Bacin rai zai iya sa zuciya ta buga?

Image caption Mai bacin rai yana tare da hadarin bugun zuciya

Tsananin bacin rai zai iya kisa kamar yadda wani bincike ya tabbatar. To amma me ya sa likitoci suka dade ba su gano shedar hakan ba duk da ta bayyana a fili?

Ga bayanin Jason G Goldman

A shekarar 1986 aka kwantar da wata mata mai shekara 44 a babban asibitin Massachusetts da ke Amurka. Larurar da ke damunta a lokacin ita ce, da safe lafiya kalau take jin kanta amma da zarar yamma ta yi sai ta rika jin wani zafi mai tsanani a kirjinta, yana bi ta hannunta na hagu.

Wannan alama ce karara ta cutar bugun zuciya, amma abin mamakin shi ne ita ba ta samun wata larura ta zuciya ba. Ga shi kuma babu alamun wani dunkulallen jini a jijiyoyin da ke kai jini zuciyarta.

A haka daga waje za a iya dauka ciwon zuciya ne, amma kuma ba shi ba ne. Da suke bayyana larurar wadda ba a gane ta ba a lokacin, amujallar harkokin lafiya ta 'new England Journal of Medicine, Thomas Ryan da John Fallon, suna ganin ciwon kamar ya danganci abu ne na tunani ko bacin rai maimakon na fili.Daman tun da farkon wannan rana an gaya mata cewa danta mai shekara 17 ya kashe kansa.

Zai iya kasancewa matar tana fama da bacin rai ne? Kamar yadda aka fahimta daga baya, amsar na nan boye a fili. Wannan lamari na rashin lafiyar wannan mata abu ne da ya ba wa likitoci mamaki, amma kuma ba wani labari ba ne ga kowa.

Tsawon shekaru da yawa likitoci sun yi watsi da tunanin cewa akwai alaka tsakanin tunanin mutum da kuma jikinsa.

A littafinsu (zoobiquity) Kathryn Bowers da Barbara Natterson-Horowitz sun bayyana yadda yawancin likitoci suke da wannan al'ada ta kin mayar da hankali kan, tunanin cewa tunani ko bacin rai zai iya haifar wa da jiki ciwo da za a iya gani a zahiri a zuciya.

Likitocin zuciya suna mayar da hankali ne kan matsalolin da za a iya gani a fili, amma kuma likitocin halayya ko kwakwalwa na lura ne da hankali.

Duk da wannan , shedar da ke nuna cewa tsananin tunani ko bacin rai ko tsoro zai iya tasiri a zuciya aba ce da ta dade har shekaru gommai, amma kuma ba a dan adam ba.

Masana rayuwar dabbobin daji da likitocin dabbobin ne suka fara gano cewa tsananin tsoro zai iya illa ga jiki. Ya zuwa tsakiyar karni na 20, masanan sun lura cewa akwai wani abin mamaki da ke faruwa idan wata dabba ta shiga wani yanayi na tsananin tsoro, misali farmaki daga wata dabba da za ta hallaka ta.

Idan dabbar ta kama ta, sai sinadarin tsoro (adrenalin) da jiki ke fitarwa (a cikin jiki) idan halitta ta samu kanta cikin wata fargaba, ya cika jijiyar jini, ta yadda jinin zai zama kamar wata guba, har ya bata jijiyoyin karfin dabbar, tare da zuciya, abin da ake kira ''tsananin fargabar kamu''.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Tsawon shekaru masana rayuwar dabbobin dawa sun gano cewa tsananin damuwa na iya yi wa dabba illa

Zuwa shekara ta 1974 likitocin dabbobi da yawa sun san matsalarar sosai, har ma wata wasika da aka wallafa a mujallar halittu ta 'Nature' da ke bayar da shawarar yadda za a kaucewa larurar ba ta damu ta bayar da bayani a kan ya ma ainahin matsalar take ba.

A lokacin masu bincike sun gano cewa kama dabbobi domin binciken kimiyya ko kiwo ko wasu abubuwa makamantan haka, kusan na da hadari ga rayuwar dabbar.

A lokacin da likitoci suka fara nazari a kan wannan larura da ba su sani ba wadda ke da alaka da tunani ko bacin rai a Massachusetts, tuni likitocin dabbobi suka gano cutar zuciya da ke da alaka da damuwa, a dabobo daban-daban masu yawa.

Daga kusan tsakiyar 1990 an kara samun wasu mutanen da aka fara gudanar da bincike a kansu kan yadda tsananin larurar da ta shafi damuwa ko bacin rai ko tunani take iya haifar wa da jiki illa.

A 1995 masu bincike, Jeremiy Kark da Silvie Goldman da Leon Epstein sun gano cewa Yahudawa sun fi fuskantar hadarin mutuwa sakamakon matsalolin da suka shafi zuciya a ranar 18 ga watan Janairun 1991, fiye da a kowace rana kafin wannan watan ko kuma watanni biyu gaba, da kuma irin wannan rana a shekarar da ta wuce.

Dalilin haka kuwa shi ne saboda a wannan rana ne aka fara yakin tekun Fasha, wanda ya haddasa harba makamai masu linzami har guda 18 cikin Isra'ila daga Iraki.

Wannan nazari ya gano cewa karin mace-macen da aka samu a lokacin ba wai sun danganinci raunukan da makaman suka ji wa mutane ba ne kai tsaye, mace-mace ne da tsananin tsoro (na mutuwa) ya haddasa.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Fargabar harin makami mai guba ta sa mutane sun yi ta mutuwa a Isra'ila a 1991

''Fargabar barazanar da za ta iya hallaka mutum ta yadu,'' kamar yadda masu binciken suka rubuta a mujallar kungiyar likitoci ta Amurka (Journal of the American Medical Association).

''Domin shirya wa harin guba, sai aka raba wa kowa takunkumin kariya daga guba da kuma allurar maganin guba. Dukkanin iyalai sun samar da wani daki na musamman na kariya a gidansu, sannan an rika ba wa mutane bayanai ta kafafen yada labarai yadda za su iya kare kansu.''

Hankalin dukkanin kasar ya tashi, fargabar harin makamai masu linzami ta yi tsanani ta yadda wasu ba za su iya jure mata ba.

Bayan wannan shekarar, wasu masu binciken sun dukufa wajen gudanar da bincike kan mutuwar bakatatan da ke da nasaba da ciwon zuciya a Los Angeles ranar 17 ga watan Janairun 1994 .

Wannan ita ce ranar da aka yi wata babbar girgizar kasa da ta kai maki 6.8, ''daya daga cikin girgizar kasa mafi girma da aka taba yi a wani babban birnin Amurka ta Arewa,'' kamar yadda masu binciken suka bayyana, inda ta faru da misalin karfe 4: 31 na safe.

A mujallar likitanci ta 'New England Journal of Medicine', sun ruwaito cewa an samu gagarumar karuwar mutuwar da ke da alaka da bugun zuciya sakamakon fargaba da tsoron da girgizar kasar ta asuba ta haddasa.

Kamar yadda yawancin mutuwar Yahudawa ba ta shafi raunin makami mai linzami ba, haka su ma, yawancin mace-macen ba su danganci ciwon da aka ji sakamakon girgizar kasar ba, abu ne da tsoro ya haddasa.

Sai dai kuma yawancin wadanda suka mutun, daman ba ma su cikakkiyar lafiya ba ne.

A shekarun 1990, masu bincike na kasar Japan sun sanya wa, wannan larura ta ciwon zuciya a sakamakon tsananin tsoro lakabin "takotsubo cardiomyopathy", wanda ya danganci wata tukunya (takotsubo ) da ake kamun wata halittar ruwa (octopus) da ita.

An sanya wa cutar wannan lakabi ne saboda yadda bangaren hagu na zuciya yake kumbura kamar wannan tukunya ta su.

Hakkin mallakar hoto spl
Image caption A shekaru goma da suka wuce ne aka yarda sosai damuwa na iya sa zuciya ta buga

Har sai a shekara ta 2005 ne aka fara bayyana cikakken bincike a mujallun harkokin lafiya, cewa likitocin dan adam sun fara lura da wannan larura ta cutar zuciya da ke haddasa mutuwa a sanadiyyar bacin rai ko fargaba.

Abin kunya ne a ce an dauki tsawon lokaci kafin likitocin dan adam su amince da abin da masana rayuwar dabbobin dawa da kuma likitocin dabbobin suka sani da dadewa.

Idan wanna ya koya mana wani darasi, to bai wuce cewa abubuwan da muka yi tarayya a kansu da dabbobi ba sun fi yawan yadda muka sani a da.

Kamar yadda wannan shafi ya gano, abubuwan da muka hada da dabbobi suna da yawa, kama daga iya rawa, da gudanar da mulki ta dumokradiyya ko kuma shawo kan mata ko mazanmu da kanshin turare.

Dukkanin wadannan abubuwa suna rubuce karara a tsarin yadda rayuwarmu ke gudana. Halittarmu (dan adam) wani dan karamin reshe kawai ta kama ta mamaye a katuwar bishiyar rayuwa (halittu).

Zai zama abin kunya idan aka ce girman kanmu ya hana mu amfani da ilimin da binciken shekara da shekaru kan sauran halittu da ke duniyar nan ya gano.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Can you die of a broken heart?