Wai tsoffi ba sa buƙatar barci sosai?

Hakkin mallakar hoto Getty

Muna ƙara girma yawan barcinmu na raguwa, wannan kusan shi ne abin da aka yi amanna da shi. To sai dai ga alama akwai wasu dalilai na daban da ke sa mutum saurin tashi daga barci da safe.

Claudia Hammond ta yi bincike a kai.

Abu da aka saba ji a wurin mutanen da suka manyanta ka ji cewa ba sa iya barci. Kusn rabin yawan irin wadannan mutane sukan ba da bayanin cewa suna gamuwa da matsalar barci, kuma kusan daya bisa hudu ko sulusinsu suna da matsalar kasa barci.

Ga alama akwai manyan matsaloli biyu a nan: barci a farkon dare da kuma tashi da safe da wurwuri, kuma duk da haka mutum ya kasa komawa barci.

A wani lokacin, rashin dadin da yanayin rashin lafiya ke sanya wa mutum yana kara matsalar kasa barci, amma mutane da yawa suna jin cewa ko da babu matsalar rashin lafiya, sukan kasa barci akalla zuwa wani tsawon lokaci da daddare.

Rashin barci na iya yin tasiri na dogon lokaci a garkuwar jikin mutum da sauran fannonin lafiya, ciki har da lafiyarsa, da sa mutum barci da rana da kuma yuwuwar yin hadari.

To amma fa mutane da yawa ba sa bukatar barci idan suka girma saboda haka bai kamata su damu ba idan ba sa barci sosai a lokacin da suka kai wasu shekaru na manyantaka.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jikin tsofaffi na iya hana su barci ko da suna son yin barcin

Ba abu ne mai sauki ba a iya tabbatar da yawan barcin da za a ce kowane mutum yana bukata ba daidai da shekarunsa. Ba shakka za ka iya auna yawan barcin da mutane ke samu, kuma idan ka yi haka, za ka ga yawanci mutanen da suke da shekaru ba su kai na kasa da su yawan barci ba, amma kuma hakan kawai yana nuna maka cewa suna barci kadan ne, ba wai ba sa bukatar barcin ba ne.

Wani lokaci mutane za su ce manya ba sa iya barci da daddare wai saboda sun shafe rana suna gyangadi. Amma kuma wasu mutanen za su ce yawan jin barci sosai da rana ba zai yuwu ya zama wata alama ta tsufa ba.

Ba ko da yaushe likitoci ke daukar matsalar rashin barci da manya ko tsofaffi ke fama da ita ba a matsayin wani abu na damuwa ba.

A wani nazari kashi 69 cikin dari na tsofaffi ko mutanen da suka manyanta sun bayyana cewa suna fama fa matsalar barci, amma kuma kashi 81 cikin dari daga cikin masu wannan matsala ba a ga wannan matsalar a abubuwan da ake gani na lafiyarsu a asibiti ba.

Saboda haka idan muka yi tunanin cewa tsofaffi ko manya suna bukatar barci mai yawa kamar haka, to me ya sa kenan suke barci na 'yan sa'o'i kadan?

Wani nazari da aka yi ya nuna cewa girma ko tsufan da jikinsu ke yi yana rikita aikin da jikinsu na saba yi (agogon jiki) na sa'a 24, inda yake sa su tashi daga barci tun kafin lokacin da ya kamat su farka.

Nazarce-nazarce sun nuna cewa agogon jikinsu ga alama shi ne yake sauya yanayin aikinsa, yake sa mutane su tashi da safe da wuri kuma daddare su kwanta da wuri.

Za su iya bukatar barcin duk da haka, amma kuma ba za su same shi ba, kuma idan ma sun samu to ba za su ji dadinsa kamar yadda suke ji ba lokacin da ba su kai shekarun da suke ba yanzu.

A wani sabon nazari da aka yi a Rasha, wasu mutane 130 sun shiga dakin binciken kimiyya wata rana da safe, suka zauna a na tsawon ranar har dare. Ma'aikatan wurin ba su bari sun yi barci ba tsawon lokacin, inda suke tambayarsu daga lokaci zuwa lokaci yadda suke jin barci.

Yanayin jin barcinsu ya bambanta duk tsawon ranar da kuma dare,kuma a yanayin bincike na hana mutum barci irin wannan, ana la'akari da abubuwan da ke haifar da sauyi a yanayin aikin jikin mutum (agogon jiki), kamar dumin jiki a lokuta daban-daban na rana da kuma sakin sinadarin da ke sa barci (melatonin)da jiki yake yi da almuru.

Haka kuma a lokuta da dama an auna yadda kwakwalwar mutanen ta rage aiki da rana da kuma da daddare.

Daga nan sai aka yi nazarin dukkanin wadannan bayanai da aka tattara aka kwatanta su da bayanin lokacin da mutanen ke barci na sati daya da suka rubuta kafin a yi wannan gwaji da su, domin a ga yadda yanayin barcin nasu da aikin da kwakwalwarsu ke yi a hankali suka bambanta daga yanayinsu na marassa barci da wuri da dadare ko kuma masu saurin tashi da safe.

A nan ma sai aka sake ganowa cewa masu yawan shekaru a cikinsu sun rika jin barci a lokuta daban-daban fiye da wadanda ba su kai su shekaru ba, kuma suna da bambancin lokacin da kwakwalwarsu ke rage yawan aiki.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Raguwar sinadarin barci (melatonin) da jikinmu ke samarwa idan mun fara shekaru na iya shafar yanayin barcinmu

Jagoran binciken, Arcady Putilov ya a ganin abubuwa biyu ne kila suke jawo raguwar barcin. Yana ganin a lokacin da mutum yake tsakiyar shekarunsa agogon aikin da ke sa jikinsa barci yana yin rauni, wanda hakan ke sa da wuya ya iya barci, kuma idan mutum ya kai shekaru na girma sai babban agogon aikin jikinsa ya yi rauni, saboda sauyi a yanayin dimin jikinsa da kuma yadda jikin ke sakin sinadarin da ke sa shi barci (melatonin) ya yi rauni.

Bayanan da aka tattara da wata sabuwar mashigar wani shafin intanet (app; Entrain) wadda aka kirkiro domin taimaka wa masu larurar da mutane kan samu a sanadiyyar yawan tafiye-tafiye a jirgin sama, sun kara jaddada nazarin da ke nuna tasirin agogon jikin mutum wajen jirkita yanayin barcin tsofaffi.

Bayanan da aka tattara a sakamakon amfani da hanyar sun nuna cewa kila barcin da tsoffin ke yi da rana ba shi ke hana su barci da daddare ba. Maimakon haka rashin barcin da suke yi da daddare shi ke sa su barci da rana, domin biyan bashin da suka ci da daddare.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kuna bukatar kailula idan kun ci bashin barci da daddare

Mahawarar ba ta tsaya a nan ba. A wani nazari na shekara ta 2008, wanda aka yi a asibitin mata na Brigham a Amurka, an ba wasu mutane damar yin barci tsawon sa'a 16 a rana, har na tsawon kwanaki.

'yan shekara 60 zuwa 72 sun rika barcin sa'a bakwai da rabi kullum, yayin da 'yan shekara 18 zuwa 32 suka rika barcin sa'a tara.

Za ka iya fassara wannan da cewa matasan suna bukatar barci fiye da manyan, to amma ai kila sun fi manyan gajiya ne kuma kila da sun ci bashin barci, saboda ba sa kwanciya da wuri.

Wannan nazarin bai kawar da yuwuwar cewa agogon aikin jikin manyan shi ne yake hana su barci ba ko da kuwa suna bukatar yinsa.

Amma kuma nazari na gaba da masanan suka sake yi wannan karon a jami'ar Surrey ya kara da wani salo kuma. Domin a wannan karon an umarci mutanen da su yi barci a lokuta daban-daban na rana.

A nan ma sai tsoffin suka kasa yin barcin, abin da ke nuna kila agogon aikin jikinsu ne ya hana su, ko kuma ba su ci bashin barci ba kamar yadda matasan suka ci.

To a wanna karon masu binciken sun tabbatar da cewa ba su yi barci ba. Sai suka rika nazarin aikin kwakwalwarsu duk tsawon dare, duk lokacin da suka ga alamun kwakwalwarsu za ta rage aiki (barci zai zo) sai su kunna wani kida ko kara da zai hana su barci.

Washegari tsoffin sun gaji tibis har barci ya kwashe su kamar yadda yake yi wa matasan. Wannan na nuna cewa idan har suna bukatar barci, za su samu su yi, sauran lokutan barcin bai kama su ba saboda ba a hana su yinsa ba.

Bayan nazarin bincike 320, kwamitin wasu kwararru wanda hukumar tabbatar da lafiyar barcin jama'a ta Amurka ta bayar da shawarar mutanen da suka kai shekara 64 su rika samun barci da daddare na sa'a bakwai zuwa tara, wadanda suka kama daga 65 zuwa sama su rika samun barcin sa'a bakwai zuwa takwas duk dare.

Duk da haka dai maganar sauyin yanayin agogon aikin jikin mutum ba aba ce da za a yi watsi da ita ba, yayin da muke kara shekaru. Saboda haka wannan abu ne da ba za a ce wani abu ne da ba za a ce kamar almara ba ce ko wani abu da ya fi karfin sanin mutum cewa manyan mutane ba sa bukatar barci mai yawa.

Abin da muka sani dai yanzu shi ne a duk lokacin da ka yi kokarin yin barci, a lokacin ya kamata ka yi shi kuma ka gagara runtsawa, kuma ga gajiya a tare da kai, to wannan abu ne da ya kamata ka dauki mataki a kai sosai.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The truth about whether you need less sleep as you get older