Me ya sa mutuwa ke sauya mana tunani?

Hakkin mallakar hoto istock
Image caption Tunanin kabari na dan lokaci kawai na iya sauya ka

Karanta wannan dan rubutu ka iya sauya siyasarka da ra'ayinka da kuma shawararka zuwa wani dan lokaci, zai ma iya sa ka ji kana son ka yi suna a duniya. Me ya sa? Maganar mutuwa kadai na sauya tunaninmu ta hanyoyi da dama.

Ga nazarin Jonathan Jong na jami'ar Coventry

Idan mutuwa ita ce abin da ya saba wa al'ada, da kila ba za ta dade a wannan matsayi ba. A shekarun nan ana kara kokarin ganin ana tattaunawa a tsakanin mutane, a gida da kuma a taron jama'a, a kan mutuwar ita kanta da kuma yadda mutum ke kama hanya zuwa mutuwar.

Misali shagunan mutuwa (inda ake zama ana hirar mutuwa) da aka fara budewa a Switzerland a shekarar 2004 sun watsu a duniya, inda suke ba mutane damar magana kan tsoron da suke yi na mutuwa, a yayin da suke shan gahawa ko shayi da 'yan kayan kwalan da makulashe (tattaunawa kan mutuwa cikin natsuwa).

Yadda ba ma kaunar yin magana a kan mutuwa yawanci ana daukar hakan a matsayin shedar cewa muna tsoronta, saboda haka ne ma muke kauce wa duk wani tunaninta ko abu da ya shafe ta.

Sai dai kuma babu wata babbar sheda da za ta tabbatar karara cewa muna jin tsoron. To kenan mene ne yawan fargabar mutuwa? Kuma ta yaya fargabar ke bayyana kanta?

Daga irin bayanan da aka gano ta hanyar amfani da takardar tambayoyi, kusan mun fi damuwa da mutuwar wani namu da muke matukar kauna fiye da mutuwar mu kanmu.

Wannan bincike ya kuma nuna damuwar da muke yi kan yadda ake mutuwa (yanayin yadda mutum zai mutu), misali na jinyar da yake yi da kuma kadaicin da yake shiga a lokacin da yake gargarar mutuwa, fiye da ita kanta mutuwar.

A gaba daya idan aka tambaye mu, ko muna jin tsoron mutuwa, yawancinmu muna nuna cewa ba ma jin tsoro, kuma 'yar fargaba kadan muke nunawa.

'Yan kalilan din mutanen da suke nuna fargabar mutuwar sosai ana ma daukar suna da wata matsala, har ake ganin ya kamata a yi musu magani.

Hakkin mallakar hoto flickr jd hancock cc by 2.0

A daya hannun abin da ya sa ba ma nuna damuwa sosai a kan mutuwa, zai iya kasancewa saboda kin da muke yi mu yarda cewa muna jin tsoron nata, mu tabbatar wa kanmu da kuma wasu hakan.

A kan wannan nazariyya ne, masana tunanin dan adam, suka yi kusan shekara 30 a yanzu suna duba tasirin da labarin mutuwarmu ke iya yi a kanmu ta fannin zamantakewa da kuma tunaninmu.

A gwaje-gwaje sama da 200 da suka yi, masu binciken sun bukaci daidaikun mutane da su kaddara kansu ga shi sun kama hanyar mutuwa.

Gwajin farko na irin wannan an gudanar da shi ne a kan wasu alkalai a Amurka, wadanda aka bukace su da su yanke hukuncin tara a kan wata mata da ake zargi da karuwanci, a shari'a ta kwaikwayo (amma su kaddara da gaske ne za su yi hukuncin).

Abin da ya faru shi ne, yawancin alkalan da aka fuskance su da maganar mutuwarsu kafin su yanke hukuncin, sun yanke tara mai yawa sosai fiye da wadanda ba a yi musu maganar mutuwarsu ba.

Alkalan da aka yi musu maganar mutuwar sun yanke wa matar tarar dala 455 su kuwa sauran sun ci ta tarar dala 50 ne kawai.

Tun daga wannan lokacin an yi ta gano tasiri iri daban-daban a tsakanin rukunan mutane har da al'umma gaba daya na wasu kasashe daban-daban masu yawa.

Bayan sanya mu, mu zama masu tsattsauran hukunci, tunanin mutuwa yana kuma kara mana kishin kasarmu (ffita kasarmu kan ta kowa da muke yi), da sanyawa mu kara zama masu wariyar jinsi da addini da shekaru da sauran dabi'u na wariya.

Da aka tattara sakamakon gwaje-gwajen gaba daya an ga cewa tuna wa mutum mutuwa yana karfafa mana dangantakarmu da kungiyoyi ko bangarorin da muke ciki, mu nisanci wadanda ba namu ba.

Harwayau tuntar da mu mutuwa na shafar akidarmu ta siyasa da ta addini ta hanyoyi da dama. A fanni daya maganar mutuwa na raba kanmu, inda masu sassaucin ra'ayin siyasa suke kara zama masu wannan ra'ayi, yayin da su kuma masu ra'ayin rikau suke kara zama masu wannan ra'ayi.

Haka kuma mutanen da ke da addini suna kara rike addininsu da kyau, sannan marassa addini suke kara fandarewa.

Hakkin mallakar hoto istock
Image caption Mutuwar wani naka ta fi damunka a kan mutuwar kai kanka

A daya fannin kuwa wadannan nazarce-nazarce sun kuma gano cewa tunanin mutuwa yana yi mana barazana ta fannin addini ko ta wasu fannoni, maganar mutawar kan sa mu kara riko da addini ta yadda ma kila ba lalle mun lura da muna kara rikon ba da shi ba.

Kuma idan tunatarwar mutuwar ta yi karfi sosai, kuma ya kasance mutanen da lamarin ya shafa ba su damu da ra'ayinsu na siyasa ba, masu sassaucin ra'ayi da masu ra'ayin rikau, dukkanninsu suna zabar ra'ayin rikau da 'yan takara masu wannan ra'ayi.

Wasu masu binciken sun ce ma wannan ne dalilin da ya sa aka karkata ga bangaren jam'iyyar masu ra'ayin rikau (republican) bayan harin 11 ga watan Satumba.

To amma me ya sa mutuwa take sa mu zama masu tsattsauran hukunci da ra'ayin rikau da kuma bin addini? Kamar yadda masana da yawa suke gani, mutuwa na tilasta mana mu nemi mafaka, yadda ba za mu mutu ba (aljanna). To addinai da dama suna bayar da wannan mafaka (alkawarin aljanna).

Su kuwa sauran madogararmu wadanda ba na addini ba, kamar kasashenmu da kabilarmu suna iya sama mana mafaka ta alama. Wadannan abubuwa da muke dogara da su da tsarinsu bangare ne na mene ne mu, kuma muna mutuwa mu bar su, sun fi mu tsawon rayuwa.

Saboda haka kare al'adunmu zai kara sa mu ji karfi a ranmu cewa lalle mu 'yan wannan kabila ne kuma mu zama masu tsattsauran hukuncin a kan mutanen da suka saba wa wadannan al'adu namu, misali karuwanci, to alama ce ta hakan.

Haka kuma a kan wannan fassara dai, masu bincike sun kuma gano cewa tunanin mutuwa na kara mana burinmu na yin suna da samun 'ya'ya, wadanda duka biyu alama ce ta dorewar mutum (bayan mutuwarsa). Ta bayyana cewa muna son a cigaba da tuna mu, kada mu kauce ko bayan mun mutu ta hanyar aikinmu da kuma kwayar halittarmu.

Hakkin mallakar hoto istock
Image caption Tunanin mutuwa na iya sauya ra'ayinka na rikau

Idan aka tambaye mu a game da (tsoron) mutuwa, muna karfin hali, mu nuna hatta a kan mu kanmu cewa ai ba ma tsoronta. Ba ma kuma ko tunanin ma tsoron mutuwa yana wannan tasiri (da muka bayyana a baya) mai yawa a kan dabi'unmu.

Amma duk yadda muka so ko muka ki, akwai iyakar abin da zamu iya boyewa. Mun yi fice wurin hasashen yadda za mu ji ko mu yi idan wani abu ya faru da mu a rayuwa, haka kuma mun kware wajen fadin dalilin jin abin da muka ji, ko ma abin da ya sa muka yi wani abu.

Saboda haka ko mun gane ko ba mu gane ba, ya tabbata ga alama kawo mutuwa gaban zuciyarmu kamar kawo wa mutum duk tarin masifa da bala'i na duniya ne baki daya.

To ya za mu dauki wadannan sabbin matakai na warware siddabarun da ke tattare da mutuwa da kuma yadda ake yin mutuwar ta hanyar tattaunawa ko hira? Abu ne mai wuya a fada.

Kamar yadda binciken ya nuna kara yawan kawo tunani da maganar mutuwa a harkokinmu da kuma wadanda muke yi da sauran jama'a, zai iya sa mu kara zama masu tsaurara hukunci da nuna wariya.

To amma watakila abin da ya sa mutuwar take wannan mummunan tasiri a kanmu shi ne saboda ba mu saba da tunani da kuma magana a kanta ba.

A tsarin yi wa mutum magani ta hanyar hada shi da abin da yake jawo masa rashin lafiyar, idan a hankali a hankali ana sanya mutum cikin wannann yanayi, ko kuma misali ana hada shi da dabba ko wani abu da yake jin tsoronsa, ta hakan za a kai ga lokacin da wannan abu zai daina razana shi, sai ya samu lafiya daga wannan larura wacce a da abin yake haddasa masa.

Haka ita ma mutuwa ta wannan hanya za a iya maganin fargaba da razana mu da take yi, ta yadda za mu zama masu jajircewa da karfin zuciya a kanta.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Why contemplating death changes how you think