Ra'ayinmu na siyasa a jininmu yake?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Akwai shedu da dama a yanzu da ke nuna alama gadon ra'ayinmu na siyasa muke yi daga kwayoyin halittarmu. To amma kafin mu yi watsi da akwatin zabe mu karkata ga gwajin kwayoyin halitta (DNA), Tom Stafford ya bayyana yadda sanin kwayoyin halittarmu ba zai bayyana mana kai tsaye yadda tunaninmu ke aiki ba.

Akwai abubuwa da yawa da suke tasiri da tsara yadda ra'ayinmu na siyasa yake kasancewa, kama daga yadda muka taso da aikinmu da watakila abokai na mu'amullar yau da kullum da na auratayya.

Amma a 'yan shekarun nan ana samun karin sheda da ke nuna ga alama akwai wani abin mafi tasiri da ke sa mana ra'ayinmu na siyasa, abin shi ne kwayar halittarmu.

A yanzu wannan tunani ko magana ta samu karbuwa, inda da yawa an yarda cewa ra'ayinmu na siyasa yana da alaka da yanayin kwayar halittarmu, har ma ana tunanin bullo da fagen ilimi mai sunansa (genopolics).

Wannan ya fara ne da nazari na gwaji da ke nuna cewa tagwaye ('yan biyu) da suke da kamanni daya sun fi kasancewa da ra'ayin siyasa iri daya fiye da 'yan biyun da ba su yi kama da juna ba.

Wannan yana nuna cewa ba wai zaman teburin me shayi daya ba ne ko zaman wata majalisa daya ba ne kawai yake sa a samu ra'ayin siyasa iri daya tsakanin jama'a ba (wanda dukkanin irin 'yan biyun suna yi), sai dai a sanadiyyar kamannin kwayoyin halitta (wanda 'yan biyun da suka yi kama da juna suka fi samu).

Babban abin da aka gano a sakamakon wannan bincike shi ne, yawanci akidar mutane ta siyasa daga mai sassauci zuwa mai ra'ayin rikau gado ne.

Abin mamaki shedar da aka gano a wannan bincike tana da karfi sosai, domin har ana iya amfani da bayanan da ke tattare da kwayoyin halitta wajen hasashen bambancin ra'ayin siyasar mutum, ba tare da wani shakku ba (wato hasashen ya tabbata), fiye da yadda za mu yi amfani da bayanan na kwayoyin halitta mu yi hasashe kan tsawon rayuwar mutum ko yuwuwar ya fada dabi'ar shan giya ko akasin haka ko kuma wata dabi'a.

To wannan na nufin nan gaba kadan za mu iya watsi da zabe kenan, sai mutane su rika aiko da yawunsu kawai ana amfani da shi wajen sanin abin da suka zaba?

Ko alama, wannan dai ya kara fito da muhimmancin neman ilimin tushen dangantakar kwayoyin halittarmu da dukkanin wani abu da ya shafi tunaninmu da jikinmu.

Tun lokacin da muka fara ganin taswirar kwayoyin halittar mutum sama da shekara 13 da ta wuce, muka ga alamar cewa, kila za mu iya gano duk wani sirri game da rayuwar mutum.

Kuma ta hanyar amfani da tsarin fitar da alkaluma na soji da kuma gagarumin bincike da nazari nna yadda 'yan uwa suke samun kwayoyin halitta kusan iri daya, masana ilimin halitta a yanzu suna kara gano abubuwan da ke sa kamanninmu da lafiyarmu da kuma halayyarmu.

Amma kuma fa akwai wata matsala, domin babu wadatattun bayanai a taswira ko rumbun kwayoyin halittar mutum da za su iya bayyana mana komai, domin dan adam yana da kusan kwayoyin halitta 20,000 wanda ya kasa da kadan ko bai kai na shinkafar dawa ba.

Wannan yana nufin kusan bayanan da suke cikin rumbun kwayoyin halittarka daidai suke da wadanda suke cikin wakoki takwas na na'urarka ta mp3.

Saboda haka abin da ke haifar da sauran jikinka da dabi'unka sakamako ne na ayyukan wadannan kwayoyin halitta naka da sinadarin gina jiki (protein) da suke samarwa da kuma muhallin da kake.

A takaice dai muna nufin, idan muna maganar amfani da kwayoyin halitta wajen yin hasashen ra'ayin mutum na siyasa, hakan ba yana nufin za mu iya gano wata kwayar halitta takamiaimai ba ne kan yadda mutane ke zabe ko kuma kwayar halittar da ke sa dalilin da mutum ke wata dabi'a ba.

Bari mu bar maganar cewa za a iya amfani da wannan hanyar nazari wajen sanin ra'ayin siyasa ta hanyar amfani da ma'auni mai sauki, wanda zai iya ba wa mutane masu bambancin ra'ayi maki iri daya, mu mayar da hankali kan abin da takamaimai ake nufi da cewa za a yi amfani da kwayoyin halitta wajen hasashen ra'ayin mutum da wannan ma'auni.

A zahirin gaskiya babu wata kwayar halitta da ke da alhakin aikin tsara yadda mutane ke amsa tambaya kan ra'ayinsu na siyasa, domin idan muka ce haka kusan abin sai ya zama wani na ban dariya, wanda kuma zai nuna mun dauka cewa akwai wata kwayar halitta da ke boye a matattarar kwayoyin halittar mutum, tsawon miliyoyin shekaru, har sai da masana kimiyyar siyasa suka kirkiro da tsarin darasin tambayoyi, kwayar ta fito fili. Wanda hakan ko alama ba zai zama haka ba.

Kada dai mu tsaya da wannan bayani a nan, bari mu kara jaddada cewa maganar samun wata kwayar halitta da ke sa mutum ya zabi jam'iyyar masu sassaucin ra'ayi maimakon jam'iyyar masu ra'ayin rikau ba abu ne mai yuwuwa ba.

Ta yaya za a ce akwai wannan kwayar halitta tun kafin a kirkiro dumokradiyya? Me za a ce wannan kwayar halitta take yi kafin a bullo da tsarin zabe har ya zama gama-gari?

Kasancewar bayanan da ake da su a matattarar kwayoyin halitta ta mutum kadan ne, hakan na nufin ba lalle ba ne a ce ga wata kwayar halittar wadda ita ce ke sanadin abu kaza.

Amma dai akwai wasu abubuwan masu sauki kamar launin idanu, da za a iya cewa wasu kwayoyin halitta ne ke tsara yadda suke, sai dai yawancin abubuwan da muke son aunawa a game da rayuwa ta yau da kullum, misali ra'ayin siyasa da sauran dabi'u ko cutuka da aka saba gani na dan adam ba su da wata kwayar halitta takamaimai da za a ce ita ke haddasa su.

Karfin alakar da ake gani tsakanin kwayoyin halitta da maunin ra'ayin siyasa na mutum, na nuna cewa akwai wani muhimmin abu wanda kwayoyin halitta suke haddasawa, wanda shi kuma a nasa bangaren yake sa mutum ya dauki wani ra'ayi na siyasa.

Wani dantakara zai iya kasancewa abin da ke tafiyar da ra'ayinmu ko yanayinmu. Misali wani nazari ya nuna cewa masu aikin sa kai na agaji wadanda suka fi fara zufa (gumi) sosai, da sun ji wata kara kwatsam, ba shiri, su ne suka fi yuwuwar bayar da goyon baya wajen aiwatar da hukuncin kisa da kuma yaki a Iraki (a lokacin).

Wannan na nufin mutanen da aka fi ganin alamun damuwa na bayyana a jikinsu idan wata barazana ta faru, sukan kai ga samun ra'ayin rikau na siyasa.

Wani nazarin kuma amma wannan karon a Biritaniya, ya nuna bambanci tsakanin tsarin kwakwalwar masu ra'ayin rikau da masu sassaucin ra'ayi.

Bambancin shi ne bangaren kwakwalwa da ke koyon martanin da mutum kan dauka ko yake ji idan wani abu na tayar da hankali ya faru (amygdala) na masu ra'ayin rikau ya fi girma.

Harwayau wannan ya nuna cewa ga alama bambancin ra'ayin siyasa ya iya kasancewa yana samo asali ne daga bambancin yanayin yadda mutuane suke ji (emotion) a jikinsu idan wani abu ya faru.

Amma fa ka lura cewa, ba wata magana da ke nuna cewa yanayin halittar jikin mutum ne kai tsaye yake tafiyar da ra'ayin siyasarsa. A maimakon haka ana ganin ra'ayin mutum na siyasa yana samuwa ne daban a wurin mutanen da ke da yanayin jiki na daban (kamar yadda aka gano bambanci kwakwalwa tsakanin masu bambancin ra'ayin siyasa a Biritaniya).

Kwayoyin halitta su na da tasiri kan misali girman wani sashe na kwakwalwa, amma yadda kwayoyin halittarmu suke haifar da wannan bambanci a wani sashe na kwakwalwar shi ne daya daga cikin abubuwan da ke daure kai, wanda kuma wasu kwayoyin halittar da wasu abubuwa kan jingina a jiki su faru.

Saboda haka maganar cewa kwayoyin halitta za su iya tasiri wajen haifar da irin ra'ayin siyasar da mutum ke da shi, ba abin mamaki ba ne.

Kuma maimakon a bar maganar iya nan, kamata ya yi a fahimci yadda lamarin ya kara zurfafa sarkakiyar yadda halittar jikinmu da tunaninmu suke mu'amulla da juna.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Is our political view really encoded in our genes?