Shin taimakon bako na da amfani?

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A wasu shagunan shan shayi da gahawa, daruruwan mutane kan sai wa junansu, domin yada wannan dabi'a ta alheri

Masu taimako sun fi farin ciki da kuma lafiya a cikin jama'a, amma kuma duk da haka, yawanci a kan zargi mutum da wata muguwar niyya idan ya yi niyyar wani alheri, misali ba da abinci, ko rage wa mutum hanya a mota. Me ya sa haka?

David Robson ya tattauna da wata kwararriya kan tunanin dan adam, wadda ta yi kokarin gano amsar.

Za ka dauka cewa Sandi Mann na neman wanda zai yarda ta mare shi ne, ba wai kofin gahawa take neman wanda yake bukata ya karba ba.

Ita dai Sandi Mann ta saba zuwa wannan shagon sayar da shayi da gahawa ne kusan duk safiya, tare da 'ya'yanta, inda za su karya kafin ta kai su makaranta.

To shi karamin cikin 'ya'yan nata ba ya son gahawar da ake hado masa da kayan kwalan da makulashen, saboda haka sai dai ya cinye kayan ya bar gahawar. Saboda haka ne sai Sandi take ganin zai dace ta rika bayar da gahawar kyauta ga wasu da suke bukata a shagon.

Da ta bi tebur-tebur tana kokarin bayar da gahawar kyauta sai ta sha mamaki, yadda mutane suke yi mata wani irin kallo (na zargi ko reni?). Ta ce, ''na dauka za su karba cikin farin ciki da murna, amma sai na ga kusan kowa na ba wa sai ya bata rai.''

''Kamar suna zargin ko na tofa yawu a ciki ne? Ko kuma suna ganin na sanya wata guba ne''?

A karshe dai Sandi Mann, wadda kwararriyar malama ce ta nazarin tunanin dan adam a jami'ar Lancashire, ta fahimci cewa ba ta biyo hanyar da ta dace ba ne, shi ya sa ta gamu da wannan zargi.

Daga nan ne kuma, Sandi ta fara gudanar da sabon bincike a kan al'adar da ake cewa ''alheri danko ne ba ya faduwa kasa banza,'' (paying it forward), wadda ta kunshi yi wa wani bako ko mutumin da ba ka sani ba alheri, da zummar shi ma ya yi wa wani a gaba, ta yadda hakan zai sa mutane su dauki dabi'ar yin alheri ga wasu.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ba kowa za ka mika wa kyautar alewa ko wani abin ci ba ya karba

Dabarar Sandi, ita ce ta jarraba abin da kanta na dan wasu makonni domin ta ga yadda mutane za su yi. Domin ai daman mutane da yawa kila suna da aniyar taimako, amma dai ba kasafai suke da karfin halin yin ba.

To idan haka ne, me ya sa yake da wuya mutum ya bayar da taimako ko kuma ya karbi wani abin alheri, idan bai san wanda ya ba shi ba?

Yana kuma daga cikin abin da take son ganowa, ko yin alherin yana da wani amfani , ko dai zargi ya bi ya cika mu kan wani abin alheri da wani zai iya yi maka a hanya?

Duka wadannan abubuwan da ta gamu da su na dadi da bacin rai ta rubuta su a littafin ( Paying It Forward : How One Cup of Coffee Could Change the World), wanda ta wallafa kan wannan bincike nata.

Kamar yawancin mutane sha'awar Sandi kan gudanar da wannan bincike ta samo asali ne daga wani labari mai sosa rai da wata kawarta ta Facebook ta rubuta.

Kawar tata Debbie, wadda 'yar Amurka ce, ta dade tana zuwa wani shagon sayar da shayi da gahawa, amma kusan a duk lokacin ta aka zuba mata gahawar sai ta ji a n ce mata ai na gabanta ya biya mata.

Wannan labarin ya ratsa Sandi, daga nan ta fara tunanin yadda alherin mutum daya yake iya ratsa kusan duniya baki daya.

Da ta fara gudanar da bincike kan halin sai ta gano cewa abu ne da yake da dadadden tarihi, inda masu hali a kasar Italiya suka yi fice wajen saya wa mutanen da suke ganin ba su da hali kamar su gahawa ko shayi, idan suka je shagon sayar da gahawa.

Benjamin Franklin na daya daga cikin masu yada wannan dabi'a, inda a lokacin da yake ba wa wani abokinsa rancen kudi, sai ya gaya masa cewa, na ba ka rancen wannan kudi ne, domin idan ka hadu da wani mutumin mai gaskiya, wanda yake cikin irin wannan hali na bukata da kake ciki, ka biya ni ta hanyar ba shi bashin kudin.

Ya rubuta cewa,'' wannan wata dabarata ce ta yin wani alheri da wani dan kudi.''

A yau wannan dabi'a (''paying it forward'') ta zama wata sananniyar dabi'a mai matukar tasiri, wadda ta kai an rubuta littafi da yin fim a kanta.

Ka bincika ta a Google za ka sha mamaki da irin labaran da za ka gani masu sosa rai na taimako da alheri a sanadin dabi'ar, kamar yadda wasu masu taimakon da ba sa bayyana sunansu suke tura kudi asibiti domin biya wa marassa lafiyar da ke bukatar aiki mai tsada kudin aikin, ba tare da tsammanin a saka musu da wani abu ba.

Yawanci dai dan abin da bai taka kara ya karya ba ne ya fi ratsa rai. Sandi ta yi nuni da labarin Josh Brown, wani yaro dan shekara 12 wanda ya tsinci waya a jirgin kasa ya nemi mai wayar.

Mai wayar ta ji dadi matuka har ta aiko masa wani dan ladan kudi. Maimakon ya karbi kudin, sai ya rubuta mata wani sako ya hada da wayar ya aika da cewa,'' kada ki damu da kudin, ke dai ki yi wa wani alheri kawai.''

Hakkin mallakar hoto FlickrHeath BrandonCCBY2.0
Image caption Masu kiran a yi alheri, na ganin ko da wani dan karamin abu ka yi na taimako na iya yada akidar a duniya

Ba lalle ba ne mutane masu irin wannan al'ada ta taimako da alheri su sami wani sakamako na nan take, in bayan murna da godiyar wanda suka taimaka, amma mutane irin su Brown, suna samun ladansu ne ta hanyar gamsuwa da jin dadinsu na rayuwa gaba daya.

Micheal Norton na jami'ar Harvard ya bayar da wasu shedu masu gamsarwa, da ke kara tabbatar da cewa, mutanen da suka kashe mafi yawa daga cikin albashi ko dukiyar da suke samu wurin taimakon wasu, sun fi zama cikin farin ciki, idan tafiya ta yi tafiya, fiye da wadanda suke kashe ta a kan kansu.

Wannan ba wai sakamakon bincike ba ne na rayuwar kasashen yammacin duniya masu wadata ba kadai, sakamakon bincike ne da ya gudanar a sama da kasashe 130 na duniya, kama daga Amurka zuwa Uganda.

Ya ce, ''a dukkanin kasashe, a tsakanin mai hali da talaka, kuma a duk wata nahiya, mutanen da suke bayarwa sun fi samun farin ciki.''

A kan wannan dalilin, yana ganin farin cikin da ke tattare da bayarwa, ''yana samun duk mai taimakawa'', wanda wannan dabi'a ce da ke tattare da rayuwar mutum, ba ta da alaka da al'adarka.

Sandi Mann ta ce, ta dauki wani lokaci ka je kana taimakon sauran jama'a ka iya kare ka ma daga kamuwa da wasu cutuka. A wani bincike da aka yi na sama da shekara 30, matan da suka yi aikin sadaukar da kai, suna da kariya ta kashi 16 cikin dari ta kamuwa daga wata babbar cuta a cikin wannan lokaci.

Ana ganin watakila saboda abin da suke yi na taimakon na rage musu damuwa, wanda a sanadin hakan kuma garkuwar jikinsu za ta kara karfafa.

Hakkin mallakar hoto FlickrDncnHCCBY2.0
Image caption Duk da yadda muke son yin abokai wani lokaci mukan ki amincewa da wani alheri, daga baki kamar shiga lema a lokacin ruwan sama.

Akwai dalilai da dama, da za su sa idan mutum ya yi wani abu ba na son kan shi ba, jikinsa da zuciyarsa za su iya jin dadi ta wannan hanya.

Taimako ko bai wa wasu ka iya kara maka masoya da abokai, zai kuma kara maka sanin muhimmancinka a rayuwa, za ka ji cewa lalle ka yi wani tasiri, za ka fahimci amfanin tashinka da safe.

Norton ya ce, kasancewar mutum, halitta ce mai mu'amulla da junanta, wannan zai iya kasancewa ya samo asali ne daga wannan rayuwa tamu.

Kamar yadda za mu ji bukatar cin maimako ko shan zaki, dukkanninmu za mu iya jin bukatar taimakon wasu mutanen.

Farin cikin maitaimako

Wannan akalla shi ne nazarin, amma kuma duk da haka Sandi ta gano cewa wannan jin dadi da mai taimako kan ji abu ne mai wuyar samu.

Bayan da ta karanta wannan bincike, sai ta shirya yin sati biyu tana gudanar da wasu 'yan abubuwa na taimako.

Ta ce, ''na kudiri aniya sosai zan yi hakan kuma ba wani abu ba ne da zai ci kudi da yawa ba.''

Abu na farko da ta tsara yi mai sauki ne, inda ta je shagon da take shan gahawa tare da 'ya'yanta. Abin da ta shirya shi ne ta bayar da gahawar karamin danta, wadda shi ba ya sha.

Ko da ta fara kewaya teburan jama'a masu shan shayi da gahawa a shagon tana neman mai son gahawar, wanda zai karba, maimakon a samu mai karba tare da godiya, sai ma kallonta ake da alamar zargi.

Ta ce, ''sai na ji kamar na fito fili na ce wa mutane so nake kawai in yi wani alheri.''

Sai bayan da ta sauya salon bayar da kyautar gahawar ne, ya kasance kyautar ba ta fito fili karara ba, ta kauce wa wannan zargi na ganin kamar tana da wata muguwar manufa ne (kamar ko ta sa guba ko ta tofa yawu a ciki), sannan mutanen suka sauya yadda suke kallonta

Ta ce, ''nan da nan sai labari ya sauya, sun ga cewa lalle dan nawa ba ya son shan gahawar.'' Amma duk da haka sun ki karba, amma kuma ba alamar kallon zargin, sai ma murmushi suke yi da kuma godiya.''

A karshe dai wata mata mai suna Rochel ta karba, wadda ita ma a cikin wannan makon na ga ta ba wa wani kyautar gahawar.

A cikin wadannan kwanaki 13, a kullum na nemi yin wani alheri ga bako ko wanda ba mu san juna ba sai na ga alamar wannan zargi da rashin yarda da ake nunawa.

A inda na nemi taimaka wa wani ko wata da lema ne lokacin da ake ruwa, ko biya wa wani kudin wurin ajiye mota, ko ba wa wani da nake gabansa a layi a kanti damar ya shiga gabana. ''A duk wadannan sai da na ga alamar wannan zargi gaba daya.'' Ta ce.

A duk lokutan , sai ta bayar da wani dalili ne mai gamsarwa, mutane suke yarda da taimakon nata, kamar a layin ta ce tana jiran wani ne bai karaso ba.

A kan hakan ne da ta waiwayi abin da ta gani a lokacin ta bayyana dabi'ar da ta kira ''bako hadari''. Ta ce, ''an tarbiyyantar da mu ne kan mu ji tsoron baki.''

Hakkin mallakar hoto FlickrJill Allyn StaffordCCBY2.0
Image caption Wata hanyar yada akidar yin alheri, ita ce yin rubutu a hanya, mai dauke da sako na karfafa gwiwar mutane

Duk da haka akwai lokacin da ta yi tasiri ga rayuwar wani, inda wani mutum ya karbi alewar da ta ba shi zuciya daya, ''ya ce wanzar da kauna maimakon tsana abu ne mai kyau.'' In ji Sandi.

Ta ce, ''idan ka san ka taimaki wani ka fitar da shi daga halin da yake ciki na damuwa, to za ka ga ba abin da ya kai haka.''

Ta hakan ne ma har ta samu wata kawa mai kirki. Har yanzu suna kawance da wannan mata Rochel, wadda ta karbi gahawarta a shagon nan a ranar farko.

Ko ba komai, wannan zargi ko mugun kallo da ake yi mata idan ta nemi yin taimakon da ba a bukata ba, ya kara mata kwarin gwiwa ne da kuma juriya.

Mai binciken ta yi nuni da wani nazari da aka yi, wanda ya nuna cewa mutane sun zama kowa kansa ya damu da shi ba wani ba, a cikin goman shekarun da suka gabata, kuma sun ci jarrabawa kan nuna tausayi da taimakon wasu da kasa da kashi 40 cikin dari, a kan mutanen da suka taso a shekarun 1970.

Kila mun ci baya ne wajen son taimako da alheri da kuma samun sakamakon alheri kan abin da muka yi.

Ta ce, ''wannan abin takaici ne idan har al'ummar da muka zama kenan.'' Ta kara da cewa, '' gaba da tsana da kuma zargi sun yi mana katutu, kuma kusan kowa ya fi fifita kansa , ji muke kanmu kadai muke yi wa yaki da fafutuka.

Saboda haka wannan abu ne da ya kamata mu yi yaki da shi, mu kirkiri al'ada ta yin alheri da taimako, za a ga kamar abu ne mai sauki amma dai ina ganin shi ne abin da muke bukata.''

Masu shakku a kan tsarin za su iya sukansa da cewa ba abu ne na ainahi ba, na bogi ne za su ce. Za ma su iya kallon kamar abu ne na tilasta wa mutanen su yi alherin da zuciyarsa ba lalle tana so ba.

Kai za su iya nuna shedar cewa ma ai alheri ba ya yaduwa da sauri kamar yadda masu rajin ganin ana alherin suke dauka.

Misali bincilken da Norton ya yi da kansa, ya nuna cewa tsana da handama da babakere sun fi yaduwa tsakanin jama'a fiye da alheri.

Ya yi bayanin cewa, ''idan mutum matsolo ne (ya yi maka matsolanci) za ka ga mu ma abin ya bi mu, mun yi wa wani a gaba.''

Hakkin mallakar hoto FlickrStill WandererCCBY2.0
Image caption Ba abin da za ka yi asara idan ka yi nufin alheri, ko da murmushi ka yi wa mutum a hanya yana da kyau

To wannan shi ne zai sa kai kuma ka nuna cewa ai hakan yana daya daga cikin dalilan da suka sa muke bukatar mu zama ma su yin alheri a duniya domin kawar da wannan ta'ada (bazuwar matsolanci) da sauransu.

Bugu da kari ko da dabi'ar alherin sun ce ba ta dundundun ba ce (ta bogi), ba ta dorewa, kamar yadda suke gani, to ai akwai shedar da ke nuna yadda alheri ke sauya mutum ya zama mai taimako har abada.

David Rand na jamia'r Yale ta Amurka, wanda ya gano cewa mutanen da aka karfafa musu gwiwar yin abubuwa masu kyau, su kan zama masu kirki a gaba, ya ce ,''za ka iya koyon halaye na gari.

Shi yana ganin hatta wani abu da mutum zai yi na taimaka wa wasu, kamar jarumtar da wasu suka nuna a lokacin harin da aka kai Paris na baya-bayan nan, duka ya samo asali ne daga dan wani abin kirki karami, wanda har ya fadada mutane kawai suka ji ba abin da ya kamata su yi da ya fice su sadaukar da kansu su taimaki wasu.

Sandi Mann ita tana ganin ai dukkanninmu za mu iya sauya hali mu zama na-gari. A matsayinta na kwararriya kan tunanin dan adam a fannin lafiya, har ma ta fara shawartar mutanen da ke fama da larurar damuwa da su yi kokarin sanya tsarin yin wani dan abu na alheri a cikin tsarin matakan maganin da suke bi.

Sandi ta ce, ''za ka ji masu larurar damuwa na cewa, ba su san amfani ko ma'anar rayuwa ba, kuma su ba su ga amfaninsu a duniya ba.''

Sai ta ce to duk da dai wannan dabi'a ta yin alheri ba maganin cutar ba ce, domin tsarin maganin da suke bi yana nan yadda yake da amfaninsa, ''to amma yin alherin dama ce ta bayar da gudummawa ga al'umma, kuma wannan zai sa su ji dadi, su ji kamar lalle su ma suna da wani amfani.''

Ta ce idan ka yarda za ka jarraba wannan dabi'a (alheri), to tana shawartar ka da lalle ka zama mai juriya. Ta ce, ''abu ne mai bukatar kuduri da karfin hali.

A bisa wannan dalilin ne take ganin idan za ka fara, to ka soma da kadan-kadan, ta ce, ''ba zan ba ka shawara ka je ka tsaya a bakin titi kana ba wa mutane kyautar wani abu ba, abu mai sauki shi ne, ka fara da misali yin fara'a ga mutum idan ka hadu da shi a hanya, ko yin magana mai dadi da mutuntawa ga masu aiki a kantin sayar da kaya ko gidan mai.''

Yi wa mutane kallon mutunci da fara'a ko gaishe da mutumin da ta hadu da shi a hanya ya zama abu mafi sauki na alheri da ta fahimta mutane na yabawa da shi.

A karshe dai tana fatan littafinta zai taimaka wajen tuna mana cewa wani lokaci zama me alheri shi kansa wani abin alheri ne mai amfani a karan kansa.

Ta ce, ''abin da nake son na sauya shi ne, ba wai sai da wani dalili za a yi alheri ba. Za ka iya yin alheri ba domin komai ba sai don kawai ka taimaka.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Does it pay to be kind to strangers?