Me ya sa hadda a lokacin jarrabawa ke sa mu fadi?

Hakkin mallakar hoto Getty

Za ka dauka cewa kai ka san kanka, amma idan aka zo maganar hadda ko iya tuna abu, bincike ya nuna cewa ba ka san kan naka ba.

Idan muna kokarin koyon wani abu, yawancinmu muna nazari ta hanyoyin da ke hana abin zama a kwakwalwarmu.

Sai dai kuma shi wannan binciken bai bar mu haka ba sai da ya bayyana mana hanyar da za mu iya bunkasa yadda muke koyon abu.

Ga nazarin Tom Stafford

Dukkanninmu mun taba fuskantar wata jarrabawa mai wuya akalla sau daya a rayuwarmu. Walau ta makarantar furamare ce ko sakandare ko jami'a ko ma ta wurin aiki ce, akwai wata shawara guda daya da kusan a ko da yaushe ake ba mu. Wannan shawara ita ce, ka tsara yadda za ka yi karatunka.

Idan muka yi tsari za mu iya shirya yadda za mu yi nazarinmu na tunkarar jarrabawar maimakon mu takura wa kanmu da hadda a wani lokaci guda kuma a daren ranar da za mu yi jarrabawar, da zummar cewa hakan zai kai mu ga nasara.

Shawara ce mai kyau. Cikin kalmomi hudu a dunkule: hadda ba ta aiki. Sai dai abin takaicin, yawancinmu muna burus da wannan shawara. Akalla wani bincike ya gano cewa kashi 99 cikin dari na dalibai sun amince cewa suna yin hadda.

Za ka iya tunanin cewa ba wani abu ba ne yake sa ka haka, illa rashin tsari. Ba shakka zan yarda cewa ya fi sauki ka bari sai jarrabawar ta zo dab da lokacinta ka fara shiri maimakon ka shirya mata makwanni ko ma watanni kafin zuwan nata.

Amma nazarce-nazarce da aka yi a kan hadda sun nuna cewa akwai wani abu daban da ke wakana.

A shekara ta 2009, misali, Nate Kornell na jami'ar California, Los Angeles, ya gano cewa shirya wa jarrabawa ko koyon abu a cikin wadataccen lokaci ya fi hadda inagnci ga dalibai kashi 90 cikin dari wadanda ya gudanar da wani nazarinsa daya a kansu.

Amma duk da haka kashi 72 cikin dari daga cikinsu suna tunanin cewa hadda ta fi amfani. To me ya ke faruwa a cikin kwakwalwar tamu da muke sa kanmu yadda cewa hakan ya fi?

Hakkin mallakar hoto comedynoseFlickrCC BY 2.0
Image caption Ya fi dacewa ka rika karatu tun kafin lokacin jarrabawa a kan ka yi hadda idan jarrabawar ta zo

Nazarce-nazarcen da aka yi na kwakwalwa sun nuna cewa muna da wata al'ada maras kyau ta dogaro da sabo da abin da muke karantawa da cewa hakan ko zai sa mu san abin.

Matsalar ita ce saboda ba abin dogaro ba ne kuma ba shi da kyau wajen hasashen cewa za mu iya tuna abu ko ba za mu iya tuna shi ba.

Sabo, ba tunawa ba

Bayan sa'o'i shida na kallon littattafai ko takardun darasinka (da shan kofin shayi ko gahawa uku da 'yan ciye-ciye), abu ne mai sauki mu dauka cewa ai mun haddace karatun.

Ko wa ne shafi da ko wa ne muhimmin bayani, yana kwantar mana da hankali, mu ji a zuciyarmu cewa mun saba da shi.

Haddar ta yi wani dashe na wasu ayyuka a kwakwalwarmu da sauran sassan hankalinmu, wannan dashe shi ne yake sa kwakwalwarmu nan da nan ta dauki takardu ko rubutun nazarin namu a matsayin ''abin da ta taba gani''. To sai dai iya gane abu ba daya yake da iya tuno shi ba.

Kowane sashe na kwakwalwa akwai irin abin da ya ke haddacewa. Abin da ke karfafa kwakwalwa ta gane abu, shi ne irin saukin da bayanan suka samu wajen shiga hankali ko sassan kwakwalwarmu, kamar yadda idonmu ya rika ganin rubutun.

Sassa daban-daban ne na kwakwalwa ke taimaka wa wajen tuno abu, inda wasu daga cikin sassan suke aiki tare, domin su sake kirkiro abubuwan (bayanan) da aka sanya a kwakwalwar daga alamomin da ka ba ta.

Saboda kawai hankalin idonka yana aiki da kyau wajen sarrafa rubutun da kake dubawa, bayan ka yi sa'o'i biyar a jere kana kallon rubutun, hakan ba yana nufin sauran sassan kwakwalwarka za su iya sake kirkirar kamannin rubutun ba a lokacin da kake matukar bukatar su yi ma wannan aiki ba.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Tsabar tunanin abin da ke kan allo kadai bai isa ya sa ka iya shi ba

Nazarin yadda kwakwalwa ko zuciyarmu (tunani) ke aiki ya sa an gano sauran gurguwar fahimtar da muke yi a game da wasu abubuwan.

Misali, yawancinmu muna dauka cewa yawan tunani a kan kokarin koyon wani abu zai taimaka mana mu tuna abin. Amma nazarce-nazarce da aka yi sun nuna lamarin ba haka yake ba.

Abin da ya fi hakan dacewa shi ne sake tsara bayanin (abin da kake son koya), ta yadda zai kasance yana da wani tsarin kamanni ko sura wadda kwakwalwa za ta fi rikewa.

Ma'ana, ka sake rubuta abin da kake son kwakwalwar ta tuna ko ta haddace ko ka koya ta hanyar da za ka fi fahimtarsa sosai.

Idan ka san wasu daga cikin kurakuren tunani ko zuciyarka, to za ka iya taimakon kanka ta hanyar dauka cewa za ka gyara su.

Daga nan ne za ka yi kokarin yaki da su. Saboda haka shawarar ka rika tsara wadataccen lokaci na nazari ko karatunka na jarrabawa, za ta yi amfani ne kawai idan mun dauka cewa daman mutane ba sa ware wadataccen lokacin domin yin karatun (abin da ya fi kyau kamar yadda binciken ya nuna).

A lokacin da muke tunanin yadda za mu yi karatu, muna bukatar a tuna mana amfanin yin nazari ko karatun jarrabawa a wadataccen lokaci, saboda ya saba da tunaninmu na dogaro da sabo da abin da muka karanta (hadda).

A takaice dai wani lokacin za mu yi mamakin irin dimbin amfanin da za mu samu idan muka saba wa tsarin tunaninmu da muka saba bi.

Ya za ka ware yawan lokacin da za ka rika koyo ko nazari? Amsa: ya dan fi yawan yadda kake so.

'Yan magana sun ce, 'ka tashi (tafiya) a lokacin da kake so, sai ka je a lokacin da ba ka so. Kuma ta shi a lokacin da ba ka so, sai ka ga ka je a lokacin da kake so'.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Memory: Why cramming for tests often fails