Ka taba buge hannunka ya sage?

Hakkin mallakar hoto Getty

Ba zafin da ya fi wanda kake ji idan hannunka ya sage a duk lokacin da ka buge gwiwar hannun. To amma me ke sa hannun naka ya sage?

Jason G Goldman ya bincika mana

Kowa ya san cewa buge gwiwar hannu ba abu ne mai ban dariya ba, amma ka san cewa abin da kake ji idan hannun naka ya sage, wannan abin da kake ji ba daga kashin naka yake ba sam-sam.

A maimakon kashin jijiyoyin hannunka ne da suka bi ta gwiwar hannun suke sa ka ji wannan sagewa.

To shi dai kashin hannun naka ana kiransa ne kashin dariya (funny bone) da harshen Ingilishi, sai dai kuma ba a san dalilin da ya samu wannan suna ba.

Wasu na cewa sunan ya samu ne saboda wasa da kalmomi da aka yi, domin kashin da yake tsakanin gwiwar hannunka da kafadarka yana da suna da ya dangancin kalmar dariya (humerus).

Wasu kuwa suka ce ai an sanya masa sunan ne saboda abin da kake ji, idan ka buge a wurin, hannun ya sage.

To ba dai lalle ba ne musan asalin wannan suna na kashin, amma dai mun fahimci abin da yake sa ka ji ba dadi matuka idan ka buge shi.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Amfani da waya na tsawon lokaci ya kan iya yi wa jijiyar hannu illa

Jijiyar hannun ta taso ne daga laka ta bi ta kafada sannan ta tafi hannu, inda a hannun kuma ta kare a karamin dan yatsa da kuma yatsan da ake sa zobe.

Yadda tarin jijiyoyi suka bi ta hannunka, jerin kasusuwa da tsoka su kuma sai suka kare jijiyoyin da ke kai sako su kuma karba daga tsokar hannu.

Matsalar ita ce yadda jijiyar hannun ta bi ta gwiwar hannun ta wuce ta bi makamar kashin hannun ta ratsa ta wani rami mai tsawon mili mita hudu (4mm).

Daga nan kuma kafin kungurun kashin gwiwar hannun, akwai makata ko mahada wadda a nan ne kuma kasusuwan suka hadu.

A nan din ne dai jijiyar ta ratsa tsakanin kashi da fata, ba tare da wata ko 'yar shimfida da ta kare tsakanin kashi da fatar ba ko kuma wata kariya.

Saboda haka idan ka buge hannunka a daidai gwiwa kamar ka kara jijiyar ne a jikin dungun kashin da ke gwiwar hannun.

To idan hakan ya faru sai ka ji hannunka ya sage. Kuma saboda jijiyar ce ke jawo wannan ciwo ba ainahin kashin hannun ba, sai zafin ya mamaye duka hannunka inda ya ke karewa a karamin dan yatsa da yatsan zobe.

Wasu mutanen sukan dan shafa gwiwar hannun nasu ne na wasu 'yan mintina, sai ya farfado, su daina jin zafin ko sagewar.

Ka dauka kamar wani mutum ya rika bin ka yana ta kwakkwala maka wani abu kamar dan katako a gwiwar hannunka, wannan shi ne yanayin da ake ji idan mutum ya gamu da wata larura da zai ji hannunsa na sagewa akai akai.

Wannan larura ce da ke damun mutum da ciwo da rashin jin dadi, idan ta yi tsanani ma ta kan sa ya daina amfani da hannun.

Akwai dalilai da za su sa mutum ya gamu da wannan matsala ta sagewar hannu, ta dan lokaci ko kuma ta larura wadda ke aukuwa akai akai.

Matsalar kan faru idan ka yi ta tankwarar da gwiwar hannun kana kuma mikar da ita na tsawon lokaci.

Ko kuma idan ka tankwarar da gwiwar ka dade kamar idan kana amsa waya ko ka kwanta hannunka a tankware ko ka kwanta a kan hannun ma.

Yawancin likitoci su kan bi wasu hanyoyi na magance matsalar ba tare da yin tiyata ba, amma idan abin ya ki sai su yi aiki.

Hanyar da aka fi bi wajen maganin matsalar ita ce ta, barin yin abin da ke jawo sagewar hannun.

Idan mutum yana da dabi'ar tankwarar da hannunsa idan yana barci, zai iya sa dan wani zirin abu kafin gadon ko ya daura dan matashin kai ko tawul a gwiwar hannun nasa, domin kada ya takura hannun, ya zama a sake.

Wadanda amsa waya ke jawo musu matsalar, sai su rika bude lasifakar wayar, ta yadda za su rika magana da ji ba tare da sun kara wayar a kunnensu ba.

Wadannan na daga cikin hanyoyi masu sauki na yau da kullum da masu fama da matsalar ta sagewar hannu za su iya bi, kuma su samu sauki sosai.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Yawanci sagewar tana daukar dan lokaci ne kawai ta wartsake

Amma kamar yadda kungiyar likitoci masu tiyatar hannu ta Amurka, ta ce wani lokacin abin sai ya kai ga tiyata.

Wannan zai iya hada wa da sauya wa jijiyar wuri daga bayan gwiwar hannun zuwa gaba, ko kankare kashin ko ma gutsure shi domin ya daina matse jijiyar.

Matsalar ita ce har yanzu matsayar da ake da ita a kan tsarin tiyatar da ya fi kyau a tsakanin biyun kadan ce.

Wani nazari da aka yi a shekarar 1989 ya duba kasidoji na kusan shekara dari da aka rubuta, da wasu bayanai na masu fama da cutar su sama da 2000 da ke bukatar tiyata.

A cikin rahoton, wani likita na Baltimore, A Lee Dellon, ya nuna takaicinsa cewa, '' maganar yin magani ta shiga wani yanayi na rashin samun matsaya tun daga lokacin da likitoci suke ganin kusan kowace matsala ta cutar sagewar hannun sai an yi mata tiyata, saboda ba su ga wani da ya warke, ba tare da tiyata ba, zuwa yanzu da aka gano wasu, masu cutar za su iya warkewa ta hanyar da ba sai an yi aiki ba.''

Sama da shekara 25 da wannan, har yanzu 'yan abubuwa kadan ne suka sauya. Hatta a shekara ta 2014, masu bincike suna cigaba da gudanar da nazari, inda suke duba hanyoyi daban-daban na tiyata, don sanin wadda ta fi.

Kuma a farkon shekara ta 2015 wasu likitoci (masu tiyata) Prasad Sawardeker da Katie E Kindt da Mark E Baratz na babban asibitin Pittsburgh Allegheny sun ce, ''babu wani tsari na takamaimai na yin tiyatar matsalar, domin shedara da ake da ita kawo yanzu ba ta isa ta tabbatar da tsarin da ya fi dacewa ba.''

Saboda haka idan nan gaba ka bige a gwiwar hannunka da kujera ko kofar mota ko da wani abu, (hannun ya sage) kada ka damu, domin zai iya fin haka zafi ma.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Why does it hurt so much to hit your funny bone?