Ko kun san kuna yi wa kunnenku illa?

Hakkin mallakar hoto science photo library

Yawancinmu muna amfani da abin sauraren sauti na sanya wa a kunne wanda muke kira iyafon (earphone), kusan a duk tsawon rana, a wurin aiki ne ko a lokacin da muke kan hanyarmu ta zuwa wurin aikin. Anya ta yin hakan ba muna lalata kunnenmu ba ne a hankali?

Molly Crain ta bincika lamarin.

Abin ya fara a sannu a sannu. Ka daina jin amon kidan jita a wakar da ka fi so sosai kamar yadda a da kake ji, saboda haka sai ka kara karar rediyonka. Hirar da ake yi a talabijin sai ka kasa kunnenka sosai ka ji. Sauraron abin da abokanka suke fada a cikin taro ya zamar maka wahala.

Yawanci matsalar daina ji ba wai tana samun mutum ba ne lokaci daya kwatsam, tana samunmu ne a hankali a hankali. Wasu kwarraru na ganin dabi'unmu na zamani kamar yawan amfani da muke yi da abin sanya wa a kunne domin sauraron kida ko fim hakan na sa mu samu matsalar ji (kunne) da wuri.

Kuma wannan ita ce matsalar da za ta iya shafar matasan manya fiye da yadda ake gani a da.

Me zai sa in damu da jina (kunne)?

'' Abin mamaki ne ka ga yawan fannin rayuwarka da ke gamuwa da kara (sauti mai yawa) wanda ba ka ma sani ba har sai mai faruwa ta riga ta faru,'' in ji kwararriyar likitar ji, Jill Gruenwald, ta jami'ar Vanderbilt, a Nashville, Tennessee da ke Amurka. Ta kara da cewa, '' Kara iri daban-daban na sauti na kewaye da mu, mune amfani da iyafon da halartar wuraren kada-kade da sinima wadanda duk ana sa sauti mai kara sosai. Dukkanin wadannan hanyoyi ne da muke gamuwa da sauti mai kara a kullum.''

Hakkin mallakar hoto Getty

Gruenwald wadda ta gabatar da lacca a kan hadarin yadda ake rasa ji a makarantar koyon kade-kade da waka ta jami'ar Vanderbilt, ta bayyana cewa idan mutum yana yawan samun kansa inda kara mai yawa yake, hakan zai iya kara masa hadarin gamuwa da matsalar ji wadda kara ke haddasawa.

Akwai dalilan da ke nuna cewa mutum zai iya fara samun wannan matsala ta rashin ji sakamakon kara tun yana yaro walau a sanadiyyar sana'arsa, ko abubuwan nishadi, musamman a cibiyar kade-kade da wake-wake ta Nashville.

''Wani lokacin illar karar sautin da kake gamuwa da ita tun kana yaro ba ta bayyana sai ka fara shekaru sai ta fito bakatatan, ba saurarawa,'' in ji Gruenwald.

Wane irin sauti ko kara ne zai iya yi min illa a lokacin nishadi?

Hukumomin tabbatar da kare lafiyar jama'a a wurin aiki ( National Institute for Occupational Safety (NIOSH) and Occupational Safety and Health Association (OSHA), sun sa mizanin karar ya zama daidai da (85 decibels), hayaniya da karar da ake iya ji ta ababan hawa a kan titi a cikin wani birni, a cikin mota.

Duk karar da ta fi haka to za ta iya yi wa jin mutum illa a sannu a sannu. Illar za ta iya faruwa a lokacin da mutum ya samu kansa a cikin wannan kara ko hayaniya, amma kuma abin da aka saba gani shi ne illar ka iya bayyana can gaba a rayuwar mutum lokacin da ya fara tara shekaru.

Iyafon da matasa maza da mata kan sa a kunne domin sauraren wake-wake da kade-kade suna sa kara sosai (120 decibels) kamar yadda wani nazari da ka yi a jami'ar Leicester ya nuna, wannan hadari ne kwarai domin duk karar da ta wuce 110dB za ta iya yi wa kunne illa, kuma irin wannan illar ba za a iya gyara ta ba.

''Kayayyakin laturoni (rediyo da mp3 da mp4 makamatansu) suna fitar da karar da ta kai ta 90dB,'' in ji Dakta Todd Ricketts na jami'ar Vanderbilt. ''injin yankan bishiya da karamin kwale-kwale mai inji na tsere kararsu ta kai 100dB, idan kuwa kana maganar kara mai yawa ne, misali a gidan rawa ko wani dandalin waka za ta iya kaiwa 105dB.

Rediyon mota mai kara sosai kuwa za ta iya kaiwa kusan 120dB ko ma fiye da haka. Idan kuma kana maganar 'yar tazara tsakaninka da bindiga to karar ta kai 140dB wadda ta kai ko ma ta wuce karar da za ta iya sa ka dan daina ji.''

Mutane da yawa sukan sami matsalar daina ji ta 'yan wasu kwanakai bayan sun je wani taron kade-kade da wake-wake ko wurin wata liyafa da aka yi kade-kade, amma daga baya jin nasy yana dawowa.

Idan ka samu kanka a yanayin da jinka ya dauke na wasu kwanaki, sai ka je wani wuri da ba hayaniya ko kara, har sai jin naka ya dawo, daga nan kuma sai ka tabbatar cewa ka daina zuwa wurin da za ka sake gamuwa da irin wannan matsala a nan gaba.

Ta yaya zan gane idan jina ya fara raguwa?

Idan ya kasance lokacin kana yaro ka samu kanka a yanayi ko wuri da ke da kara ko hayaniya sosai, idan ka tsufa za ka iya gamuwa da larurar ji matuka, ko ma ka samu matsalar tun kana matashi.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Matsalar kunne na faruwa a hankali ba tare da an sani ba

Wani hoton bidiyo da AsapScience suka sa a YouTube a 2013 ya zo da tambayar ''Shekarun kunnenka nawa?'' Matsalar ita ce, kila ba za ka so sakamakon da za ka gani ba, domin kunnen zai iya kasancewa ya tsufa da shekara 20 a kan shekarunka.

Idan kana da wata fargaba ko damuwa a game da lafiyar kunne ko jinka, akwai hanyoyin da za ka gwada lafiyar jin naka kafin ka je wurin likitan kunne.

Idan kana amfani da wayar iPhone, Uhear na daya daga cikin gwajin da aka fi yi. An kuma samar da gwajin Mimi a watan Afrilu na 2015, wadda ita kuma za ta sa ka yi amfani da iyafon (earphone) na Apple domin samun kyakkyawan sakamo. Bayan gwajin za ka iya sanin matsayin shekarun jinka (kunnenka).

Idan kuma kana amfani da Android ne, to akwai gwajin da za a yi maka wanda har ma za a iya wallafa sakamakon a takarda ko ma ka aika shi ta email

Ta yaya fasaha za ta iya taimakawa?

Ga wadanda suke samun matsalar daukewa ko raguwar ji kadan-kadan, za su iya amfani da wata fasaha (app) da tsohon likitan kunne Rodney Perkins, ya kirkiro, mai suna Soundhawk, wadda fasaha ce da ake amfani da ita ta hanyar Bluetooth.

Ta yaya zan iya dakatar da matsalar jina daga tabarbarewa?

Hanyar da za ka iya dakatar da matsalar daga ci gaba, sai ka rage karar wayarka, kamar zuwa kashi 70 cikin dari. Kuma idan za ka je wani wajen kade-kade to ka tafi da abin toshe kunne (wasu 'yan robobi na musamman), domin ba ka san ko za ka samu kanka a kusa da wata lasifika, ko amsa kuwwa mai kara ba.

Ka rika amfani da abin sauraron sauti babba wanda ake iya rage sauti ta yadda wani kara na daban ba zai shigo maka ba maimakon iyafon dan karami da ake cusawa a kunne.

Wannan kila ita ce hanya mafi sauki da a yanzu za ka iya tabbatar da cewa wakoki da kade-kaden da kake jin dadin sauraro ba su raba ka da arzikin jinka ba.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Are you damaging your hearing without realising it?