Mutum ko dabba, wa ya fi iya jifa?

Hakkin mallakar hoto thinkstock

Dabbobi da dama suna iya jifa, amma za su iya kamar yadda mutane ke yi? Damar jefa wa abokinka robar ruwa ko lemo ko kwallon kwando a raga kila abu ne da yawa daga cikinmu suke renawa, amma da za su lura da sun sauya tunani.

Ga nazarin Jason G Goldman

Ba jifa kawai ba, a'a ka jefa abu ya je daidai inda ka yi nufi ko ya samu abin da ka yi nufi, wannan abu ne da masu binciken kimiyya (biologists, anthropologists) suka dauki kila shekaru masu yawa suna tunani a kai. Mune halittar da ke iya jifa kadai?

A shekarar 1975 PJ Darlington na gidan adana kayan tarihi na dabbobi na jami'ar Harvard a Amurka ya yi ikirarin cewa a yi jifa ya je daidai inda ake so, mutum ne kadai zai iya wannan a cikin halittu.

''Ba wata dabba da za ta iya jifa kamar yadda mutum yake yi,'' ya rubuta. Masanin ya bayyana wani bincike na yadda wasu jinsin gwaggon biri suka jefa wasu abubuwa 44, amma sai sau biyar kadai suka samu abin da ake so su jefa, kuma a hakan ma sai daga nisan kafa shida da rabi (mita biyu) suka iya jifan yadda ake so.

Ya ce, ''wasu birai sukan yi jifa da sanda da duwatsu, amma ba su da saiti kamar na jifan mutum. Amma za ka ga mutumin da ya iya jifa zai iya fasa kan wani mutumin da dutse daga nisan kafa 100 (mita 30).''

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Wasan jefa kibiya na bukatar wani tsari na halittar kashi da tsoka a hannu

Ka duba yadda ake wasan jifan wuka ko kibiya (da hannu), za ka ga daidai wurin da kibiyar ke cakewa (a inda aka shata) ya dogara ne ga wurin da kibiyar take da gudun da ta taho da shi da kuma inda tafiyarta ta nufa a lokacin da aka jefa ta.

Kuma dukkanin wadannan abubuwa sun dogara ne kacokan da tafiyar hannun da kuma daidai lokacin sakin kibiyar da hannun zai yi.

Ko da ya ke ba dukkanninmu ba ne za mu iya samun daidai inda ake so a samu a wasan jifan, amma ko ba komai za mu iya kai wa kusa.

Sakamakon wani bincike da aka wallafa a farkon shekara ta 2014, masu nazari sun ce wannan was abu ne da za a iya koyo kuma a kware a wajen iya jifan.

Kwararrun masu wannan wasa ba sa kuskure sosai kamar wadanda ba su kware ba, wurin sanin daidai lokacin sakin kibiyar da kuma motsin iya tafiyar da za su yi da hannuns lokacin jifan.

Duk da cewa saitin jifa abu ne da mutum zai iya kwarewa da shi a hankali a hankali, amma jifan shi kansa ba abu ne da lalle sai mutane sun koya ba.

To amma wannan ba lalle haka yake ba a rayuwar jinsin biran Japan (Japanese macaques), inda shekaru da dama da suka wuce masu bincike daga cibiyar nazarin rayuwar birai ta jami'ar Kyoto suka zuba ido domin ganin alamar dabi'ar jifa a tsakanin wasu birai iri daban-daban guda 10 da suke bangare daban-daban na kasar.

Sun ga lokaci 83 da aka yi jifa a tsakanin gungun birai daya, sannan kuma suka ga bibbiyu a tsakanin wasu gungun daban-daban guda biyu, a sauran ragowar gungu shidan kuwa ba su ga biran sun yi jifa ba.

Masu binciken sun fahinci cewa jifan da biran ke yi galibi suna yi ne domin sanar da 'yan uwansu wani abu (sadarwa), tun da yawanci suna yinsa ne a lokacin wata barazana ko idan wani abu da zai tayar musu da hankali ya nufo (kamar jiragen sama na yakin sojin Japan wadanda ke yawan bi ta yankin cibiyar nazarin da biran su ke).

Abin da binciken ya nuna shi ne, duk da cewa nau'in biran Japan a kirarsu za su iya jifa to amma su a wurinsu wata al'ada ce, domin babu wata alama ta yin jifa kamar yadda mutane suke yi a tsakanin biran.

Hakkin mallakar hoto Science Photo Library
Image caption Wasu nau'in biran Japan suna iya jifa, amma ba dukkaninsu ba.

To me ya sa dan adam ya samu wannan kwarewa ta jifa? Kila wannan kwarewa ce ta ba wa kakanninmu damar samun abinci sosai, kuma da ba za su iya hakan ba in ba domin yadda yanayin kasusuwan jikinsu yake ba da kuma yadda jikin nasu ya saba ta yadda suke iya juya hannu da kugunsu idan za su yi jifan.

Haka kuma zai iya kasancewa shi ma dan adam ya soma dabi'ar ne a matsayin wata hanya ta sadarwa kamar yadda biran Japan suke yi.

Watakila wannan shi ya sa wasu ke ganin a sanadin koyon jifa mai kyau dan adam ya kara samun wasu abubuwa na basira da suka hada da yare ko harshe da kade-kade, domin jifa na bukatar wata kwarewa ta tunani.

Domin fahimtar yadda dabi'ar ta jifa ta samo asali sosai, masanin tunanin dan adam Justin Wood yana duba yuwuwar ko zai iya raba tsakanin yanayin tsarin kasusuwan jiki wanda ake bukata kafin a iya jifa da kyau da kuma basira ko aikin kwakwalwa da ke tsara yadda jifan zai kasance da kyau (a samu abin da ake nufi).

Domin samun hakan sai mai binciken ya duba wasu nau'ukan birai wadanda tsarin kasusuwan jikinsu ya yi daidai da na biran nan na Japan, saboda haka idan har sun yi jifan, to ba zai zama da saiti ba sosai, domin su ma nau'in na Japan din haka suke jifan.

To shin su wadannan birai sun ma fahimci mene ne jifa sosai? Za su gudu idan wannan mai bincike a kansu ya dauki dutse ya yi kamar zai jefe su? (masu binciken ba su yi jifan ba, saboda haka biran ba su fuskanci wani hadari ba. A zahirin gaskiya idan da biran sun san ma'anar abin da za a yi musu da dutsen da aka dauka da sun tasowa masu binciken da fada.)

Kashi 85 daga cikin dari na biran sun gudu lokacin da masu binciken suka yi cikakken jifa, amma kuma kadan daga cikinsu ne suka damu su gudu lokacin da suka auna suka ga yanayin dagewar masu jifan da yadda suka yi da hannunsu jifan zai iya zama da hadari idan ya same su.

Kuma ba su damu ko ba komai a hannun mutanen ko wani abinci mai laushi suka rike ba. Ma'ana dai duk da cewa biran ba sa iya jifa da saiti kamar yadda mutum ke yi, amma suna da hankali da basirar sanin idan a wurin da suke da kuma irin jifan da za a yi zai iya samunsu ko kuma ba zai same su ba.

Wannan kenan ya nuna cewa tun a da kakannin birai suna da sani game da jifa na saiti ko samun wani abu, kamar jifan wata dabba da dutse tun kafin kasusuwa da tsokar jikin kakannin mutum su juya yadda zai iya jifa kamar yadda yake yi a yau.

Gajerun yatsu da sauran abubuwa na tsarin hannunmu, sun ba wa mutum damar yin motsi da hannun da karfi kuma da kyau ta yadda zai yi jifa da saiti da kuma karfi in ji likitan hannu Scott Wolfe.

Ya ce, '' yadda mutum yake da damar wannan kwarewa ta daban ta motsa wuyan hannunsa kusan a ko da yaushe, da duk wani abu da zai yi, hakan na nuna wannan ma ya taka muhimmiyar rawa a rayuwar dan adam.''

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Bincike ya nuna kokarin jifa na mata manya ba shi da bambancin da na maza

Idan kana mamaki to ka sani cewa mata ma za su iya jifa kamar maza ko da ya ke nasu ba zai yi karfi ko sauri kamar na mazan ba.

A shekarar 2011 Kevin Larson da abokan aikinsa sun kwatanta jifan maza da na mata, amma matan na rukunin shekaru gida uku.

Na farko masu shekara 14 zuwa 17, sai masu shekara 18 zuwa 25 da kuma manya masu 35 zuwa 55. Duk da cewa masu binciken sun gano wasu 'yan bambamce-bambance a aikin jiki tsakanin maza da mata na rukunan masu kananan shekaru biyu na farko amma lokacin da suka girma sai bambancin ya bace.

Tsakanin maza da mata ba wanda zai fi wani bisa bambancin jinsi idan ana maganar jifa ne, amma a tsakanin mutum da biri, dan adam ya fi sosai.

Har yanzu ba na son na yi wasan jifa da Santino, sanannen gwaggon birin nan mai jifa wanda ke gidan namun daji na Sweden, wanda duk safiya yake tattara 'yan duwatsu da sauran kananan abubuwa a cikin kejinsa ya tara, ya rika jifan masu ziyara da suka biyo ta kusa da gidansa.

A wannan fafata da gwaggon biri Santino, kwarewata ta mutum ta iya wasan jifan kibiya ba za ta yi amfani ba, gara in noke idan ya auno ni da dutse.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Can humans throw better than animals?