Turancin Sarauniyar Ingila ya baci?

Hakkin mallakar hoto AP

Tsabar Turanci da salo na daban a magana cikin Ingilishi da aka san 'yan gidan sarautar Ingila da shi ya fara gushewa, abin da ke nuna irin gagarumin sauyin da ake samu a al'ummar Biritaniya.

David Robson ya duba mana wannan lamari

Idan da malamar da aka ajiye ta musamman da ke koya wa Sarauniyar Ingila karatu (lokacin tana karama) a gida tana nan a raye yau, da kila ta lura da wasu sauye-sauye a Ingilishin Sarauniyar.

Masana ilimin harshe sun lura cewa duk da dai Sarauniyar ba ta bar Ts da Gs da aka santa da furtawa ba kamar mai wasan barkwanci Russell Brand, amma Turancin da aka santa da shi tana matashiya, ya ragu yanzu ya zama kamar na gama-gari.

Ba ita kadai Mai alfarmar ba ce wannan sauyi ya shafa. Salon Turancin da aka san 'yan gidan sarauta da manyan masu hali a Biritaniyan da shi a 'yan gomman shekarun da suka gabata ya rasa karsashinsa ne saboda mutane da yawa na kokarin kwaikwayonsa, wanda hakan ya sa aka samu gamin gambiza ko wani salon na daban.

Kokawa da gushewar karsashin Ingilishin 'yan gidan Sarautar da sauran manyan na iya zama wata alama ta yadda 'yan Biritaniya ke matukar son zama masu matsayi na daban a cikin jama'a.

Hakkin mallakar hoto PA

To amma kasancewar a yanzu hatta ita kanta Sarauniyar ba ta wannan Turanci mai karsashi da ake dangantawa da ita, wanda ake kira Ingilishin Sarauniya, na zamanin da, wannan ya ba mu damar sanin abubuwan da ke tasiri wajen tsara muryoyinmu.

Maganar wani harshe ko salo da ya fi dacewa ta bayyana ne a kwanan nan a tarihin harshen Ingilishi, kamar yadda Jonnie Robinson, masani a kan amfani da harshe a dakin karatu na Biritaniya ya nuna.

Masanin ya ce hatta Samuel Johnson marubucin Ingilishi na karni na 18 bai zabi wani salon furucin fadar kalmomi ba a cikin kamus dinsa na harshen Ingilishi, domin yana ganin akwai dan sabani a kan hanyar da tafi dacewa ta fadar kalmominsa.

Robinson ya ce, ''idan ka koma baya zuwa karni na 18, za ka ga hatta masu ilimi da attajirai da za ka ji suna magana da salon Ingilishi na mutane gama-gari.'' Shi kansa Dakta Johnson an san shi da Ingilishi irin na yankin Lichfield.

Masanin ya ce, ''karuwar farin jinin makarantun kwana ne ya sauya yadda masu matsayi a cikin jama'a suka fara sauya yadda suke Turanci, inda suka fara yada salon harshen da ya fi kamanni da na yankin Kudu maso gabashin Ingila( inda yawancin makarantu da jami'o'i suke)''.

Daga nan ne kuma wannan salo ya zama wata alama ta matsayi da iko, wanda ya fadada lokacin da BBC ta dauki salon (Received Pronounciation) take amfani da shi a labarai da shirye-shiryenta.

Robinson ya ce, ''murya ce da kowa yake danganta ta da iko a fadin duniya.''

Hakkin mallakar hoto Reuters

Zuwa tsakiyar karni na 20, tsarin bambancin zamantakewar na sarakai da attajirai da masu mukami a Biritaniya ya ragu, inda yanzu salon harshe ya zama daya daga cikin 'yan alamamomi ko hanyoyuin da za a iya bambancewa tsakanin wadanda suka gaji dukiyarsu da wadanda suka samu dukiyarsu da kansu.

Kamar yadda marubuciyar nan wadda ita ma jinin masu hali ce, Nancy Mitford ta bayyana a littafinta mai suna Noblesse Oblige, '' ta hanyar Turancinsu ne kadai a yanzu za a iya gane 'yan wannan rukuni na manya a cikin al'umma, tun da ba su fi kowa tsafta ko arziki ko kuma ilimi ba.''

Watakila dan lokaci ne kawai ake jira kafin shi kansa bambancin harshen ya fara gushewa, domin ana samun karuwar 'ya'yan ma'aikata suna rike manyan mukamai na iko, kuma harshen Ingilishin na kudancin Ingila ya fara shiga wanda aka fi dauka mafi dacewa (Received Pronunciation;RF).

''Akwai wadanda suke yin Ingilishin da kusan yake sabo na zamani wanda yake kamar gamayyar wanda aka dauka ya fi dacewa( RF) da kuma na 'yan yankin da cocin St Mary-le-Bow Church ta ke, yankin da ake jin karar kararrawar cocin idan an kada ta.'' In ji Jonathan Harrington na jami'ar Ludwig Maximilian ta Munich a Jamus.

Hakkin mallakar hoto PA

Misali a da masu magan da harshen Ingilishin da aka fi amfani da shi a hukumance (RP) za ka ji suna furta kalmomin ''poor'' da ''moor'' da tagwayen wasulla, ta yada za ka ji kamar suna furta su da ''poo-uh; a yau kuwa za ka ji suna furta su kamar ''paw'' da ''maw''

Haka kuma sautin ''Y'' din da ke karshen kalmomi kamar ''really'' da ''very'' sun zama masu tsawo yanzu ba kamar a da ba, a lokacin da ake furta su kamar ''E'' a kalmar ''pet''

Kazalika ''A'' din da ke ''the cat sat on the mat'' a da ana furta su ne da bude baki kadan, ta yadda za ka ji su kamar, ''the ket set on the met''.

A matsayin wata alama ta yadda wannan sauyi ya zama ruwan dare, Robinson ya nuna cewa ana iya jin hatta Yarima William da Yarima Harry suna magana da salon Ingilishin na zamanin nan (RP) wanda ya kunshi salo daban-daban.

Hatta a lokacin auren Yarima William da Kate, Robinson ya lura Kate (yanzu Gimbiyar Cambridge) tana magana da Ingilishi na gama-gari na gargajiya (RP) ba kamar mijinta ba, wanda kila alama ce ta matsayinta na 'yar talakawa, da kuma alamunta na rashin sabo da bayyana a cikin jama'a.

Ya ce, ''idan ka hau wani sabon matsayi dole ne ta yi kokari sosai ka yi amfani da salon da ya fi wanda ka saba da shi, wanda kuma ya fi dacewa da matakin da ka kai.''

Hakkin mallakar hoto AFP

Ba abin mamaki ba ne ka ga matasa sun dauki salon Ingilishin da suka ji ana yi a titi, kila a matsayin wani sanadi na yadda suka taso

''Akwai abubuwan da za mu iya yi a lokacin da muke tashen kuruciya domin tafiya da zamani, wadanda kuma za mu yi watsi da su idan muka girma.'' In ji Robinson.

To irin wadannan ai ba za ka yi tsammani ka same su a tare da Sarauniya mai shekara 89 ba. Amma duk da haka nazarin Harrington ya nuna bakin Sarauniyar (turancinta) ya sauya, ya zama kamar daidaitaccen Turanci na matsakaitan jama'ar Kudancin Ingila a gomman shekarun da suka wuce.

Inda a da take furta kalmar ''lost'' da furuci daya da kalmar ''law'', yanzu sai dai ka ji ta furta ''lost'' din kamar yadda yawanci za ka iya jin mawakiyar nan Londoner Adele tana furtawa a wakarta ''I ain't lost just wandering''. Sannan kuma ta daina furta kalmar ''family'' kamar yadda take yi a da, da take cewa ''femileh'', yanzu ta dawo kamar yadda yawanci ake furta kalmar.

Harrington yana ganin watakila Sarauniyar na daukar wani darasi ne na sauya yadda take Turanci domin ta dawo da kanta kasa-kasa kamar talakawanta.

Nazarin da ya yi na jawabanta na Kirsimeti na shekaru ya ga yadda ake samun sauyi a hankali a hankali a yadda take furta wasu wasullan kusan a duk shekara, saboda idan har tana yin hakan ne da niyya domin koyi da talakawanta, to sai a sa ran gagarumin sauyi a Turancin nata.

To amma kuma masanin yana ganin akwai kuma wani dalilin da zai iya zama sanadin wannan sauyi a Turancin na Sarauniyar Ingila, kamar yadda masana tunanin dan adam suke gani.

A nazari da dama da aka yi, an gano cewa a duk lokacin da muke magana da wani, mu kan sassauto da maganarmu ta yadda za ta zo kusan daya da irin ta wanda muke magana da shi (watakila za mu iya cewa wani yunkuri ne da ba mu san muna yi ba na kulla dangantaka ko fahimtar juna da wanda muke magana da shi).

Akwai kuma shedar da ke nuna cewa yin magana irinta wanda kake tattaunawar da shi na kara sa ka fahimci abin da yake fada da kyau.

Abu mafi muhimmanci a nan kuma shi ne wannan tasiri yana cigaba da kasancewa tare da ku (da kuka tattauna) har bayan kun kammala maganarku, kun rabu.

Harrington ya ce, ''idan ka auna, ko ka yi nazarin maganar mutanen biyu za ka ga kusan maganarsu ta zama iri daya bayan tattaunawar tasu, fiye da yadda maganar take kafin haduwarsu.''

Hakkin mallakar hoto AP

Harrington ya nuna cewa kafin Sarauniyar ta hau gadon mulki, ba lalle ba ne tana haduwa da talakawa da sauran mutane gama-gari akai akai, amma yadda aka samu bunkasar zamantakewa a shekarun 1960 da 1970, mutanen da harshensu bai kai na manyan mutane (masu iko) ba, a hankali sun samu kaiwa ga manyan mukamai na gwamnati.

''Ka duba misali wadanda suka zama fira minista. A shekarun 1950 masu rike wannan mukami suna fitowa ne daga cikin iyalan manyan mutane, sannan a shekarun 1960 da kuma na 70 za ka ga mutane ne da ba su da dangantaka da wani babban gida ko jinin sarauta sam-sam, kamar Harold Wilson da Edward Heath da Margaret Thatcher.''

Ba a ma maganar ma'aikatanta (Sarauniyar) da 'ya'yanta da jikokinta, wadanda dukkanninsu sa iya magana da ita da murya daban-daban (Ingilishi ko salon magana iri-iri), wanda kuma hakan zai iya shafar yadda take magana ita ma.

A gaskiya ma Harrington yana ganin ga wani babban misali a kan ma'aikatan kafofin yada labarai, kamar David Attenborough, wanda shi ma irin wannan sauyi ya shafe shi, idan ka duba yadda shirye-shiryensa na talabijin na farko suke.

Harrington ya kara da cewa, ''wannan kwaikwayo da muke yi cikin ruwan sanyi, ba tare da mun sani ba, na daya daga cikin manyan abubuwan da ke haifar da sauyin sauti (furuci).''

Abin ban sha'awa da mamaki shi ne wannan sauyi a da ana ganinsa ne a tsakanin mutanen da ake gwajin kimiyya da su, amma ba sarauniyar da ke kan gadon sarauta ba.

Duk da matsayi da kimarta da kuma dukiyarta, Sarauniyar Ingilar tana yin 'yan isharorin da mukan yi ba tare da mun sani ba, abin da ke nufin duk ganawar da ta yi, tattaunawar na haifar da wani sauyi a maganar Sarauniyar (maganar na tasiri a kanta).

A wasali daya kawai, za mu iya gano alamar duk mutanen da Sarauniyar ta hadu da su, wanda wannan alama ce ta irin sauyin muryar (Ingilishi) Biritaniyar karni na 21.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Has the Queen become frightfully common?