Ka san dabarar masu sata a gidaje?

Hakkin mallakar hoto Getty

Ta yaya za ka iya satar shiga gidan mutane ba tare da ka sha wuya ba? Wani bincike ya duba dabarun da kwararrun barayi ke amfani da su na sata, domin sanin yadda za a iya maganinsu.

Ga bayanin nazarin na David Robson

Da farko abin kamar ba wata wahala. Na bi ta bayan gidan na ratsa ta lambu, ba ka jin karar komai sai ganye da iska ke kadawa, na shiga gidan ta kofar baya, ba tare da wani ya gan ni ba. Ina aikata laifi ne da rana kiri-kiri, kuma ba mai kama ni.

Ba jimawa ba sai murnata kusan ta koma ciki, na rude. Da farko na kamo talabijin, sai na ajiye ta a kasa. Lokaci na kurewa, saboda haka sai na garzaya na hau matattakala, na je dakunan sama, sai na sake dawowa kasa, kuma na koma sama dai.

Na dauki kwamfutar tafi-da-gidanta na sanya a jaka tare da waya, amma a saurin da nake yi sai na manta daya daga cikin muhimman abubuwan da ya kamata na dauka.

Sai wadda muka zo satar da ita, Claire Nee, ta nuna min wata riga da ke rataye a kan kujera, a cikinta akwai 'yar karamar jakar hannu (alabe), da ke dauke da katunan banki da mukullai.

Sai kuma ta kara nuna min wata 'yar kwamfutar iPad a kan kujera da kuma fasfuna a cikin kwabet, wadanda dukkanninsu na kwashe. Kai abin ya ba ni takaici, domin na dauka ai zan iya sata kamar wani kwararren barawo.

To ba komai dai domin ba wanda zai kama ni, kasancewar gidan da muke wannan sata ba na gaske ba ne, gida ne na wasan kwamfuta, wanda yana daga cikin abubuwan da Nee, kwararriyar masaniya kan tunanin dan adam a jami'ar Portsmouth, take jarrabawa domin fahimtar yadda zuciyar barayi take.

Ta ce, ''a da mutane suna daukar barayi a matsayin wasu 'yan ta-fadi-gasassa, ba sa daukar cewa mutane ne masu dabara da wayo da kuma kwarewa, tun da yawancinsu ba masu ilimi ba ne.'' Ta hakan kuskure ne, domin malamar ta gano cewa barayi, mutane ne kwararru da suke da dabara kamar, 'yan wasan dara (chess) da kwararrun 'yan kwallon tennis.

Idan har muna so mu yi maganin barayi da sauran masu aikata laifi a nan gaba to lalle sai mun yarda da wannan kwarewa tasu.

Hakkin mallakar hoto Network Instiitute at Vrij University Amsterdam
Image caption Me kake son ka dauka? Jami'ar Vrij ta Amsterdam ta kirkiro wasan kwamfuta na yadda za ka kwaikwayi yadda ake sata a gida

Nee ta fara gudanar da bincikenta ne a gidan yari, inda cikin natsuwa take tattaunawa da daurarru kan abin da suka aikata da yadda suke yin sata da sauran laifuka.

Ta kan yi musu tambayoyi, da baka kuma ta ba su takardu masu dauke da tambayoyi su amsa, sanna kuma ta kan nuna musu hotuna da taswirar cikin gida da titina domin su tuna irin dabarun da suke amfani da su a lokacin da za su yi sata.

Kai za ka dauka barayin za su ji haushi ko ba za su ba ta hadin kai ba, ganin cewa sirrinsu ne take son su bayyana mata, to amma abin sabanin haka, dadi ma suke ji da suke yi mata bayani.

''Su farin ciki ma suke yi kan cewa ga wata da ke sha'awar sanin abin da suke yi,'' in ji ta.

Amma duk da haka, ayarinta sun gamu da 'yan abubuwan mamaki. Daga irin gwajin (sata) da take yi ne, ta gayyaci wasu dalibai da kuma wasu daga cikin daurarrun barayin nan zuwa wani gida na musamman na 'yan sanda (wanda aka ba ta izini), domin ta ga yadda za su iya shiga gida, a matsayin yadda barayi kan shiga gida je jama'a.

Kofar gidan ta can baya a bude take, amma masu daukar hoton yadda abin ke kasancewa sun yi mamaki ganin yadda wasu daga cikin barayin ba su bi ta kofar ba,sai kawai suka kama tagar da ke saman kansu suka shiga gidan.

Kuma a can gaba ita kanta mai binciken, wato Nee, ta manta da jakarta a kasa a cikin gidan, (lokacin sun hau bene).

Ta ce, ''yanzu ina da hoton bidiyon wani daga cikin barayin yana lalube min jaka, ya kuma kwashe min duka kudina, wannan abin mamaki ne kuma abin dariya.''

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Yawancin barayi, sun kware ba sa ma tsayawa tunanin inda za su nufa da abin da za su dauka in sun shiga gida

Su dai barayi suna amfani damar da ta samu, kuma suna amfani da kwakwalwarsu da zarar dama ta samu ba tare da bata wani lokaci ba, sai su biya bukatarsu.

Su suna nazarin wurare ne a lokacin harkokinsu na yau da kullum, inda za su ga wata taga ko kofar gida a bude ko kuma gidan da aka yi tafiya ba kowa. Za kuma su iya sauya inda suka yi niyyar zuwa idan suka ga wani wanda zai fi musu saukin shiga.

Shigarsu wuri ke da wuya, sai su natsu, su dukufa amfani da kwakwakwar nan tasu, su ga ina da ina ne za su samu abubuwa masu daraja ba tare da bata wani lokaci ba.

Ba kamar ni ba,a lokacin da nake jarraba wannan wasan kwamfuta, lokacin da na samu shiga gidan da zan yi satar, sai na rasa takamaimai abin da zan dauka, na dau wannan na ajiye in na rarumo wannan abin sai na ga wani can na ajiye na tafi dauko wancan.

Su kwararrn barayi kusan dukkaninsu tsarinsu daya ne, idan suka shiga gida, (idan bene ne), abu na farko da suke yi sai su je dakunan sama, sanna kuma su dawo dakunan kasa, a wannan tsakanin ne sai cikin sauki su duba aljihun riguna, domin dauke 'yar karamar jakar hannu, wadda ke dauke da katin banki, da sauran tufafi masu tsada da kayan karau na mata (sarkoki da 'yan kunne da awarwaro na gwala-gwalai), da sauran 'yan abubuwa masu daraja.

Za ka ga ba su damu da kayan kallo da sauran kayan laturoni ba wadanda za su yi saurin tsufa, da kuma za su zamar musu kaya wajen dauka.

Cikin akalla minti hudu, kwararren barawo ya tattara kaya da kudi na kusan fan 1000 ko dala 1560 a cikin gida, fiye da abin da daliban Nee suka tattara a gwajin satar da suka yi a gidan nan na 'yan sanda.

Abin mamaki yawancin tunanin da ke amfani a wannan lokaci da barawo ke neman abubuwan da zai dauka masu daraja, tunani ne da yake zuwa masa ba ma tare da ya sani ba, domin abu ne da ya riga ya zama jiki, abin kawai da yake gabansa a lokacin shi ne yadda zai kauce wa kamu a gidan.

A lokacin da Nee take tattaunawa da barayi a gidan yarin da ta je, daya daga cikinsu ma ce mata ya yi, ''ai zan iya bincike gidan idanuwana a rufe.''

Wani kuma ya ce mata, ''neman, abu ne da ya zama kamar wata halittar jiki, kamar aikin soji.'' ya kara da cewa, ''abu ne da ya zama jiki ka natsu da abin da kake yi da kuma inda za ka samu abubuwa, yawancin abin da mutum ke mayar da hankali a kansa shi ne kada wani ya dawo ya rutsa ka a gidan, in banda haka neman ai abu ne da ya zama kamar tsoka da jini.''

A kan haka Nee, take gani sata tana bukatar kwarewa, domin abubuwa ne da mutum zai yi cikin dan kankanin lokaci, wanda idan ba kwararre ba ne sai ya rasa me zai yi idan ya shiga gida.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Katin sayayya na banki na daga abubuwan da barayi suka fi nema idan sun shiga gida

Duk da cewa nazarin Nee, ba lalle ya kasance abu ne na zahiri ba, amma tana da kwarin gwiwa binciken zai iya samar da hanyar yaki da masu aikata laifi. Bisa la'akari da bincikenta, ba ta yi mamaki ba cewa kararrawa ko jiniyar tona asirin barawo a gida ba ta hana barayi sata yanzu, domin makwabta da yawa ba sa daukar matakin kiran 'yan sanda ko da sun ji wannan kararrawa o kara har wajen minti 20 ko ma fiye da haka.

Hakan ma ya sa barayi suka gane ba sa razana idan sun ji karar, sai su cigaba da satarsu ba tare da sun kula ba.

A maimakon haka Nee tana ganin dabarar da ya kamata mutane su rika yi, ita ce su bullo da wani abu da ba ya cikin tunanin barawon kamar yadda ya saba, wanda zai iya sa ya bar satar ya gudu, kamar ka nadi sautin karar tafiyar mutum ko wani dan surutu, wanda zai iya sa barawon ya damu.

Haka kuma za ka iya yin tsarin gidanka ta yadda zai rudar da barawo daga irin tsarin gidaje da ya riga ya saba da shi. Ta kara da cewa, '' abin da ya wajaba shi ne sai ka zama mai kirkira, domin duk abin da ka yi za su saba da shi a hankali, sai ka rika sauyawa.''

Hakkin mallakar hoto Getty

Karkatar da tunani da hankalin barawon na iya karkatar da shi daga rayuwar da ya saba ta aikata laifi, wato ya daina sata. Nee na ganin yin wasu abubuwa da ke iya jan hankalin barawo, kamar barin tagar gidan da ba kowa a bude na iya sa barawo ya yi tunanin amfanin da zai samu idan ya je gidan ya jarraba sa'arsa.

Ta ce ba lalle ya zama da tunanin yin satar ba amma idan ya ga galala sai hankalinsa ya karkata kan dadi da amfanin da zai samu idan ya yi satar.

A yanzu Nee tana aiki tare da Jean-Louis Van Gelder na cibiyar nazarin miyagun laifuka ta kasar Holland domin gano yanayin da barawo ke shiga a lokacin da yake sata.

A halin yanzu daia akwai matakai masu sauki da za mu iya dauka domin kariya daga barayi. Bayan abin da aka sani, Nee na ganin, daya daga cikin dabarun da suka dace, ita ce, ka yi kamar da mutum a gidan ko da yaushe, domin kusan dukkanin barayin da ta gana da su, sun nuna cewa za su yi duk abin da za su iya domin kaucewa haduwa gada da gaba da mai gida (daya ne kawai daga cikinsu ya ce shi ya kan so ya ma je ya leka ya ga masu gidan da zai yi wa sata suna sharar barci).

Saboda haka daga yanzu idan za ka fita daga gidanka ka dan je wani wuri, sai ka dan yi wani abu na alamar kamar kana sallama da iyalanka a cikin gidan, ta yadda za a iya dauka akwai wasu a cikin gidan, da kake ce musu sai ka dawo., ko da kuwa ba kowa a gidan.

Kafin na barku da wannan bayani, ina mamakin ko Nee watakila ta fara ganin alamar sace-sace a ko ina, ko da kadan ne kila, kamar barayin da take nazari a kansu.

Ita kanta ta amsa cewa, kamar kwararren dan wasa, a yanzu a duk lokacin da ta fita wani dan tattaki, misali da karenta da safe, tana iya ganin wuraren da ke da rauni wadanda ta ce, ''da ina sata ne to da na kai musu ziyara, domin yanzu ina ganin na samu ilimi sosai a kan dan hali''.

Dadin abin dai yanzu shi ne ba ta kai ga biya zuciyarta, ta jarraba wannan kwarewa tata ba.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The strange expertise of burglars