Sa ma ido na sa ka shiga taitayinka?

Hakkin mallakar hoto Getty

Ana kallon abin da kake yi? Hakan zai iya sa ka sauya dabi'arka ko halayenka ta yadda za ka rika yin abin da ya kamata ba tare da kai kanka ka sani ba.

Ga bayanin binciken Jason G Goldman

Idan akwai wani abu da shafukan sada zumunta da muhawara na intanet suka koya mana a yau shi ne, yadda za mu natsu mu san irin bayanai na gaskiya da za mu rika bazawa a duniya a game da kanmu..

Muna tunanin yadda idanuwan ma'abota karatun labaranmu na Twitter da sauran shafukan da muke yada bayananmu ta intanet suke nazarin wadannan bayanai.

A kan gargadi daliban manyan makarantun gaba da sakandare cewa jami'an daukar dalibai a makarantun za su iya ganinsu a shafukan intanet, kuma masu neman aiki su rika tabbatar da cewa ba su sanya hotunan batsa ko na wasu munanan abubuwa ba a shafukansu na intanet ba.

Tuni daman Google ya daina amfani da tsarin nan nasa na yadda mutum zai iya gamuwa da wani ko wata da ba su san juna ba, wanda mutum ba lalle ba ne ya sa bayanansa da hotunsa na gaskiya ba.

Harkokinmu na shafukan intanet a yanzu sun zama wata hanya ta kare kima da mutuncinmu, domin duk abin da muka yi ba daidai ba zai iya shafar mutuncinmu.

Hankoron da mutum ke da shi na bayyana halayensa na kirki ba abu ne da lalle a ce ya tsaya ga zuwan fasaha ba. Nawa ne daga cikinmu muke natsuwa mu san yadda ya kamata mu tafiyar da harkokinmu idan har mun san an zuba mana ido ko kuma wata na'ura na nazarin halayyarmu?

A zahirin gaskiya ma mukan natsu mu yi abin da ya kamata, idan ana kallonmu, ko da zane ko hoton ido ne aka kafe a wuri ya kan shafi halayyarmu ko sauya dabi'armu.

Kuma ba lalle ne ba ma mun san da kasancewar wannan zane ko hoto na idanuwa a wurin, amma dai idan har mun san an zuba mana ido to mukan natsu. Mutane ne kadai suke da irin wannan dabi'a?

Sama da yara 360 ne suka shiga wani gwaji na dabara kan dabi'ar dan adam ba tare da sun sani ba, wanda a shekarar 1976 ya tabbatar da wannan tasiri na yadda mutane ke yin abin da ya kamata idan sun san ana kallonsu.

A lokacin wata al'ada ce kamar ta tashe (a kasar Hausa) inda yara ke zuwa gida-gida suna wasa ana ba su alewa, a wannan lokaci sai wasu masana tunanin dan adam 18 suka shiga gidaje daban-daban, suna jiran yaran.

Idan yaran suka kwankwasa kofa sai masu gidan na bogi wato masu binciken su bude musu gidan, idan suka shigo suna wasan sai masu gidan su ce, 'ga kwalin alewa nan idan sun gama tashen, su dauki alewa daya kawai su tafi, su kuwa masu gidan su kauce su ba su wuri, tare da wani mudubi a ajiye a wurin, amma kuma akwai wani daga cikin masu binciken da ke boye yana lura da abin da yaran ke yi bayan an ba su baya.

Masu binciken sun fahimci cewa ba lalle ba ne yaran su yi dan hali, su dauki alewar da ta wuce daya idan suna ganin kansu a mudubin nan.

Wannan shi ne abin da masu binciken suka gano, wato idan yaran suna ganin fuskarsu a mudubin ko da kuwa sun rufe fuskar tasu da kayan tashen da wuya su aikata wani abu na rashin gaskiya.

Sanya ido

Wasu masanan daga jami'ar Newcastle a Biritaniya sun bullo wa binciken ta wata siga, inda suka gano cewa sanya ido na iya rage satar kekuna.

Masanan sun yi amfani da bayanan jami'ar inda suka gano wurare uku da aka fi satar kekuna a makarantar, sai suka kakkafa wasu alamomi a wuraren.

Alamar da suka sa, ta hoton idanuwa ce dauke da wani rubutu da ke cewa, ''Barayin keke: Muna kallonku'', da sunan ''Aikin Kama Barayi'' da kuma tambarin rundunar 'yan sanda a jikin kwalayen da aka kakkafe.

Wannan alama ta sa an samu raguwar satar keke a kowanne daga cikin wuraren da kashi 62 cikin dari. Sai dai kuma abin takaice sai barayin suka karkata da satar a wasu wuraren a cikin harabar jami'ar.

Duk da cewa barayin sun karkata zuwa wasu wuraren da satar kekunan amma dai an ga yadda wannan sanarwa ta gargadi da aka kakkafe da ke nuna cewa ana kallonsu ta sa sun rage sata a wuraren, ta zama gargadi.

Hakkin mallakar hoto Nettle et alOperation Crackdown
Image caption Da aka sa wannan alama a harabar jami'a an samu raguwar satar kekuna

Can gaba a wannan shekara da aka yi wannan gwaji ne, masu binciken suka sake dawowa wuraren uku, kuma har a wannan lokacin wadannan alamomi da ka kakkafe suna nan duk tsawon wannan lokaci.

A wannan karon masu binciken sun zo ne da niyyar gwajin ganin ko wannan alama ta idanuwa da rubutu ta hana satar keke za ta iya hana mutane zubar da takardu da ke bata wuri.

Masu binciken sai ma suka makala 'yan takardu (kamar na tallata wani abu) a jikin hannun duk kekunan da ke wurin da kyauro (rubber band), domin masu kekuna da sun zo kawai su cire takardar su jefara awurin bayan sun karanta (watakila).

Bayan rabin lokacin da suka tsara, sai masu gwajin suka zubar da wasu takardu a wurin, domin idan masu kekunan sun zo sun ga alamun an zubar da takarda su ma su zubar.

Bayan sun yi haka sai kuma suka karkato da hoton idanuwan nan ta yadda idon ke kallon kasa. Kamar yadda aka yi tsammani sai mutane ba su zubar da takardun a wurin ba, idan aka kwatanta da wurin da ba a sanya wannan alama ta gargadin kama barayin kekr ba.

Haka kuma takardun da masu nazarin suka zubar domin yaudarar masu kekunan su ma su zubar ba su sa sun zubar ba.

Wannan tsoro na kiyayewa da mutum ke yi idan ya san ana ganinsa, ya yi abin da ya dace, bai shafi birai ba, domin a kwanan nan wadannan masu bincike na jami'ar Newcastle tare da hadin gwiwar wasu masana halayyar birai (Max Planck Institute for Evolutionary Anthropology)suka karkata da nazarin nasu a kan wasu birai a Zambia (Chimfunshi Wildlife Orphanage Trust).

Masanan sun tsara yadda biran za su debi gyada ne (wadda suke sha'awa sosai), a gaban wani hoton idanuwan biri. Tun da su birai suna bin matsayi da girma ne a cikinsu hatta wurin dibar abinci, masanan sun yi tsammanin duk karamin birin da ya zo zai wuce ta wurin idan ya ga hoton idanuwan biri na kallonsa zai ki daukar gyadar, sai ya daku karas da aka ajiye da kusa da wurin, domin tsoron ana ganinsa.

Su kuwa manyan biran idan sun zo wurin za su dauki gyadar duk da wanna ido da ke kallonsu. Abin mamaki biran sai ba su la'akari da wannan hoton idon da yake kallonsu ba.

Wani binciken ma ya kara tabbatar da haka, inda a wani gwajin da aka yi birai suka ki sauya dabi'arsu duk da cewa wani birin na kallonsu.

Idan har da biri ya damu da mutuncinsa kamar yadda mutum ke son kare kima da mutuncinsa, to da idan wani ya gan shi lokacin da ya dauki wannan gyada ( ko ya yi sata) kuma wani birin ya gan shi, to da sai su raba da daya birin, kamar yadda aka ga mutane na yi (idan barawo ya yi sata wani ya gan shi sai ya yi kokari ya rufe masa baki, ya ba shi wani abu).

A duk lokacin da mutuncinmu zai tabu, sai mu yi kokarin hada kai da wanda ya gan mu muna yin abin da zai shafi mutuncin, amma idan muka san ba a ganinmu sai mu yi son ranmu.

Ba wai su birai ba su san sanya ido ba ne gaba daya ba, a'a, nazari a kan kura ido ya nuna cewa birai da mutane ba su da bambanci yadda suke kallon fuska, inda suke lura sosai da idanu sannan kuma su duba baki.

Saboda haka biri ya sani idan an kura masa idanuwa ko sanya masa ido, ba ya damuwa ne kawai da kallonka.

Amma shi kuwa mutum, ya san idan ana kallonsa, sai mu sauya halinmu ba tare da mun ma san mun sauya ba, in dai har mun lura an sanya mana ido. Kuma haka muke yi ko da kuwa hoton idon ne ke kallonmu.

Idan akan son karanta wannan a harshen Ingilshi latsa nan. How being watched changes you - without you knowing