Ka san abin da ya sa mutane suka fi wawanci a taro?

Hakkin mallakar hoto istock

Ba a ko da yaushe ba ne salon maganar nan da ke cewa 'kisan baki sai gayya yake zama da kyau ba', musamman a lokacin bayyana ra'ayi, domin mutane su kan dauki matsayin da bai dace ba, domin wasu sun zabi hakan.

Ga nazarin Micheal Bond

Yawanci masana kimiyyar tunanin dan adam ba za su taba zabar dakin kasa na benen gidan shan barasa na Landan, domin gudanar da aikinsu na bincike a kan yanke hukunci ko daukar matsayi kan wani abu da mutane kan yi ba, amma a wurin Daniel Richardson wurin shi ne ya fi dacewa.

Wannan masanin tunanin dan adam na jami'ar Landan, yana da sha'awar sanin yadda taron mutane ya ke tasiri kan ra'ayin wasu mutane a game da wani lamari.

Ma'ana idan mutum yana tare da wasu mutane, misali abokansa ra'ayinsa ya kan karkata ya zama daya da nasu, inda kusan dukkansu za ka ga sun dau matsayi daya a kan wani lamari.

A kan wannan dalilin ne mai binciken ya bukaci wurin tattaruwar jama'a na gaske, maimakon wani wuri na musamman na gudanar da bincike, inda ake lura ko sanya ido kan mutanen da za a yi binciken da su(dakin kimiyya).

A wannan dare kusan mu hamsin muka taru a dakin gudanar da wasannin kwaikwayo da sauran taruka na Phoenix da ke Soho a Landan (Phoenix Arts Club), domin shiga aikin nazari ko binciken da Richardson zai yi.

Kowa na cikin nishadi awurin, inda mai binciken shi kuma ya tsaya can a gabanmu ya tattare hannun rigarsa, kamar wani mai shirin gabatar da wasannin nishadi. Amma kuma fa aiki ne na kimiyya za a yi.

An hada kwamfutar kowannenmu ta yadda idan muka motsa wata alama ta digo a kanta za a ga wannan digon da muka motsa a wani makeken allon sinima da ke gaban dakin.

Kowa zai iya ganin tunaninmu na gaba daya a wannan allon na sinima (kuma Richard zai auna ya gani).

Idan kowa ya motsa wannan alamar digo a kwamfutarsa, sai a ga tarin alamar digo kamar kudan zuma, sun nufi wuri daya a kan wannan allo na sinima.

Hakkin mallakar hoto Getty

Bayan mun saba da tsarin sai ya yi tambayarsa ta farko: ''Ka taba sata ko magudin jarrabawa?''

Wadanda suka amsa 'a'a', sai suka tura alamar digon bangaren hagu, wadanda kuma suka ce 'e' suka tura dama.

Da farko kowa ya bayar da amsarsa ne shi kadai, inda aka boye alamar digon, wato ba a fito da ita ba a kan allon nan na sinima, inda kowa zai gani, daga baya kuma sai aka yi gaba daya, wato aka ga alamomin a kan allon.

Abin da Richardson yake son ya sani shi ne, ko yanayin biyu zai bayar da sakamako daban-daban.

Mun fi fadar gaskiya idan kowa shi kadai ya amsa ba tare da wani ya san amsarsa ba? Ko muna sauya matsayinmu mu bi na wasu?

To daga nan ne kuma sai aka fara ainahin aikin binciken, inda aka tambaye mu ra'ayinmu.

''Ya kamata Biritaniya ta fita daga kungiyar kasashen Turai EU,'' mai binciken ya fada.

Daga nan sai kusan dukkanin alamar digon (amsar ke nan a kan allon sinimar) sai ta yi gefen hagu wato a'a (ba su amince da maganar ba).

Magana ta biyu da masanin ya kawo, kuma domin bayar da amsar ita ce:

''Ya kamata doka ta haramta yajin aikin ma'aikatan jirgin kasa na karkashin kasa na Landan.'' Sai kawai alamar digon ta rika kai-kawo, muna neman inda aka fi yawa domin mu bi.

Sai kuma tambaya ko kalma ta uku: ''Duk wanda ya sai wa abokansa abinci yana da damar dibar mafi yawa.'' Sai kusan kowa ya yi tsaki a lokaci daya, sannan aka rika tura digon zuwa hannun hagu, wato an amince da wannan maganar.

To amma maganar ita ce mutum nawa ne a cikinmu suka ja ko kin amincewa a lokacin da aka boye alamar matsayin da kowa yake zaba?

Sai dai abin takaicin shi ne ba a bayyana sakamakon ba a wanna lokaci da muka yi jarrabawar( za a yi amfani da shi ne a wani rubutu na neman digiri na uku).

Amma dai Richardson yana ganin a karshe sakamon zai nuna yadda idan mutum yana tare da wasu mutane ya kan bi ra'ayinsu, maimakon kowa ya bi tunaninsa, wanda hakan kuma ba lalle ba ne shi ya fi dacewa ko basira kan na daidaiku.

Mai binciken ya ce, ''idan mutane suka hadu tare, sukan tafi a kan ra'ayi daya, wanda kuma sai ka ga ra'ayi ne maras kyau.''

''Ba wai bayani suke musaya a tsakaninsu ba, ra'ayi suke bi kawai. To muna kokarin fahimtar abin da ke sa hakan ne, da kuma yadda za mu sa ra'ayi na jama'a gaba daya ya zama ya fi yadda yake kasancewa.''

Wanna bincike na Richardson ya zo daidai da gwajin da aka yi shekara sama da 60 da ta gabata.

A shekarun 1950, masanin tunanin dan adam na jami'ar Harvard Solomon Asch, ya kwatanta yadda mutane a yawancin lokaci suke daukar ra'ayin bangaren mutanen da suka fi yawa, ko da kuwa ya bayyana ba daidai ba ne, kuma ko da a hankalinsu ba haka abin yake ba.

A dai wannan lokacin, Read Tuddenham na jami'ar California, ya gano cewa dalibansa za su bayar da amsa mai ban dariya a kan tambaya mai sauki.

Hakkin mallakar hoto Dean Hochman flickr cc 2.0

Ya bayar da misalin cewa, daliban za su ce jarirai maza suna da tsawon rayuwar shekara 25, idan suka dauka sauran dalibai haka suka amsa.

Ra'ayi irin na (inna rududu ko kowa ya karkata wuri daya) a bi yarima a sha kida, ya saba da ra'ayin da za a ce na yawanci mutane, inda idan aka tattara ra'ayin daidaikun mutane a taro ake samun na yawanci, amsar yawancin mutane a nan za ta fi zama daidai a kan ta wani mutum shi kadai.

Hakan na kasancewa ne idan kowane mutum a cikin taron ya bayar da amsa bisa ra'ayi da fahimtarsa ba tare da la'akari da ra'ayin wani ba, kuma hakan ya fi kasancewa idan tarin mutanen sun sha bamban.

A daya bangaren kuwa, a taron mutanen da suke da alaka daya (ba su bambanta ba), kishin samun hadin kai za ka ga ya sha gaban komai.

Saboda haka idan Richardson ya nuna mana hoton irin katon kifin nan da akan kira giwar ruwa (whales), ya tambaye mu, nawa muke ganin nauyinsa zai zama, zai fi dacewa ya yi amfani da amsar da ya samu daga kididdigar amsar yawancinmu, maimakon ya yi amfani da alamar digon da zai gani a allon sinimar nan, domin wannan kowa yana iya ganin amsar kowa, sai yawanci a bi inda aka fi karkata.

Wanna shi ne nazarin. Bayanin da za a samu daga wannan bincike na ganin amsa a allon sinima zai taimaka wa Richardson da dalibansa su gwada abin da suke son tabbatarwa a nazarin tare kuma da sanin yadda ainahin kasancewar wasu a tare da mu ke tasiri a kan ra'ayi da tunaninmu.

Malamin ya bar mu da tunanin yadda shafukan sada zumunta da muhawara suke a yau.

Ya ce, ''muna daukar intanet a matsayin wata babbar kafa ta ilimi da bayanai. Ba haka ba ne, babbar kafa ce kawai ta ra'ayi.

Shafukan Facebook da Twitter hanyoyi ne masu muhimmanci na musayar bayanai.

Sai dai mun dauke su hakan ne saboda sun ba mu damar musayar ra'ayoyinmu, amma a takaice suna kara sangartar da mu ne kawai.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Why people get more stupid in a crowd