Ainahin abin da ya sa maza ke ajiye gemu

Hakkin mallakar hoto Getty

Za ka dauka cewa duk gashin da kake gani a fuskar maza a titi kama daga gemu da gashin baki zuwa hana karya wata hanya ce ta neman jan hankalin musamman mata. Abin ya wuce haka.

Ga bayanin Tamsin Saxton ta jami'ar Northumbria

Mene ne amfanin gemu, idan ana magana a kan asalin dalilin halitta? Yara da mata da kuma wasu tarin mazajen ba su da shi kuma ba abin da ya dame su.

To amma ka fita titi a yanzu ka duba za ka ga mutane da gashi a fuskarsu iri-iri, gemu ne ko gashin baki ko hana karya, da gyara ko tsari iri daban-daban..

Idan muka ga maza na gyaran jikinsu(fuska) sai mu dauka suna yin haka ne domin jan hankali ko birge mata, amma bincikenmu a kan gemu da murya ya nuna mana cewa watakila gemu ya samo asali ne domin ya sa mutum ya fi 'yan uwansa maza kwarjini.

Idan aka kwatanta da maza da matan birrai da dama, maza da mata (na mutane) akasari sun bambanta daga juna yawanci saboda gashin fuskar mazan.

Kuma idan muka ga irin wannan bambanci tsakanin maza da mata sai mu danganta shi da yadda bambancin halitta ya faro tsakanin maza da mata, abin da ke kara tasiri wajen jan hankali ko sha'awa tsakanin halittun biyu.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ba lalle ba ne gemu ya ja hankalin mace

To amma kuma wani abin mamaki shi ne mata ba su damu da gemun maza ba. Duk da cewa wasu nazarce-nazarcen sun nuna cewa mata suna son gashi kadan a fuskar maza ko ma da yawa, wasu nazarce-nazarcen kuwa sun nuna cewa mata sun fi son mazan da suka yi gyaran fuska gaba daya.

Rashin cikakkiyar sheda na nufin ba za mu iya ayyana cewa gemu ya samo asali ba ne saboda mata sun fi son mazan da suke da gemun ba.

Masu bincike suna ganin akwai wani abin da kuma za a iya dauka a matsayin dalilin da ya sa maza ke da gemu wanda ya shafi soyayyar mace da namiji.

Wannan dalili kuwa shi ne, idan har za ka shawo kan mace kana bukatar ka yi gogayya da sauran maza, ba kawai don kana da kyau ba a ce za ka yi galaba a kan takwarorinka maza, an ce idan kana da kyau to ka hada da wanka, saboda haka namijin da yake da gemu ana ganin ya fi maras gemu kwarjini.

Ko da yake ba wai lalle namijin da yake da cikakken gemu yana da karfin jima'i ba ne, amma bincike da dama na nuna cewa maza da mata na daukar mazan da suke da gemu a matsayin wadanda suka fi shekaru da karfi da kuma barazana.

Kuma daman mazan da suke da kwarjini da karfi za su fi samun damar shawo kan mace ta hanyar sanya tsoro a zuciyar abokan nema su ja baya.

Wannan abu ne da aka tabbatar a zamanin yau da kuma na da cewa karfi da kwarjinin namiji na ba shi fifiko wajen samun mace.

Bincike ya danganta yayin da aka yi na tsayar da gemu a Biritaniya a tsakanin shekara 1842 da 1971 ga yawan maza da mata da ke neman aure a lokacin.

Nazarin ya gano cewa a lokacin da maza da yawa suke fafutukar neman auren matan da ba su da yawa gemu da gashin baki sun zama wani abin yayi.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mai gemu Genghis Khan ya ci yawancin Asiya da yaki, wannan ya sa ake daukar masu gemu suna da karfi

Ba gemu ba ne kadai abin da ke nuna cewa namiji yana da karfi da iko, murya ma na sa a dauki namiji haka.

Mutane sun fi zabar shugabannin da suke da murya karama, kuma a yayin gasa maza sukan yi kasa kasa da muryarsu idan suna ganin sun fi abokan hamayyarsu kamannin masu nuna iko.

Kamar gemu da sauran gashin fuska, ita ma murya tana sa a iya bambancewa tsakanin maza da mata cikin sauki.

Domin gano asalin gemu da murya, mun jarraba mu ga ko ana daukarsu a matsayin masu jan hankali ko sha'awa ko nuna iko ko kuma duka biyu.

Mun bukaci maza 20 da mata 20 su auna yadda wasu maza shida da aka dauki bidiyonsu sau hudu lokacin da suka ajiye gemu, yadda kyawunsu da kuma nuna ikonsu yake.

Daga nan kuma sai muka yi amfani da kwamfuta muka kirkiri wasu hotunan bidiyon har guda hudu na kowanne daga cikin wadancan hotunan bidiyon hudu, muka sauya muryoyin mazan suka zama masu karfi da kuma marassa karfi.

Daga nan sai muka gano cewa muryar namijin da ta zama kasa da ta yawanci an fi daukarta a matsayin mafi ban sha'awa. Muryar da ta yi kasa sosai ko mai kara sosai ba su sa farin jini

Sabanin haka kuma muryar namijin da ta yi kasa sosai (mai kauri) an fi daukar mai ita da cewa zai fi nuna iko ko danniya.

Ba kasafai gemu ya yi tasiri wajen nuna kyau ko sha'awar da ake yi wa mutum ba sosai, amma wadanda suka ajiye gemu sosai an fi daukarsu a matsayin wadanda za su fi nuna iko ko danniya, kamar yadda binciken baya ya nuna.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ba lalle ba ne masu gemu suna da yawan kwayoyin halittar jima'i ba

Dambarwar da ke tsakanin batun jan hankalin mace da kuma gogayya da sauran maza ba ta tsaya ba ne a kan gemu da murya kawai.

Yawancin maza na ganin suna son a ce jikinsu na da kiba fiye da yadda mata ke cewa suna so, yayin da su kuma yawancin mata ke cewa suna son jikinsu ya kasance siriri kuma su rika yin shafe-shafe a fuska fiye da yadda maza ke cewa suna so su ga matan.

Namiji ba shi da kwarewa wajen sanin abin da mace take so, haka ita ma mace ba ta da kwarewar fahimtar abin da namiji ke so, ana ganin hakan kila ba zai rasa nasaba da cewa burinmu shi ne, mu ga mun fi sa'o'inmu ko abokanmu ba, kuma mu ja hankalin abokan soyayyarmu ba (maza ko mata).

Ba shakka yawancin wannan bincike an yi su ne a tsakanin jama'ar kasashen yammacin duniya (turawa). Amma maganar shafe-shafe da kirar jiki har ma da barin gemu da sauran nau'in gashin fuska abubuwa ne da suka bambanta sosai tsakanin al'ummomin duniya.

Amma maganar ita ce, ko da gemu ne ko kuma wani abin daban, yawanci muna ganin wannan gogayya na sa mutane su yi ado ko fita iri daban-daban.

Kana jin za ka iya burge kowa a ko da yaushe? Ko alama ba za ka iya ba!

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The real reason men grow beards