Abin da ba ka sani ba game da zabe

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Mutane na jefa kuri'a ne bisa ra'ayinsu, ko? To ka sani ba lalle haka abin yake ba, ba lalle ba ne a ce muna da iko da tsara ra'ayinmu yadda muke so, kamar yadda muke dauka cewa duk abin da muka zaba bisa radin kanmu ne.

Ga nazarin Zaria Gorvett

Kana hawan jirgin kasa za ka ji wani zarni ya buge ka a hanci, zarnin fitsari. Sai ka zauna. Fasinjan da ke fuskantarka sai ka ji ya yi atishawa. Can kuma ba ka ankara ba sai ka ji ka taka cingam. Duka wadannan abubuwan ba su harzuka ka ba tukuna?

Yanayin da ka kasance bayan da ka gamu da duk wadannan abubuwan, ka iya bayyana halinka fiye da yadda za ka yi tsammani. Kai hatta ra'ayinka na siyasa wannan zi iya bayyanawa.

Wannan ba shi kadai ba ne ke sauya ra'ayin mutum na siyasa ba tare da ka sani ba. A duk lokacin da zabe ya kusa, masu zabe sukan dauki watanni suna ta fama da nazarin manufofin 'yan siyasa da su 'yan siyasar da kuma akidu.

Idan kama ranar zabe ta zo, lokaci ne na tsayawa a yi lissafi a akwatin zabe. Ko ba haka ba?

Duk da wadannan abubuwa da kake yi, masana tunanin dan adam da yawa na ganin ba lalle ba ne, muna da ra'ayin kanmu wurin jefa kuri'ar kamar yadda mu muke dauka.

Ba shakka akwai maganar ilimi da lafiya da tattalin arziki idan za ka zabi dan siyasa, to amma akwai wasu abubuwan kuma da za su karkatar ko kuma yi tasiri wajen sauya ra'ayin mai zabe.

Wadannan abubuwa sun kama daga yadda kake da saurin bata rai da yadda mutane ke da saurin jin tsoro da yadda suke yi idan yanayi na sanyi ko zafi ko ruwa ya sauya da kuma irinmartaninsu ga sakamakon wasa misali na kwallon kafa.

Abu ne sananne cewa matakan da muke dauka ko hukunci ko ra'ayin da muke dauka yawanci tunani ne da ba mu ma san muna yi ba, da yanayinmu da kuma ra'ayi ko san kanmu, su suke sa mu karkata wurin daukar wannan mataki ko yanke wannan shawara.

John Krosnick, farfesan kimiyyar siyasa a jami'ar Stanford ya shafe kusan rayuwarsa ta aiki a kan wannan lamari. Malamin ya bayyana cewa, '' daga abin da muka sani na shekara 50 na nazarin tunanin dan adam, shi ne za ka iya raba kwakwalwa gida biyu. Kuma a zahirin gaskiya duk wani hukunci ko shawara da mutum ke yankewa yanayi ne ba tare da ya sani ba.''

Krosnick ya ce, a lokacin muhawarar talabijin, ko da yake masu zabe suna sauraron 'yan takara, akwai wasu abubuwan da za su iya tasiri a kan ra'ayin masu zabe ko ma fiye da muhawarar da suke sauraro.

Misali shi da abokan aikinsa sun gano cewa a zaben shugaban Amurka na 2008, masu zabe da dama batun kabilanci ko jinsi ya yi tasiri a kansu wajen zaben Barack Obama da John McCain, fiye da yadda su masu zaben suka gano.

Mutane masu ra'ayin bambancin launin fata, abin da yake a jikin mutum ba tare da ya sani ba, ba lalle ba ne su zabi Obama.

Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Bincike ya nuna masu ra'ayin rikau na siyasa sun fi saurin nuna kyama

Yoel Inbar farfesan tunanin dan adam a jamia'r Toronto, ya yi nazarin wata hanyar ta boye da ka iya tasiri a kan ra'ayoyinmu, inda abubuwan da suke sa mu ji haushi ko kyama ke karkatar da ra'ayinmu.

Masanin ya yi gwajin auna yadda abu zai yi saurin bata ran mutum, inda ya tara mutane ya yi musu gwaji da wasu maganganu na kazanta, kamar a ce, ''ya za ka ji idan ka gano cewa sau daya a mako abokinka yake sauya singiletinsa?''

Daga nan ne kuma ya yi nazari a kan ra'ayin wadannan mutanen na siyasa bisa abin da ya gano na saurin bacin ransu ko kyama kamar yadda ya gano a gwajin da ya yi musu na farko.

Farfesan ya gano cewa wadanda suke saurin bata rai ko nuna kyama sun fi samun ra'ayin rikau na siyasa. Ya ce, ''muna da bayanai kusan a kan duk wani bangare na duniya in ban da yankin Afrika na kudu da hamadar Sahara. Kuma mun ga yadda abin yake zama daidai,'' in ji Inbar.

Wasu masu binciken kuma sun nuna cewa yanayin da mutum yake a rana na iya yin tasiri a kan ra'ayinsa shi ma. Wani nazari da aka yi ya nuna cewa ka sa mutane su yi tunani a kan wata cuta, zai iya sa su ra'ayi na wariyar launin fata.

Haka kuma wani nazari da aka yi a Amurka a 2014 ya gano cewa, mutanen da suke wani rashin lafiya za su fi zabar dantakara mai siffa mai kyau fiye da abokin hamayyarsa wanda bai kai shi kyawun siffa ba.

Hakkin mallakar hoto Getty

Inbar ya ce, ''dabi'ar da mutane ke yi sakamakon dabi'ar garkuwar jiki (ta kyamar wani abu mai ta da hankali ko kazanta), abu ne da muke dauka a matsayin na gargajiya''.

Ya kara da cewa abu ne da ya jibanci kauce wa mutanen da ba ka saba da su ba, da bin dabi'un da aka saba da su na al'ada, sannan kuma da bin hanyoyi na al'ada na jima'i. Kyama yanayi ne da ke ce maka 'kai kada ka yi wannan abin, zai cutar da kai'.''

A wani binciken abin mamaki, Inbar da abokan aikinsa sun gano cewa, sanya mutane su ji wata kayama, ta hanyar sanya musu wani abu mai wari ko doyi a daki, ya kan iya sa su yi watsi da tsirarun mutane, kamar 'yan luwadi da madigo

Akwai wani dan siyasa a Amurka da a shekarun baya ma, ya sanya wa 'yan takardun yakin neman zabe da ake raba wa masu zabe warin shara, inda yake nuna cewa wata manufa da wani abokin takararsa ke yadawa tana wari.

Binciken Krosnick ya nuna cewa idan 'yan siyasa suka rika bayar da fifiko wajen fito da gazawa ko raunin abokin hamayyarsu, hakan yana kara wa magoya bayansa kwarin gwiwar su fito su zabe shi.

Kuma masanin ya gano cewa idan son 'yan takara ya zo kusan daya, hakan ba ya karfafa wa mutane guiwa kan su fito su yi zabe. Nazarce-nazarce sun kuma nuna cewa mutane sukan ki zabar dan siyasa idan wasu abubuwa sun dame su ko da kuwa ba su shafi siyasa ba.

Babban misali a nan shi ne takarar AlGore da George W Bush a 2000. Zaben ya biyo bayan tarin matsalar fari da ambaliyar ruwa. Masana kimiyyar siyasa sun ce mutane miliyan biyu da dubu 800 sun ki zabar Al Gore saboda jihohinsu suna fama da fari ko kuma ambaliya.

Hakkin mallakar hoto Chris WareGetty Images
Image caption Mummunan yanayi (ruwan sama ko iska da sauransu) na iya tasiri kan zaben da mutane ke yi

Irin wannan mataki ba ya tsaya ba ne kan yanayi kadai, har da wasan kwallon kafa da sauran wasanni da kuma wasu abubuwan abubuwa.

To idan mutane suna zabe ne bisa wani ra'ayi nasu da ba su ma san yana tare da su ba, wannan na rage ingancin zaben kenan? ''Wannan tambaya ce mai ban sha'awa.'' In ji Inbar, ya kuma kara da cewa, ''idan zan iya bayyana dalilin da ya sa kake son askirim (ice cream), to kenan sai a ce bai dace ba da kake son askirim? Bana jin haka.''

Amma kuma duk da haka yana da kyau ka san abubuwan boye da suke sa mutum ya bi wani ra'ayi, nan gaba idan ka jefa kuri'a.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The hidden psychology of voting