya wallafa wani bincike da ya gano cewa daudar kunnen mutanen da suke 'yan asalin gabashin Asiya ta bambanta wajen wari da ta 'yan asalin Turai da 'yan Afrika da kuma 'yan Amurka, kamar yadda warin jikinsu ma ya sha bamban da na sauran mutane.

''Tuni mun riga muna gano cewa akwai alamar da ke nuna za a samu bayanin wata cuta daga shinshina daudar kunne.

Akwai ma bayani game da inda ka je da abin da ka ci. Abin jira a gani dai shi ne ko za a iya samun bayanan lafiya daga daudar kunne fiye da yadda ake samu a jini da sauran ruwan jikin mutum, amma dai ba mu sani ba sai mun bincika.'' Preti ya bayyana.

Akwai kuma zufa. Tsawon gomman shekaru da zufa ake amfani wajen jaririn da ke da matsalar da ke shafar daidaito tsakanin sidarin 'sodium' da kuma 'chloride' a ckin guminsu.

Yanzu akwai kayayyakin da ake kirkirowa wadanda 'yan wasan tsere za su iya daurawa a jikinsu, wadanda za su iya nuna musu, idan akwai wani sauyi a jikinsu da zai nuna suna gab da faduwa saboda ruwan jikinsu ya kare.

Wani amfani da lura da yadda zufa take shi ne, abu ne da za a iya yi cikin sauki.

Ba ka bukatar ka tsira wata allura a jikinka, ko kuma ka yi ta fama da auduga.

Abin da za a yi kawai shi ne a sanya wata 'yar na'ura a jikinta, daga kasan tufafinka, inda na'urar za ta rika aikawa da sako ba tare da wata waya a tsakani ba, ba ma tare da kai ka san ma me ke faruwa ba.

To amma gwajin zufar ma na da iyaka. ''Zufa tana dauke da wasu kwayoyi, amma sun bambanta sosai, wanda hakan zai iya sa ba za su shafi amfanin zufar ba kan lafiya,'' kamar yadda Jeremy Nicholson shugaban sashen nazarin kimiyyar kwayoyin halitta na kwalejin Imperial ta London ya bayyana.

Sannan 'yan mitsi-mitsin halittun da ke rayuwa a kan fatarmu ma na iya jirkita aikin sinadaran da zufar ta kunsa.

A daya fannin jini shi ne zai fi bayar da kyakkyawan sakamako na bincike, domin shi yana ratsa duk wata tsoka, kuma jiki yana kiyaye wa da duk sinadaran da ya kunsa ba tare da wani ya yi masa kutse ko shafar aikinsa ba.

Ko da daga digon jini kawai akwai bayanai masu yawa da za a iya samu fiye da yadda ake samu a yanzu.

Misali a yanzu Manfred Kayser na asibitin jami'ar Erasmus da ke Netherlands yana aikin kirkiro wata hanyar gwajin kwayoyin halitta na ''DNA'', wanda ta hanyarsa daga digon jini za a iya gane shekarar mutum da yadda kamanninsa ya ke da asalin yankin kasarsa ta ainahi, wanda hakan zai iya taimaka wa 'yan sanda gane wanda ake zargi da laifi ko kuma gawar da ta rufe sosai.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Wasu daga abubuwan ban sha'awa su ne yadda 'yan mitsi-mitsin halittun da ke rayuwa a jikinmu ke da tasirin samar da hasashe.

''Muna ganin wadannan 'yan halittu ne na jikinmu ke aikin sarrafa akalla kashi daya bisa uku na kayan abincin jikinmu da sauran sinadarai.'' In ji Tim Spector, Farfesa a kwalejin Kings da ke Landan, kuma marubucin littafin 'the Diet Myth'.

Kuma yanzu an gano cewa wadannan 'yan halittu suna tasiri a rayuwarmu sosai fiye da yadda a da aka dauka.

Misali a da an dauka kwayoyin halitta na kwakwalwa ne kadai suke samar da sinadarin da ke sauya yanayin mutum (damuwa ko farin ciki ko tausayi da sauransu), amma yanzu an gano cewa wasu kwayoyin baktiriya da ke cikin mutum su ma suna samar da wannan sinadari.

Kuma saboda haka ana ganin suna taka rawa wajen yanayin damuwa da mutum kan shiga.

Amma wurin da ya fi dacewa a duba domin sanin sauye-sauye a kan wadannan kananan halittu na jikinka , shi ne kashi.

Spector ya ce, ''idan ka bani kwayoyin halittar jikinka na DNA da kuma kashinka, zan fi sani kai waye daga nazarin kashinka.

Saboda duk da cewa kwayoyin halittar duk wasu mutane biyu sun kai kashi 99.9 bisa dari a kamanni, amma kuma muna da kashi 10 zuwa 20 cikin dari ne na kananan halittun na jikin namu da suke iri daya.

Kuma nazarin da aka yi a baya-bayan nan ya nuna cewa, irin 'yan mitsi-mitsin halittun da ke cikin jikinmu, da kuma kashinmu abin da muke ci da kuma inda muke zaune na tasiri a kansu.

Mai bincike ya ce, ''za mu iya gane bambancin Turawa da 'yan Afrika da mutanen Latin Amurka, kuma muna da bayanan farko daga 'yan biyu, da ke nuna mana bambanci tsakanin wadanda suke zaune a Scotland da kuma wadanda suke zaune a Ingila.''

Nazarin 'yan halittun da ke cikin kashin mutum da kuma sinadaran da halittun ke fitarwa, ba kawai zai iya taimaka wa wajen kara samun ilimin cutuka masu wuyar sha'ani, kamar damuwa da teba da cutar sukari ba, zai kuma iya nuna alamun gargadi na cewa mutumin da ya tsufa yana kan hanyar ramewa sosai, saboda haka yana bukatar samun karin kulawa.

Spector, ya ce, ''yayin da tsofaffi suke kara tsofewa jikinsu yana samun karin wasu daga cikin 'yan mitsi-mitsin halittun, ko kuma rashin wasu.''

Yayin da wadannan sabbin hanyoyin samun bayanan suke kara ingantuwa, kuma tsadar nazarin bayanan da za a samu daga garesu ke raguwa, ana kara samun kayan gwajin da mutum zai yi amfani da su da kansa, ba sai ya je wani asibiti ba.

Wasu na ganin wannan zai kara fadadawa tare da saukaka harkar kula da lafiya, sannan ya rage bukatar tashin mutane su tafi wani wuri a yi musu magani, da kuma ba wa mutane kwarewa da dama ta lura tare da daukar dawainiyar kula da lafiyarsu.

Haka kuma yanayin zai kawar da damuwar ba gaira-ba-dalili da mutane kan samu kansu a ciki da kuma gwaje-gwaje marassa inganci.

''Sai dai fa za mu iya ba wa mutane kayan gwajin abubuwa ko cutuka daban-daban, amma kuma fassarar sakamakon za ta bukaci jagorancin kwararren ma'aikacin lafiya.'' Kamar yadda Carpenter ya ankarar.

Haka kuma maganar kare sirrin mutum ma za ta kasance da muhimmanci a nan.

A halin yanzu dai 'yan kadan ne daga cikinmu muke damuwa ko mayar da hankali wajen sanin abin da ke faruwa da abubuwan da muke fitarwa daga jikinmu da zarar sun bar jikin.

Amma kuma nan gaba kadan ka kwana da sanin cewa, dan digon jininka da zufarka, kai har ma da daudar kunnenka za su zama abubuwan da ake buka kadai domin sanin tarin muhimman bayanai game da dabi'arka da lafiyarka da kuma jikinka.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan The future of medicine is testing our body fluids at home