Ka taba faman tuno wata kalma ko suna da ka manta?

Hakkin mallakar hoto istock

Kokarin tuno wani suna ko kalma wadda ka santa amma ta gagare ka tunawa a lokacin da kake son amfani da ita abu ne da zai bata maka rai, amma kuma zai bayyana abubuwa da yawa kan yadda kwakwalwarmu (hadda) ke aiki.

Ga nazarin da Mark Gwynn ya yi a kai

Ka taba kokarin amfani da wata kalma amma ka kasa tuna ta ko fadarta?

Ba shakka yawancinmu mun taba yin wannan mantuwa wadda a Ingilishi ake kira ''Lethologica'', amma idan hakan ta kasance sai nan da nan mu karkata kundin kwakwalwarmu domin neman wata kalma domin cike wannan gurbi na wucin-gadi.

Yawan kalmomin da ake amfani da su domin cike gurbin na nuna tsananin yadda mutum yake yawan manta sunayen abubuwa da mutane.

Kamar yawancin kalmomi ko sunaye na Ingilishi, masu nasaba da zuciya (tunani), ita ma kalmar wannan mantuwa 'lethologica' sabuwar kalma ce da aka kirkiro daga harshen mutanen Girka na asali.

A nan kalmomin na Girka su ne 'lethe' (mantuwa) da 'logos' (kalma). A addinin gargajiya na mutanen na Girka kalmar 'lethe' harwayau na nufin daya daga cikin koguna biyar na karkashin wannan duniya, inda ruhunin wadanda suka mutu yake shan ruwa domin ya manta da duk wani abu da ya sani game da duniya.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana ganin masanin tunanin dan adam Carl Jung ne ya kirkiro kalmar mantuwar kalma (lithologica)

To ita kalmar 'lethologica' da aka lakaba wa wannan irin mantuwa ta kalma ko suna, ana cewa masanin tunanin dan adam Carl Jung shi ne ya hada ta a farkon karni na 20.

Amma kuma cikakken bayani na farko yana cikin Kamus din kalmomin likitanci ne na Amurka wallafar Dorland bugu na 1915, inda a ciki aka fassara kalmar ta 'lethologica' a matsayin 'kasa tuna kalmar da ta dace'.

To koma dai menene asalin wannan kalma, amfanin hadda da mantuwa a binciken da Carl Jung ya yi na abin da muke yi ba tare da mun sani ba, da kuma a ilimin addinin gargajiya na Girka, ya kara bayyana a fahimtarmu ta yau da yadda hadda ke aiki a kwakwalwa.

Kamar yadda da dama daga cikinmu za mu iya fahimta da kanmu, kwakwalwa ba ta aiki kamar kwamfuta, inda ake adana bayanai a tsanake, sanna kuma idan ana son nemo su a danna wani abu kawai su fito.

Masanin tunanin dan adam, Tom Stafford ya nuna cewa, ''kwakwalwarmu (hadda) na da ban mamaki, amma kuma tana aiki ne da yawan dangantaka ko alakar da yi wa wani sabon bayani da muka adana a cikinta.

Ba ruwanta da matukar bukatar da muke da ita a lokacin da muka bukaci sani ko tunowa ko dauko wannan bayani daga gareta.''

Ma'ana idan muka adana kalmar 'riga' a cikin kwakwalwarmu, to muna bukatar mu danganta kalmar 'riga' da misali abin da ke rufe jiki da sauran abubuwa, to da haka ne a duk lokacin da muka bukaci wannann kalma daga kwakwalwarmu (hadda) sai ta kawo mana kalmar.

Kuma yawan abubuwan da muka danganta da rigar a lokacin da muka mika wa kwakwalwar kalmar ta ajiye mana shi ne zai sa ta yi saurin kawo mana ita idan mun bukace ta. Amma idan ba mu yi haka ba sai ya kasance ta kasa kawo mana kalmar.

Tuno da duk wata kalma da ke kwakwalwarmu abu ne mai wuya. Misali kamus din Ingilishi na Oxford yana dauke da kalmomi dubu 600, kuma hakan ma ba wai iya karshen kalmomin Ingilishi kenan ba.

Kalmomin da babban mutum ke amfani da su a rubutu da magana ba su kai ko kusa da dubu 600 ba, amma kamar yadda David Crystal ya bayyana su kan fi dubu 50.

Amma kuma akwai wasu kalmomin da yawa wadanda mutum ya sani wadanda ba ya amfani da su a rubutu da maganganunsa na yau da kullum. To irin wadannan kalmomi su ne yawanci suke cikin wadanda ba ma iya tuna su wani lokaci.

Hakkin mallakar hoto istock
Image caption Kalmomin da suke kanmu sukan fi 50,000 kuma mun fi manta wadanda ba ma amfani da su sosai

Kalmomin da ba kasafai muke amfani da su ba kamar na sunayen mutane su muka fi mantawa. Kuma saboda kamar yadda muka ambata a can baya, idan ba mun danganta kalma ko mun raba ta da wasu bayanai ko abubuwa da muka sani ba, sai mu kasa tuna ta a lokacin da muke son tuno ta, domin sai ta haka ne kwakwalwarmu za ta iya kawo mana ita nan da nan, idan mun hada kalmar da wasu abubuwan da tun da muka ba kwakwalwar ajiya ta saba da su.

Kalmar 'lethologica' na nufin mantawa da wata kalma, da kuma aikin nemo wannan kalma (da muka manta) wadda muka sani tana wani sako a kwakwalwarmu.

Watakila dole ne mu sha ruwan kogin 'lethe' (kogin karkashin duniya wanda matattu suke shan ruwansa su manta da abubuwan duniyar nan) domin ya taimaka mana na wucin-gadi mu manta da abubuwa marassa muhimmanci da wadanda ba su zama dole a wajenmu ba, saboda mu fi bayar da fifiko kan kalmomi da bayanan da ke da amfani ga rayuwarmu.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Lethologica: When a word's on the tip of your tongue