Ko tabin hankali na kara basira?

Hakkin mallakar hoto istock

Yawanci an yi amanna cewa larurar tabin hankali na kara basira, to amma mece ce shedar da ke tabbatar da hakan?

Claudia Hammnond ta duba mana

Kowa zai iya bayar da misalin wasu fitattun mutane daga Vincent Van Gogh da Virginia Woolf zuwa Tony Hancock da Robin Williams, wadanda dukkaninsu za a iya cewa 'yan baiwa ne idan ana maganar basira, amma kuma dukkaninsu suna da larurar tabin hankali.

Akwai misalai da yawa da ke nuna cewa akwai alaka tsakanin basira da larurar tabin hanakali. Ko binciken kimiyya zai tabbatar da wannan? Ko alama.

A gaskiya ma bayanai masu kyau da ake da su a kan wannan lamari kadan ne. A nazarin da aka yi na wasu littattafai guda 29 kafin shekarar 1998, guda 15 sun ga cewa ba wata alaka tsakaninsu, guda tara kuwa sun ga cewa akwai, sannan kuma guda biyar ba su iya ganowa ba.

Saboda haka abu ne mai wuya a iya samun alaka kai tsaye tsakanin basira da tabin hankali. Kuma wasu daga cikin nazarce-nazarcen, ba wai bincike ba ne na musamman aka yi domin gano alakar.

Daya daga cikin abubuwan masu wahala a kan lamarin shi ne, abu ne mai wuya a iya fassara mene ne basira, saboda haka masu bincike kan yi amfani da wani abu daban a matsayin basira.

Misali wani nazari na 2011 ya karkasa mutane ta hanyar ayyukansu, inda ya dauka duk wanda ke da wata sana'a ta hannu kamar mai daukar hoto ko zayyana , ko kimiyya dole ne ya zama mai basira, ko da ya aikinsa yake.

Ta hanyar amfani da bayanan gwamnatin Sweden, masu bincike sun gano cewa mutanen da suke da yanayi na wani lokaci su zama masu tabin hankali wani lokaci kuma su zama kalau, kashi 1.35 sun fi zama masu basira.

Amma kuma babu wani bambanci idan ana maganar matsalar damuwa ko zakuwa. Saboda wadannan kananan ayyuka na daga ciki. Saboda an sanya wadannan wadannan ayyuka a ciki, wannan bayani ba zai iya nuna mana cewa ko mutanen da ke ayyuka na basira sun fi gamuwa da larurar tabin hankli ba, ko kuma akanta-akanta (accountants) ba lalle ba ne su gamu da larurar.

Hakkin mallakar hoto istock

Yawancin nazarin da ake amfani da shi a matsayin hujja, wanda ke nuna akwai alaka tsakanin abubuwan biyu, ya hada da wani bincike da Nancy Andreasen ta wallafa a 1987, inda ta kwatanta marubuta 30 da kuma wasu wadanda ba marubuta ba ne su 30.

Marubutan sun fi zama cikin yanayi na gamuwa da larurar tabin hankali daga lokaci zuwa lokaci a kan wadanda ba marubutan ba. Wannan dai wani dan karamin misali ne da ya kunshi marubuta 30 kawai da aka yi wa tambayoyi a shekara 15, kuma ko da yake ana yawan bayar da misalin binciken amma yawanci kuma ana sukar shi, saboda an gano larurar tabin hankalin ta hanyar tattaunawa da su ne, kuma ba a san wadannan ka'idoji aka yi amfani da su wajen tabbatar da suna da tabin hankalin ba.

Haka kuma shi mai tambayar ba a kare sirrin ta yadda ba zai iya gane cewa wannan marubuci ba ne, wannan kuma ba marubuci ba ne daga cikinsu, wanda hakan zai iya shafar sakamakon binciken.

Sannan kuma, marubutan sun zabi su halarci wani taron karatun-ta-natsu na marubuta, wanda an san hakan wani wuri ne da mutane ke neman mafaka , saboda haka zai iya kasancewa wadannan marubuta da aka gano suna da larurar, kila ba su ji dadin yanayin wurin ba ne.

Akwai kuma wasu nazarce-nazarce biyu da ake yawan gabatarwa a matsayin sheda ta tabbacin larurar tabin hankali da basira. Na farko Kay Redfield Jamison ce ta yi, marubuciyar da ta yi suna saboda fitaccen littafinta (An Unquite Mind).

Nan ma dai binciken ya ta'allaka ne ga tattaunawa, amma a wannan karon da masu wake, da marubuta littattafai da kuma marubuta tarihin mutane da kwararu a kan abubuwa na adabi ko zane, inda binciken ya kunshi mutane 47. Mai binciken ta gano abin mamaki, domin kusan rabin yawan masu waken sun taba neman maganin larurar tabin hankali.

Ko da yake ana ganin kamar mutanen da wannan nazari ya shafa suna da yawa, amma kamar yadda masu lura da al'amura suka gani bincike ne da ya shafi mutane tara kawai.

Hakkin mallakar hoto istock

Akwai kuma binciken da Arnold Ludwig ya yi wanda ya kunshi mutane da dama, inda ya nazarci tarihin fitattun mutane sama da dubu, kuma ya gano cewa kowa ne irin aiki yana da irin matsalarsa.

Matsalar ita ce ko da yake ba shakka fitattun mutanen suna da baiwa sosai (misali Winston Churchill da Amelia Earhart), sai dai ba lalle ba ne a ce sun amsa sunan masu basira kamar yadda ainahin ma'anar kalmar take.

Duk da cewa a kan gabatar da rubutunsa mai tsawon gaske a matsayin shedar alakar basira da larurar hankali, amma shi kansa Ludwig ya yarda da kansa a wata kasida cewa, babu wata sheda da ta tabbatar da cewa an fi samun larurar hankali a wurin mutanen da suka yi fice, ko kuma a ce dole sai da larurar mutum zai yi fice.

To tun da dai shedar alakar abubuwan biyu ba ta da wani girma, kuma kamar yadda wasu nazarce-nazarcen ma suke nuna wa babu wata alaka tsakanin basira da tabin hankali, me ya sa ake ma tunanin akwai din, kuma hakan ya tsaya wa mutane a hankalinsu?

Dalili daya shi ne, mutane suna ganin tunani na daban ko ta wata hanya da ba a saba ba(kamar hauka) na iya taimaka wa basira. Wasu kuma na ganin dangantaka tsakanin basira da hauka aba ce da ke da sarkakiya fiye da yadda ake tsammani, cewa larurar hankali tana ba mutane damar tunani na basira fiye da wasu, amma kuma wannan basira na raguwa lokacin larurar ta yi tsanani.

Wannan ne ma ya sa a wani lokacin larurar tabin hankali ke iya hana mutane yin abin da suke son yi ma gaba daya.

Ba mamaki akwai illar yarda cewa akwai alaka tsakanin basira da tabin hankali, domin wasu mutanen sun yarda cewa larurarsu na kara musu basira, kuma hakan ma na hana su shan magani, saboda fargabar cewa yin maganin zai iya rage musu basira ko ma su rasa ta baki daya.

To amma akwai hadari a ce mutane sun danganta basirarsu ga larurarsu maimakon baiwarsu? Sannan ina kuma maganar wadanda suke rayuwa da larurar tabin hankali, amma kuma suka ga ba su da wata basira ta daban?

Ko akwai wani matsin lamba a kansu su ji cewa lalle dole sai sun yi fice, kuma su ji ba dadi idan ba su yi ficen ba?

A karshe dai ba na jin mutane na cigaba da tunanin cewa akwai alakar basira da larurar hankali saboda abu ne da suke jin dadinsa.

A ce muna jin dadi idan muna da larurar hankali saboda wai tana bude mana basira, kuma a ce muna jin dadi idan ba mu yi tunanin ba, saboda daukar cewa idan har mu masu basira ne ta daban to fa akwai matsalar da ke tattare da hakan.

To kila dai za mu iya cewa wannan tunani ya ci gaba da wanzuwa a hankalinmu saboda kawai muna son ya cigaba da kasancewa.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Does mental illness enhance creativity?