Me ke sa mu mantuwa in mun shiga ɗaki?

Hakkin mallakar hoto Getty

Akwai lokacin da kake shiga ɗaki domin ka ɗauko wani abu amma kana shiga sai ka manta abin da ka je ɗaukowa. Ko kuna zance sai kawai ka ji ka manta abin da za ka faɗa.

Wannan na nuna ƙarfi da kuma raunin ƙwaƙwalwar (hadda) mutum ne, kamar yadda masanin tunanin ɗan adam Tom Stafford ya yi nazari.

Ya taba faruwa a kan dukkanninmu. Ka hau bene ka shiga daki ka dauko mukullayenka, sai kawai ka ji ka manta me ka je daukowa a dakin. Ka bude firji, ka mika hannu sai ka ji ka manta abin da ya sa ka ma bude firjin.

Ko kuma abokinka na magana sai ka katse shi domin ka ce wani abu, amma kuma sai kawai ka ji abin da ke ci maka rai kake son ka fada ya bace maka a rai: Sai ka ji mun ce, ''Me ma nake son in ce?''

Ko da yake irin wannan mantuwar ko kuskure (Doorway Effect a Ingilishi) na iya kunyata mutum, amma abu ne da ya zama ruwan-dare, wanda kowa yake yi. Kuma tana bayyana wasu muhimman abubuwa ne na yadda tsarin tunaninmu yake.

Fahimtar wannan zai iya sa mu san wannan 'yar takaitacciyar mantuwa ba aba ce da za ta sa mu bata rai ko mu damu ba (duk da cewa abu ne da zai bata maka rai).

Ga wani labari na wata mata wadda ta hadu da wasu leburori ko magina a lokacin da suke hutun cin abinci yayin aikinsu, wanda ina ganin labarin zai fi bayyana yadda wannan yanayi na tunani ko kwakwalwarmu yake.

Matar ta tambayi mutum na farko, ''Me kake yi yau?'' sai ya ce mata, ''Ina dora bulo ne a kan bulo daya bayan daya.'' Sai ta tambayi na biyu, ''Me kake yi yau?'' sai ya buda baki ya ce mata, ''Ina gina bango ne.'' ansar da ya ba ta kenan. Shi kuwa magini na uku cike da alfahari, da ta tambaye shi, sai ya ba ta amsa da cewa, ''Ina gina katon coci ne!''

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kana buɗe firjin sai ka manta abin da ya sa ka je wurinsa ma. Amma hakan ba raunin ƙwaƙwalwa ba ne fa, aiki ne ya taru a cikinta

Watakila za ka dauki maganar mutum na uku, wanda ya debo maganar gaba daya cewa yana gina katafaren gini ne a matsayin magana mai karfafa gwiwa da burin da kake cike da shi.

Amma idan za a yi magana ta gaskiya ta hankali, abu mafi kyau da karfafa gwiwa shi ne, duk aikin da za ka yi, sai ka yi tunaninsa daki-daki ko mataki-mataki, idan dai har kana son yinsa yadda ya kamata.

Shi wannan magini na uku, kila yana cike da buri da karfin gwiwa na aikin da ke gabansu, amma kuma ai babu mutumin da zai gina wani katafaren gida ba tare da ya yi tunanin yadda zai dora bulo daya bayan daya ba yadda ya dace, kamar yadda magini na farko ya fada ba.

Yayin da muke gudanar da rayuwarmu ta yau da kullum, hankalinmu na tafiya tsakanin wadannan matakai; daga burinmu, zuwa tsare-tsare da dabarunmu, har zuwa mataki na kasa, wato ainahin aikin da za mu dukufa yi ko in ce dan ba da za mu dora (har mu cimma burin namu).

Idan abubuwa na tafiya daidai, mukan mayar da hankalinmu a kan abin da muke so, kuma kusan sai mu ki mayar da hankali kan yadda abin ke gudana, mu kyale shi yana tafiyar da kansa (domin komai na tafiya ba matsala).

Idan kai kwarren direba za ka rika tuka motarka ba tare da ka tara hankalinka wajen sanya giyar motar ko murda sitiyari ko kula wasu abubuwa na cikin motar ba, za ka ga kana tafiyar da komai a lokaci daya kamar ma baka san kana yi ba, hankalinka yana ma kan hirar da kuke yi da sauran mutane na cikin motar, da kuma yadda za ka kauce wa wannan motar ko wannan babur.

Idan abubuwa kuma suka saba da yadda muka saba yi, wani abu mai daukar hankali), ya shigo cikin tukin naka, sai ka mayar da hankali kan ainahin abin da muke yi, mu dauke hankalinmu daga babban abin da muka sa a gaba (hira ko kaucewa wannan motar da wuce waccan), na dan wani lokaci.

To wannan shi ne zai sa ka ji mun yi shiru a maganar da muke yi, yayin da direban ya zo wani wuri mai wuyar wucewa, misali mahada (motoci da yawa na bullowa ta ko'ina), ko kuma injin motar ya fara wata kara.

Yadda hankalinmu ke kai komo a tsakanin abubuwan da muka sa gaba muke yi, shi ne ke ba mu damar gudanar da abubuwa (dabi'unmu) daban-daban a lokaci daya, ko a lokuta daban-daban, ko a wurare daban-daban.

To wannan mantuwa (idan mun shiga daki mu manta abin da muka je dauka) tana faruwa ne, lokacin da hankalinmu ya ke kai-komo tsakanin matakai, kuma mantuwar, tana nuna dogaron kwakwalwarmu game da abin da muke dab da yi, a kan muhallin da muke ciki.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ƙwaƙwalwarmu na tsara jerin burunmi ɗaya bayan ɗaya, amma kuma ɗan abu kaɗan sai ya sa mu manta tsarinmu

Ka dauka ka hau bebe ka je dakinka domin ka dauko mukullayenka, sai ka manta mukullayen za ka dauka kana shiga dakin. To abin da ya faru a nan a bisa tsarin kimiyyar tuanin dan adam shi ne, ainahin tsarin naka (mukullayen), ka manta shi a daidai lokacin da kake tsakiyar aiwatar da wani muhimmin bangare na dabarar da ka dauka (zuwa daki).

Watakila shi kansa shirin naka (mukullayen) wani bangare ne na wani babban shirin (shirin barin gidan), wanda shi ma kila wani bangare ne na wani babban shirin ( zuwa wurin aiki, da tabbatar da ba a raba ni da aikina ba in zama dan kasa na gari, ko wani abin).

Kowanne daga cikin wadannan matakai na bukatar mayar da hankali da natsuwa a wani lokaci. To a daidai lokacin da kake cikin wannan aiki na aiwatar da mataki bayan mataki, sai bukatar mukullaye ta shigo zuciyarka ko tunaninka, duk da cewa ka sa tunanin hakan a tsarinka da dadewa, sai wani abu daban ya shigo ranka.

To wannan mantuwa tana faruwa ne saboda mun sauya abubuwa biyu muhallin zahiri da kuma na tunaninmu, muka nufi wani dakin daban da kuma tunanin wasu abubuwan na daban, to wannan burin da ka shigo da shi cikin hanzari, wanda kila daya ne kawai daga cikin tarin burinka, sai ka manta da shi, idan yanayin ya sauya.

Tunaninmu, hatta a game da burinmu ya sarkafu ne (wani ya shiga cikin wani) cikin tarin abubuwa daban-daban. Wannan shi ne zai iya zama muhallin da muke kirkirarsu a ciki, wanda shi ne dalilin da ya sa, sake ziyarar gidan da muka taso muna yara zai iya taimaka mana tuna wasu abubuwa da dama, wadanda muka manta da su.

Ko kuma zai iya zama muhallinmu na tunani, wato tarin abubuwan da muke tunani a kai yanzu-yanzu lokacin da wannan abu ya fado mana rai.

Wannan misali ne na yadda za ka iya ganin yadda muke iya tsara wa da kuma aiwatar da ayyu kanmu masu sarkakiya, a tare ba da wata matsala ba, ta yadda muke iya sanya komai a muhallinsa har mu kai ga cimma burin da muka sa a gaba na rayuwarmu.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Why does walking through doorways make us forget?