Yadda za ka fi cin moriyar motsa jiki

Hakkin mallakar hoto spl

Idan har ka damu da tsarin yadda kake motsa jiki, to ba shakka kana bukatar ka kara zage damtse, domin kada ka rika aikin baban-giwa. Ka san tsarin kimiyya na motsa jiki?

Ga bayanin William Park

Kafin ka kama hanya zuwa wurin motsa jiki, ga wasu shawarwari masu muhimmanci guda bakwai, daga ilimin kimiyya, da za su kara maka kwarin gwiwa da yadda za ka fi amfana da atisayen.

1. Abin da ya sa motsa jiki ke kara kaifin basira (IQ)

Ka lura da wannan: Yaran da suke tafiya makaranta da kafa, sun fi mayar da hankali da natsuwa tare da samun sakamako da ya fi kyau a makaranta. Haka kuma tsoffin da suke dan motsa jikinsu ba kasafai suke rasa kaifin basira ba, idan aka hada su da wadanda ba sa motsa jiki.

Ana tunanin karin yawan jinin da ke zuwa kwakwalwa a sakamakon motsa jiki, yana taimakawa girman 'yan kai sako na jiki, da kuma bunkasa samar da wasu halittun masu aikin kai sako da kwayoyin halitta na girman wadanda ke da matukar muhimmanci ga lafiyar kwakwalwa baki daya.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

2.Tasirin jin sauti a lokacin motsa jiki

Wadanne wakoki ne suke karfafa maka gwiwa da kara maka kuzari idan kana motsa jiki? Da yawa daga cikinmu muna ganin sauraren wata ko kida ko dai wani sauti yana kara mana kwarin gwiwa da kuma juriya idan muna motsa jiki.

Me ya sa sauti yake da wannan tasiri? Amsar na cikin kwakwalwarmu ne ba tsokar jikinmu ba, in ji masanin tunanin dan adam, Tom Stafford kamar yadda ya bayyana kasidarsa kan batun.

An fi ganin tasirin hakan a motsa jikin da mutum yake yi shi kadai, kamar gudu ko wasan kamar tuka kwale-kwale maimakon wasan mutane da yawa (kamar kwallo).

Sakon da ke fita daga sauti ko wakar da muke ji yana tafiya ne daga kunnenmu zuwa yankin kwakwalwarmu da ke sarrafa motsin tsoka da jijiyoyinmu, in ji Stafford, to bugun kidan zai iya taimaka wa aikin saita lokacin motsin aikin namu (motsi).

3. Rashin gishiri ne ke sa kagewar jijiya ko wata gaba (kafa ko cinya)?

Wannan wani abu ne da kusan ba a kai ga gano dalilinsa ba. Saboda yana da wuyar hasashe, kuma kokarin haifar da shi a dakin binciken kimiyya ba abu ne mai sauki ba, saboda haka yawancin binciken da ake yi ana yinsa ne a kan matsalar ta gaske.

Nazarin da aka yi a kan 'yan wasan zari-ruga na Amurka ya nuna matsalar ta rikewar wata tsokar jiki (kafa ko cinya), ta fi aukuwa a lokacin zafi, wanda haka ya sa ake ganin abin ya zo daidai da nazariyyar da aka yi cewa karancin gishiri ne a jiki wanda zufa ke jawowa ke haddasa larurar.

Sai dai kuma matsala a kan wannan fahimtar ita ce, hatta alokacin sanyi 'yan wasa suna gamuwa da larurar ta rikewar jijiya

Haka kuma wani binciken ma da aka yi a kan 'yan gasar gudun yada-kanin-wani (dogon zango) na Afrika ta Kudu ba a ga wani bambanci na sosai a tsakanin yawan gishirin jikin wadanda suka gamu da matsalar da wadanda ba ta same su ba.

Shawara ita ce, idan kana da wannan matsala to ka rika motsa kafar sosai amma ba wai ka kara yawan gishirin da kake amfani da shi ba.

Ka kara nazari kan abin da ke haddasa rikewar jijiya a nan .

Hakkin mallakar hoto iStock

Ana yawan gaya mana cewa mikar da jijiyoyinmu (kafafu ko hannu) ita ce hanyar da ta fi dacewa ta kaucewa ciwon kafa ko hannu, rana daya bayan motsa jiki ko kuma kaucewa jin ciwo a lokacin wasa. To hakan gaskiya ne?

Bincike guda biyu dukkaninsu sun nuna amsa kusan daya a kan maganar, cewa ba haka abin yake ba. A kasidar da Claudia Hammond ta rubuta, Rob Herbert daga Cibiyar George da ke Australiya, wanda ya yi nazarin daya daga cikin kasidun, ya gaya mana cewa idan kana jin dadin mimmike jiki (kafa da hannuwanka da sauran sassan jiki), kafin ka shiga atisaye (motsa jiki), to yana da kyau ka ci gaba da haka, amma ba lalle abu ne da zai taimaka maka maganin rikewar jijiya ba

Dukkanin shedun da ake da su, sun nuna cewa bambancin da ake da shi kadan ne a wurin maganin rikewar da kuma kare jin rauni, a sanadiyyar mommotsa jikin kafin atisaye.

5,. Ko takalman tsere na musamman na hana jin rauni?

Idan ka saba da atisayen gudu kila kana da wani takalmi na musamman na gudu. Akan wanna watakila sai ka jarraba gudu a gaban ma'aikacin kantin sayar da takalma, yana nuna maka yadda za ka yi da kafarka. To amma hakan yana da wani amfani?

Shedar muhimmancin amfani da takalma na musamman ba ta da yawa, har ma wasu ke ganin kamar almara ce kawai. Abin mamaki ma kuma shi ne hatta shedar cewa gudu a wuri mai tauri ko tsandauri na kara jawo wa mutum rauni,wannan sheda ba ta da karfi.

Amma kuma kamfanonin takalma za su rika kokarin yin takalma da suke cewa wai suna taimaka wa dan wasa ko kuma su rage hadarin jin rauni.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

6. Anya za mu taba tseren mita 100 a kasa da dakika tara?

Idan kai dan tsere ne mai himma, za ka iya sanya wa kanka wani buri da kake son ka cimmma. To amma mece ce iya iyakar da mutum zai kai? Ed yong ya duba mana wannan kuma kamar yadda aka yi tsammani ya gano cewa tambaya ce mai wuyar amsawa.

Ga yawancin 'yan tsere, gudunsu ya dogara ne ga karfin da za su iya sanya wa lokacin da kafarsu take kasa, saboda haka akwai zabi biyu a nan; ko ka taka kasar da karfi sosai ko kuma ka sa irin wannan karfin na tsawon lokaci.

Nazari ya nuna cewa tsokar diddigen mutum fiye da duk wata tsoka ita ce take sa yawan karfin da masu gudu suke sa wa a kasa.

Gudun mutane yana karuwa amma ta hanyoyin da ba za a iya hasashe ba, kiyasin baya-bayan nan ya nuna dole ne mu kai iya karshen abin da jikin mutum zai iya kaiwa a tsere.

7. Ko motsa jiki na taimaka wa rage damuwa?

Bincike mafi kyau da aka yi kan tasirin motsa jiki a kan yanayin damuwar mutum shi ne wanda Cochrane ya yi daga tarin bayanan da ya yi nazari a kai.

Binciken ya duba alkaluma daga gwaji guda 30 a kasashe irin su Thailand da Denmark da Australia, kuma suka ayyana cewa, lalle kam motsa jiki zai iya amfanar mutanen da ke fama da damuwa, amma amfanin dan kadan ne matuka. Ba shakka dai motsa jiki ba maganin da wasu ke ikirari ba ne na damuwa.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. How to exercise smarter