Za ka iya gane kuskure da mugunta?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Babban mutum ya kware wajen nazarin zuciya ko tunanin sauran mutane, ta yadda zai iya bambanta abin da aka yi da niyya da wanda aka yi ba da niyya ba (katari). Haka su ma 'yan kananan yara da dabbobi.

Jason G Goldman ne ya gano haka ga kuma bayaninsa

Mu dauka na zuba maka shayi ko gahawa aa jikinka. Bayan da ka natsu da abin da ya faru da kuma kila konewar da ka yi, kila za ka ji haushina.

Amma kana jin za ka huce idan na gaya maka cewa sakacina ya sa na zuba maka shayin amma ba mugunta ba? Ko da sakaci ne ko kuma da niyya na kwara maka, aikin dai zai zama daya ne ba bambanci, wato hannuna ya juya sannan shayin da ke cikin kofin ya fice, ya zuba a rigarka mai kyau.

Amma kuma ta wata hanya za ka iya bambancewa tsakanin abin da ya faru bisa hadari da wanda aka yi da niyya, ka kuma dau mataki daidai da yadda ka fahimci abin ya faru.

Daga cikin abubuwan da nake rubutawa a wannan shafi, a wannan karon ina duba yadda dan adam da kuma biri ke iya fahimtar cewa wasu halittun ma suna da abubuwan da suka yi amanna da su da bukatu da niyya, wadanda suka sha bamban da namu, abin da ake kira ''nazariyyar zuciya'' (theory of mind).

A rubutun da na yi a baya na duba yaudara. Yadda mutane da birai da karnuka da wasu dabbobin suke iya hasashen abin da wasu suka sani.

Ba za ka iya yaudara ba sai ka iya hasashen abin da wani ya sani, a takaice sai iya nazarin tunani ko zuciyar mutum ma'ana abin da za ta iya sakawa.

Wannan ne kuma zai ba ka dama ka iya fahimtar ba ma ilimi ko abin da wasu suka sani ba har ma abin da za su iya yi (dabi'arsu). A takaice dai wannan yana sa mu iya hasashen abin da zai faru nan gaba.

Wannan ilimin ko kwarewar ta dogara ne ga kwarewar da muke da ita ta fahimtar dalilin da ya sa wani ko wasu suka aikata wani abu, kuma kafin mu iya yin haka, muna bukatar mu iya bambancewa tsakanin abin da aka yi da niyya da kuma wanda ya faru ba da niyya ba.

Mu mutane muna danganta abu da wata niyya ba tare da tunani a kan abin ba, ma'ana mukan yi wa abu fassara ba tare da mun fahimce shi ba sosai.

Ka kaddara misali, ga wata mata tana tsaye kusa da dakin wata lifta (na'urar hawa dogon bene), tana daga gwiwarta sama. Idan tana rike da wasu tarin littattafai a hannunta ne za ka dauka tana son danna makunnin lifta din ne da gwiwar tata. Amma kuma da ba komai a hannunta za ka dauka tana motsa jiki (kafarta) ne kawai.

Ka ga a nan a saukake ka fassara ma'anar abin da matar take yi, sannan kuma ka kara da nazarin yanayin da take yin abin da wurin sannan ka ayyana abin da kake gani tana so ta cimma (burinta).

To a nan idan ka san burinta na wannan abu da take yi za ka iya yin hasashe na abin da za ta yi nan gaba.

Har yanzu ba ka gamsu ba? To ga wani misalin. Ka kaddara kai bako ne a duniyar, a lokacin ziyararka ta farko sai ka ga wasu mutane na wani wasa na kokarin dauko tuffa daga cikin ruwa a wani babban baho da baki.

Ba shakka za ka kaddara cewa amfani da hannusu su dauko tuffar shi ne abu mafi sauki. Kasancewarka bakuwar halitta mai basira, za ka kaddara hannuwan mutane ba sa aiki, ko kuma ka dauka a wannan duniyar tuffa tana da wuyar rikewa da hannu, sai da hakori.

Ko kuma dai ka kaddara mutanen suna wanke fuskarsu ne kawai. Idan ka ci gaba da kallon abin da suke yi, watakila a karshe ka fahimci yadda wasan yake, da dokokinsa da kuma abin da ake son a cimma da shi.

A sanadiyyar haka za ka iya yin hasashe na kwarai a kan abin da masu wannan wasa za su iya yi nan gaba.

Wannan shi ne ainahin abin da muke kokarin mu magance ko kuma matsalar da muke neman shawo kanta a duk lokacin da muke nazarin dabi'ar wasu mutanen.

Dole ne mu yi nazari mai zurfi ba kawai mu kalli abubuwan da ayyuka suka kunsa na zahiri ba, domin mu fashimci buri da kuma dalilan yin wani aiki.

Hands-free test

'Yan kananan yara (na mutum) ma za su iya yin wannan. Masana tunanin dan adam Gyorgy Gergely da Harold Bekkering da Ildiko Kiraly sun tsara wani aikin gwaji da ya kunshi yara 'yan watanni 14 da ke zaune a kan tebur kusa da mai gudanar da gwajin.

A tsakaninsu sai aka sanya wata fitila, wadda za a iya kunnawa ta hanyar taba ta. Mai gudanar da gwajin sai ta fara kunna fitilar ta hanyar taba ta da goshinta.

To rabin yaran suna iya ganin hannun matar (mai gwajin), su kuwa saurin rabin, suna rike da wani zani a kusa da kafadarta. Yaran kashin farko sai suka kwaikwaye ta, suka kunna fitilar da goshinsu, yayin da yawancin 'yan daya rukunin suka yi amfani da hannunsu.

Duk da kasancewar yaran 'yan watanni 14 'ya'yan mutum za su iya bambance tsakanin burin matar wato kunna fitilar da kuma aikinta, wato tana fitilar da goshi.

'Yan kashin farko sun iya tunanin cewa matar ba ta yi amfani da hannunta ba duk da cewa ba ta rike da komai, saboda haka tana da kyakyawan dalilin amfani da goshin nata, duk da cewa ba abu ne da suka sani ba.

Su kuwa 'yan daya kashin kawai suna ganin da hannuwan nata ba wani abu ba za ta kunna fitilar da goshinta ba da hannu za ta kunna.

Abu ne da zai ba ka sha'awa a ce yara 'yan kanana sun iya yin wannan tunani akan abin da ake son yi wato buri da kuma niyya,a irin wannan yanayi ba mai sauki ba, amma dai ba su kadai suke da wannan basira ba.

Masana ilimin sauyin halitta David Buttelmann da Malinda Carpenter da Josep Call da kuma Michael Tomasello sun gudanar da irin wannan nazari da goggon biri.

Mai gwajin ya rika kunna abubuwa guda shida wadanda sun hada da fitila ko wata kararrawa ko wani abu da dabara, inda yake amfani da goshinsa ko kafa ko kuma ya zauna a kan abin, amma kusan a rabin lokacin da yake hakan ba komai a hannuwansa, saboda haka zai iya amfani da hannuwan amma kuma bai yi ba.

A sauran lokacin kuwa yana rike da wasu abubuwan a hannunsa ba ta yadda zai yi amfani da su ko yana son yi. Kamar wadancan kananan yara ('ya'yan mutum) su ma birai sun iya kwaikwayon mutumin duk yadda ya rika yi, suna kunna fitilar da danna kararrawar da sauransu ta amfani da goshinsu ko kafa a lokacin da su ma ba komai a hannunsu kamar yadda mutumin ya rika yi.

Amma kuma lokacin da wani abu yake hannunsa birin yakan yi kokarin ya yi amfani da hannun. Kamar dai 'ya'yan dan adam biri zai iya bambance aiki da abin da ake so a yi (buri).

Ba wasu nau'ukan birai ba ne kadai da sauran wasu dabbobi suke iya kaucewa wani sunduki wanda mai nazari (mutum) ya dungura ba da niyya ba, a kan wanda ya nuna da niyya domin su nemo abinci a cikinsa ba.

Ma'ana birai da sauran wasu dabbobi sun san wurin da mutum ya nuna da niyya domin su nemi abinci a ciki, sun kuma iya sanin misali akwatin da gwiwar hannun mutum ta dungura lokacin da yake rike da wani abu a hannuwansa, sun san wannan ba nuni ba ne, saboda haka sun san ba ana nufin su duba wannan akwatin ba ne wai domin su dauko abinci.

Ko da hannunsa ba ya dauke da komai, wannan dungura da gwiwar hannunsa ta yi, mai kamar nuni ba sa daukarta a matsayin nuni.

Binciken da aka yi da aku (mai ruwan toka) irin na Afrika ma ya nuna cewa, shi ma yana iya fahimtar dabi'a a matsayin manufar yin wani abu.

Aku yana iya bambancewa tsakanin mutumin da yake da niyyar ba shi abinci da kuma wanda ba zai iya ba shi ba.

Barewar da take rayuwa a dajin Afrika cikin 'yan dakikoki ne kawai take iya fahimtar damusar da ke sando, wadda ita kuma ya wajaba ta yi sauri ta fahimci hanyar da abincin daren da take sa rai da shi zai subuci mata (tserewa).

Da farko za ka ga kamar wannan kaka-kara-kaka tsakanin damusar da barewar ba ta da wata kama ko alaka da shayin nan da na zubar a jikinka.

Amma kuma basirar dan adam ta fassara niyyar aiki ta dogara ne a kan iyawarmu ta nazartar tunani ko zuciya, wanda hakan ke ba mu dama da sauran dabbobi mu fahinci cewa wani abu da aka yi an yi shi ne da niyya ko kuma ba da niyya ba, kuma mu yi amfani da wanna bayani mu iya yin hasashen abin da kuma za a iya yi a nan gaba.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. How we can tell an accident from purposeful actions