Mutanen da ke rayuwa da damisa a Indiya

Hakkin mallakar hoto Mark Smith Alamy

A karon farko a cikin shekara ɗari ɗaya, an lura cewa yawan damisa na ƙaruwa, kuma ana ganin wasu al'ummomi da ke zaune a dazuka tare da namun daji ne sanadin hakan.

Ga binciken Niki Rust

A watan Afrilu na 2016, an samu wani labari mai dadi wanda ba kasafai ake jinsa ba a game da damusa. A karon farko a sama da shekara dari, yawan wannan dabbar daji ya karu. Kididdiga ta duniya ta baya-bayan nan ta nuna yawanta ya kai 3,890, idan aka kwatanta da 3,200 a shekarar 2010.

Akwai dalilai da yawa da suka jawo karuwar yawan damisar. Amma wani babban dalili shi ne, a wasu wuraren a yanzu mutane musamman na karkara sun gano hanyoyin yadda za su zauna tare da wannan dabbar dawa da ake yi wa kirari da 'damisa ki sabo'.

Kusan rabin yawan damisar duniyan nan suna Indiya ne, kuma a sassa da dama na kasar, wasau mazauna karkara suna rayuwa da dabbara lafiya lau.

Za a ga wannan kamar wani abin mamaki, domin an san yadda damisa ke kashe mutane wani lokaci, saboda haka za a ga kamar abokiyar gaba ce ga mutum. Amma kuma duk da haka mutane na zamantakewa da ita.

Wani abu kuma shi ne ga kila wadannan al'ummomi suna taimaka wa damisa ne. Kungiyar kare hakkin al'ummomin karkara ta Survival International, ta ce, kabilun karkara su ne suka fi kare dabbobin dawa da muhalli.

Hakkin mallakar hoto Stuart ForsterAlamy
Image caption Wasu 'yan kabilar Soligas a gandun dajin BRT Wildlife Sanctuary

Nau'in damisar da ake magana a kai na rayuwa ne tare da wata kabila da ake kira Soliga a Indiyan. Kuma wani dalili da ya sa ake samu wannan kariya ga damisar shi ne, su wadannan mutanen suna daukar damisa ne a matsayin abar bauta.

A kwanan nan an wallafa sakamakon wani bincike a watan Mayu na 2016, na nazarin da aka yi na rayuwar al'ummar da ke zaune a kusa da gandun dajin Bor Wildlife Sanctuary a Maharashtra.

Masu binciken sun gano cewa kabilun suna zaman lafiya sosai da damisa, kila saboda yawancinsu masu cin ganyayyaki ne, saboda haka ba sa farautar dabbobin dawa domin ci.

Wannan na nufin ita kanta damusa na samun dabbobin da take ci kenan da yawa a yankin.

Wani abu kuma shi ne, saboda yawancin mutanen wurin manoma ne, sun ce suna son kasancewar damisa kusa da su domin tana kare su daga dabbobi masu bannar kayan gona. Haka su ma masu samar da nono da madara, suna ganin damisa na taimak musu wajen gadi daga barayi.

Ba kamar 'yan kabilar Soliga ba, kabilun da ke zaune a kusa da gandun dajin Bor suna yi rikici da damisa, har lamarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dabbobinsu 'yan kalilan. Duk da haka wannan bai sa su gaba da kuma kisan damisa ba.

Wani dalili daya a kan wannan shi ne mutanen 'yan Hindu ne, wadanda kuma su sun yi imani damisa dabba ce ta sufurin daya daga cikin abubuwan bautarsu da ake kira Durga.

Amma kuma duk da irin wannan labari na ci gaba wajen karuwar yawan damisa a sanadiyyar rashin farauta da kisanta, hukumomi na tashin kabilun daga yankunansa na gargajiya da sunan kare muhalli.

Hakkin mallakar hoto Design Pics IncAlamy
Image caption 'Yan kabilar Gujjar a kan hanyarsu ta zuwa aiki

Maganar ko a bar al'ummomin da ke zaune a dazukan da damisoshi suke ko a tashe su abu ne da ake ta mahawara a kansa.

Akwai 'yan kabilar Gujjar da ke sanya wa mushen bauna guba domin damisa ta ci ta mutu, su rika sayar da fatarta da kasusuwanta.

A shekarun 1980 wasau daga cikin al'ummar Gujjar da ke zaune a yankunan da ake da damisa a arewacin Indiya, an tashe su aka mayar da su wani wuri.

A shekara ta 2013 Abishek Harihar na jami'ar Kent a Canterbury da ke Burtaniya, ya tambayi sauran 'yan kabilar ta Gujjar da ba su tashi daga dazukan nasu ba, inda ya gano cewa su kansu suna matukar son tashi, bayan da suka ga rayuwar 'yan uwansu da aka tasa ta inganta.

Mai binciken ya gano cewa yawan damisar ya karu da wuri a wuraren da aka tashi mutanen. Amma kuma yana ganin in har za a bar wasu daga cikin mutanen su zauna a wurin, ganin karuwar dabbar ka iya sa su farautar namun daji, wadda sana'a ce da za ta iya kasanacewa mai riba.

Hakkin mallakar hoto Andy Rousenaturepl.com
Image caption Wasu 'yawon bude idanu na kallon wata damisa

Ba abu ne mai sauki ba ka zauna tare da dabbobin da za su iya kashe ka su cinye ka da dabbobinka ko kuma su cinye dabbobin naka ba.

Amma barin mutanen karkara su kula da dazukansu na iyaye da kakanni ka iya kasancewa babbar hanyar magance matsalar gushewar dabbobin dawa. Kamar yadda Harihar ya ce, ''aiki tare da mutanen dazukan shi ne mafita''.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa na. There are people in India happily living with wild tigers