Me ya sa abincin wani yake gubar wani?

Hakkin mallakar hoto Getty

Me ya sa a wata al'adar wasu suke da wani abinci da suke jin dadinsa amma kuma wannan abincin yake kamar guba a wurin wasu, haka ma kuma a tsakanin daidaikun mutane?

Veronique Greenwood ta bincika

A lokacin da nake zuwa birnin Shanghai na Sin (china), na kan yi kokarin kauce wa wani layi da nake bi idan zan je tashar jirgin kasa ta karkashin kasa.

A ko da yaushe za ka ji wari da doyi a wannan layi kamar wata shadda ce ta fashe dagwalon bahaya yake kwarara a gefen hanya.

Amma kuma na kasa ganin abin da yake wannan wari, sai wata rana na gano inda warin yake fito wa.

Wari ne ko kuma in ce a wurin masu shi kanshi ne daga wani shagon sayar da kayan abinci na kwalan da makulashe a bakin hanyar shiga layin.

A she wannan wani abin ci ne da suka kware da yinsa wanda, ake barin kullin waken soya ya yi watanni ya tsuma a cikin hade-haden nama da madara da ta yi tsami da kuma kayan lambu.

A wurin mutumin da ya fito daga Turai kamar ni, abu ne mai wuya ka taba tunanin cewa zai kai wannan abinci kusa da bakinsa ba tare da an makure mutum ba.

To amma abin mamaki haka za ka ga dogon layin mutane a kofar shagon wadanda suka je domin sayen wannan abinci. Kuma da dadewa na fahimci cewa 'yan kasar Sin da yawa su ma haka suke jin kyama idan suka ga ana cin chukwi (irin na Turawa wato cheese).

Ko da yake cin wani abu da aka yi madara abu ne da yake kara karbuwa a Sin, a yanzu, amma a ce an bar madara har ta fara wari, sannan a sanya mata gishiri da kuma karin kwayoyin bakteriya (bacteria), sannan a cakuda a ci, kamar wani abu ne na hauka a wurinsu.

Hatta wadansu nau'ukan na chukwi wadanda ake ganin cakuden nasu da sauki, mutanen Sin na kyamar cinsu ga alama, idan kuma aka narkar da su a kan burodi, sukan ce dandanonsu ya kan ragu, kamar yadda wasu kawaye na 'yan Chinan suka sheda min.

Hakkin mallakar hoto Getty

Irin wannan babban bambanci na 'abincin wani gubar wani' ya kan taso a duk lokacin da ka duba bambancin da ake da shi kan yadda al'ummomi suke abincinsu.

Shin za ka yarda ka sanya wani abu mai wari ne a cikin abincinka na karin kumallo? Ko kuma wani abu mai gishiri, da kuma tsami wanda kamar wani ne yake son ya yi girki amma bai iya ba, ya baci kacokan, kamar yadda wani yaro dan Amurka ya bayyana?

Kayan cikin shanu abincin kanti ne da za a ci shi da taliya, ko kuma robar da ba ta taunuwa da aka zuba mata wani ruwa kamar na bandaki?

Ta wani fanni, wannan bambanci ba abin mamaki ba ne, domin ta haka ne za mu koya daga wadanda muke tare da su abin da ya cancanci a ci da kuma wanda ya kamata a kaurace masa, kuma hakan ya bambanta daga yanki zuwa yanki.

Amma dai maganar nan da ake cewa dandano abu ne da ya dogara ga yadda mutum ya dauka, kuma abu ne da ake koya, bai taba kasa shammatar mutum ba.

A kokarin da suka yi na bayyana bambancin da ake da shi tsakanin abincin al'ummomi, masana kayan abinci sukan yi la'akari ko amfani da dandanon da suka dogara da shi a matsayin ma'auni, abubuwan sun kunshi yaji da kayan kanshi, wadanda suka dace da al'adar mutane.

Hadin tumatir da tafarnuwa da ganyen na'ana da kuma man zaitun ya kan zama irin abincin Italiya, idan kuma abinci ya kunshi busasshen kifi (cray fish) da barkono da citta da kuma man-ja za ka ji ya yi kama da abincin 'yan Brazil.

Haka dai kowa ce kasa yanayin hadin kayan abincin al'ummarta yake, kuma hatta a cikin kasar ma ya kan bambanta daga kabila zuwa kabila.

Wasu 'yan yawon shakatawa 'yan kasar China a Australiya, da aka yi nazari a kansu kan abincin da suka fi so, sun nuna cewa cin abincin da ba irin nasu ba, ba ya gamsar da su. Ko da ya ke idan aka dafa kayan abincin waje ta hanyar da 'yan Sin din suke girkinsu sukan ji dama-dama.

Wannan abu ne da ya shafi kusan dukkanin al'umma, na bayyana abin da yake mafi dadi, ba wai abin da za a iya ci ba.

Idan abu ya kai matuka, bambancin al'ada wani lokaci yana bayyana wata fahimta wadda gaba daya ma take daban kan wai menene ma yake sa abinci ya kasance mai dadi.

Fuchsia Dunlop, wadda ta rubuta littafi a kan abincin Sin da girkin, ta nuna a littafin nata mai suna 'Sharks Fin and Sichuan Pepper', cewa hatta 'yan Turai da kan yi kasadar jarraba cin abincin Sin ba sa jin dadin girkin na Sin.

Ta ce misali, idan aka yi maka girkin hanjin irin manyan agwagin nan, giz, (geese) da wata dabbar ruwa mai kama da gurji (sea cucumber), za ka ji abincin ba shi da wani dandano, kuma a baki za ka ji kamar roba kake ci.

Hakkin mallakar hoto Getty

Duk da haka wannan abinci ne da ake sayar da shi sama da dala 100, kowane kashi, tsadar tasa kuma ba ta rasa nasaba da yadda ake jin dadinsa.

Magana ce ta sha'awa ko dandano

Duk da yadda za a iya yin wannan kwatanci na dandanon abinci a tsakanin al'ummomi daban-daban, akwai wasu abubuwa da ke tattare da bambancin ba dadi ne ba kadai.

Kokarin gano cewa abincin da wani ke ci, kai ko alama ba za ka bari ya je kusa bda bakinka ba, zai iya bayyana wani bambanci tsakaninku.

Ana ganin tasirin wannan magana ta abincin wani gubar wani a zahiri ta yadda muke amfani da ita wajen auna wasu masu cin abincin, kamar yadda Lucy Long mai tatsuniyar abinci, ta rubuta a littafinta 'Culinary Tourism'.

Ta ce, ''ana daukar mai cin abin da ba a ci a matsayin wani bako na daban, kila ma mai hadari, wanda ba ba shakka ba dan uwanmu ba ne, yayin da shi kuwa mai cin abin da ba shi da dadi ake daukarsa a matsayin wanda yake da wani dandano na daban.''

Za mu iya kawar da wannan bambanci a tsakaninmu idan har muka yarda cewa da yawa daga cikin abubuwan da muke kauna (abinci) ba abu ne da aka halicce mu da shi ba.

Misali tunanin da ake yi yanzu shi ne, abubuwan da ke sa mu ji daci a harshenmu sun kasance a jikinmu ne domin su gargade mu mu guji abu mai daci, wanda zai iya zama guba a jikinmu.

Jarirai sabbin haihuwa suna da halittar kin abu mai daci, wanda kishiyar yadda suke ji da abu mai zaki ne nesa. Amma kuma duk da haka mutane da dama sun koyi yadda za su sha gahawa, wadda tana da daci, kullum kuma bakar chakuleti (mai daci) ta zama abar kaunar mutanen da ke son dandano mai dadi a bakinsu.

Charles Zuker, masanin ilimin halittu, wanda ke bincike kan abubuwan da ke sa mu ji dandano, a jami'ar Columbia, ya ce, yana ganin mun saba da ci da shan abubuwa masu daci ne a yanzu a sanadiyyar kokarinmu na gano wasu abubuwa na jin dadi da kuma sanin wasu abubuwan da ba mu sani ba, kila ma hadda abu mai hadari.

Paul Rozin, masanin tunanin dan adam, shi kuwa ya hada daci ne da barkono mai zafi tare da kallon fim wanda zai sanya ka kuka dukkaninsu wuri daya (wato daya suke).

Dukkanin wadannan abubuwa suna yaudarar jikinka ne ya dauka cewa suna da hadari, amma sai a hankali ka fuskanci barazanar har ka fahinci cewa ba su da wani hadari. Kamar maganar da ake cewa, ''kura ta gane kunnen jaki ba kashi ba ne nama ne.''

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Masu yawon bude idanu da dama tuni suka zabi abincin waje da suke jarraba ci idan sun yi tafiya. To amma za ka yi tafiya zuwa inda ka san da niyya za ka ci abin da kake kyama ko ki ?

Idan da za ka ci wani abu sabo na daban, tsawon wasu 'yan kwanaki a kowane wata to da za ka ba kanka mamaki kan yadda za ka saba da wani abincin da a da kake kyama, har ma ka rika jin dadinsa.

Wannan zai iya ba ka dama ka waiwayi baya, idan ka ga wani yana cin wani abinci da ba za ka iya kaiwa kusa da bakinka ba ma, ka san yadda tarin baiwar da ke tattare da halittun jin dandanon bakin mutum suke, ka san yadda mutane za su iya cin abincin da yake wari cikin jin dadi da sha'awa.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Why some cultures love the tastes you hate