Shin zurfin ciki yana da illa?

Hakkin mallakar hoto Getty

A bisa al'ada ana ɗaukar 'yan Burtaniya a matsayin masu zurfin ciki da ƙin bayyana damuwarsu. Amma akwai shedar da za ta tabbatar da wannan fassara da ake yi musu? Shin ma kuma yin gum da bakinka a kan wani halin damuwa da kake ciki abu ne maras kyau?

Linda Geddes ta yi mana nazari

Amurkawa ba su da boye-boye kai tsaye suke abinsu; Faransawa kuwa sun iya soyayya da taurin kai. To amma akwai wata dabi'a da za a iya danganatawa da 'yan Burtaniya, watakila ba za ta wuce, karfin halin boye abin da yake damunsa ba, ko kuma in ce zurfin ciki.

Yawanci kuka a bainar jama'a a Burtaniya in dai ba a 'yan wasu lokuta na daban ba, abu ne da ake kyama; galibi dan Burtaniya ya gwammace ya kame kansa, kawai ya ci gaba da rayuwarsa idan wani abu na damuwa ya same shi.

Haka yawanci ake fassara 'yan Burtaniya. To amma a zahirin gaskiya yadda ake daukar nasu haka suke?

Kuma idan muka bar maganar kasar mutum, idan ya kasance kai mutum ne mai zurfin ciki, wannan na nufin kenan kai jarumi ko kuma wanda abu ba ya damunsa?

Duk da wannan fassara da ake yi wa 'yan Burtaniyan, wannan dabi'a tasu ta kame bakinsu gum, ta takaita ne na dan wani lokaci a tarihin kasar- daga shekarun 1870 zuwa 1945, in ji Thomas Dixon, darektan cibiyar nazarin tarihin yanayin mutane, a jami'ar Queen Mary da ke Landan, wanda kuma shi ne marubucin littafin Weeping Britannia.

Ya ce ''dabi'a ce da aka santa da 'yan mulkin mallakar da suka yi karatu a makarantar gwamnati, wadanda suka rika kewaya duniya suna yi wa kasashe mulkin mallaka.''

Hakkin mallakar hoto Alamy

Kafin wannan, mutanen Burtaniya, mutane ne da suka damu da halin da suke ciki. Hatta 'yan kasar da a zamanin Sarauniya Victoria da ake dauka masu zurfin ciki, a ainahin gaskiya mutane ne masu tausayi da kishi.

Mu dauki misalin Charles Dickens, wanda ya yi amfani da mawuyacin halin da Tiny Tim, na littafinsa na Christmas Carol, yake ciki ya sa Sarauniya Victoria wadda take matashiya a lokacin, ta fashe da kuka, lokacin da ta ji irin tafi da sowar da ake yi mata lokacin da aka bayyana sunanta a matsayin sarauniya a 1837.

Kamar yadda Dixon ya bayyana, wannan dabi'a ta zurfin ciki ta fara sassautawa bayan yakin duniya na biyu; zuwa shekarun 1960 irin kwararrun matan nan (Agony Aunt) masu taimaka wa mutanen da suke fama da wata matsala ta rayuwa da shawarwari, a fili suka rika gaya wa mutane da su fito fili su bayyana abin da ke damunsu.

Dixon ya ce, duk da irin fina-finan da aka rika nunawa da shirye-shiryen talabijin na abubuwan ban tausayi da aka rika yi, domin sauya wannan yanayi na mutanen kasar a lokacin, dabi'ar zurfin cikin kusan ta zamar musu wata alama ta bege.

A bisa wannan kila za a iya cewa har yanzu 'yan Burtaniya ba su kai sauran 'yan wasu kasashen ba nuna damuwa. Duk da cewa masana kimiyya ba su yi wani bincike a kan 'yan Burtaniya ba, akwai alamun bambancin al'ada na nuna damuwa ko yanayin damuwa tsakanin gabashi da yammacin duniya.

A misali ana ganin mutanen Japan sun fi nunawa idan sun aikata laifi ko wani abin kunya ko bashi da kuma kusanci ko shakuwa da jama'a, idan aka kwatnta da Amurkawa da 'yan kasashen Turai, wadanda suka fi bayyana bacin rai da damuwa da alfahari.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mutanen Japan

Wasu daga cikin wadannan sun dogara ne ga irin muhimmancin da kowace al'umma ta dora a kan wani yanayi. ''Yadda al'ummar muhallinka suke daukar abu da yadda kake tunanin za su yi martani shi zai nuna yadda yanayinka zai kasance, in ji Batja Mesquita mai bincike kan yanayin mutane a jami'ar Leuven da ke Belgium.

Za kuma a iya samun tasirin bambancin al'ada kan yadda mutane suke da niyyar nuna abin da ke damunsu ko yanayin da suke ciki. Wani bincike da jami'ar Oxford ta yi a kan 'yan Burtaniya sama da 2,500, a 2007, ya nuna kasa da kashi 20 cikin dari na 'yan Burtaniya suna ikirarin cewa ba sa boye komai, suna bayyana cikinsu, a cikin sa'a 24 da ta wuce, duk da cewa kashi 72 cikin dari nasu, sun yarda cewa boye damuwa a rai illa ce ga lafiyar mutum.

Kuma kashi 19 cikin dari na wadanda aka yi binciken a kansu, ba su iya tuna lokacin da suka bayyana abin da ke damunsu a rai ba ko yanayin da suke ciki.

Boye yanayin da kake ciki wato ka danne shi kada a gane, na daya daga cikin hanyoyi ko dabaru biyar da mutane suke amfani da su wajen rage yanayinsu. James Gross, farfesa a jami'ar Stanford, ya ce'' yanayin mutum na bayyana ta hanyoyi da dama, kuma ya kan iya zama tare da mutum har zuwa wani lokaci.''

Dabara daya ita ce ka guji duk abin da zai taso maka da wani yanayi; wata dabarar kuma ita ce, ka yi kokarin bullo da wata hanya ta yadda za ka karfafa damarka ta jin wani yanayi mai kyau maimakon yanayi maras kyau.

Akwai kuma wata dabarar ta mayar da hankalinka kan wani abin daban, maimakon ka bari wannan abu ya dame ka. Daga nan da zarar yanayin damuwar ya bar ka, sai ka yi kokarin kallon lamarin ta wata fuskar. Ko kuma ka yi kokarin danne shi kada ya kara taso ma.

An yi amanna idan ka iya kawar da abin da ke damunka ko yanayin damuwar da kake ciki ta wadannan hanyoyi, abu ne mai kyau, wanda yake da alaka da nasara a fannin ilimi da lafiyar tunani ko hankali da kuma tsawon rayuwa.

Amma duk da cewa danne damuwa ka iya zama abu mai amfani lokaci zuwa lokaci, sai dai cizon lebenka, a lokacin da shugabanka na wurin aiki ya yi wani kalami da ya bata maka rai a lokacin da yake ganawa da kai game da yadda aikinka ke gudana.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Danne zuciya na daga dabarar da wasu mutane ke boye yanayin da suke ciki

''A lokacin da ka yi kokarin danne wani yanayi (damuwa), kamar yadda kake kokarin danne wani tunani, to fa zai iya yi maka illa,'' in ji Susanne Scweizer ta jami'ar Cambridge. ''Ta ce wannan yanayi zai iya dawo maka da karfin da ya fi na da a can gaba.''

A bisa wannan nazari, idan yanayi mai kyau ne (farin ciki ko dariya misali) kuma ka yi kokarin boye shi to ba za ka ji dadi sosai ba. Kuma abu ne da ke bukatar kwazo na fili (jiki), domin har bugun jininka (BP) sai ya karu, a lokacin da kake kokarin boye wannan yanayi (farin cki, ko murna da sauransu).

Wasu nazarce-nazarcen ma da aka yi daga bisani sun nuna cewa, kokarin danne yanayin da mutum ke ciki na iya sa ka mantuwa, yayin da su kuma mutanen da kake hira ko magana da su sai ka gundure su.

Ta ya kuma lamarin yake a game da 'yan Burtaniya? Wani bincike da aka yi ya nuna cewa hudu daga cikin 'yan Burtaniya biyar 'yan tsakanin shekara 18 zuwa 34 sun yadda cewa suna daurewa su boye yanayi ko halin da suke ciki idan wani abu ya dame su, kuma kashi daya bisa hudu nasu suna ganin bayyana yanayin da suke ciki alama ce ta rauni.

Wannan zai sa ka dauka rayuwa a irin wannan kasa tashin hankali ne; muna fama da masu larurar hankali, da mutuwa da wuri da kuma tsanar juna.

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Yawancin matasan Burtaniya sun yarda da cewa suna nuna juriya ko da suna cikin wata damuwa

Amma kuma akwai sheda a gabashin Asiya, inda danne yanayin damuwa ya zama abu ne da aka saba da shi, har ma ake daukarsa a matsayin wata dabi'a mai kyau.

Kuma danne damuwa a wane lokaci zai iya zama abu mai kyau. Ka dauki misalin harin bam da aka kai Landan (7/7). Iadn muka ga mutane sun daure ba tare da sun nuna damuwarsu, sun cigaba da gudanar da harkokinsu na rayuwa, to hakan na karfafa mana zuciya.

Zurfin ciki, idan aka yi amfani da shi da kyau, zai iya zama mai matukar tasiri a kan yanayin da mutum ke ciki. Illa dai ba za a ce shi ne abin da ya fi tasiri ba wajen sarrafa yanayin da mutum yake ciki, domin idan ka zurfafa bincike za ka samu wadanda suka fi shi.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Is being reserved such a bad thing?