Ana yunƙurin yi wa duniya lema saboda rana

Hakkin mallakar hoto Getty

A shekaru gommai masu zuwa wannan duniya tamu da ke fama da dumamar yanayi za ta iya haifar da gagarumar matsala ga ci gaban duniya.

To amma yunƙurin kafa wata makekiyar lema in har an iya ƙirƙirota zai iya kare duniyar daga zafin rana?

Ga nazarin Zaria Gorvett

Fafutukar gano hanyar da za a rage yadda duniya ke dumama na daya daga cikin manyan kalubalen da ke fuskantar duniyarmu. Shawararmu ta yadda za a yi kokarin dakatar da wannan dumi za a iya cewa abu ne da kusan ba a taba jinsa ba a duniyar nan, dabarar kuwa ita ce samar da wata katafariyar lema da za a girka a sararin samaniya.

Tuni daman bisa kuskure muna yin kusan wannan tsari na samar da wata babbar inuwa da ke kare mu daga zafi ko hasken rana, saboda haka me zai hana mu yi hakan da niyya ta hanyar fasaha?

Tunani ba na wasa ba, kuma zai iya tabbata. Domin rage yawan hasken ranar da ke zuwa doron duniyarmu zai iya sanyaya duniyar cikin sauri, ko da da yawan iskar numfashinmu da muke fitarwa (carbon dioxide).

Maganar samar da inuwa a sararin samaniya domin rage zafin rana a duniyar nan abu ne da ya samu karbuwa a wurin hukumomi da dama daga hukumomin kula da samaniya na Ingila zuwa na Amurka, da na Turai. Lamarin ya ma jawo hankali tare da nuna sha'awa da hukumar duniya da aka fi martabawa a kan batun dumamar yanayi (IPCC) ta yi a kai.

Tsarin zai iya kasancewa mafi muhimmanci, amma yadda za mu yi shi, shi ne mai wuya. Yadda za a sanyaya duniyar kasancewar tana tafiya kullum, dolew ne sai dai a kafa lemar a wani wuri a waje da zai kasance tsakanin maganadisun da ke jawo abu kasa na duniya da kuma rana wanda ake kira L1 point, wanda ke nisan kusan mil miliyan daya.

Injiniya James Early shi ne ya fara wannan tunani a 1989, wanda ainahin tsarin shi ne samar da wani gilashi makeke mai fadin kilomita 2000, wanda wannan abu ne mai girman gaske da sai dai a kafa shi a kan duniyar wata.

Wasu dabarun da kuma aka yi tunani a baya-bayan nan sun hada da kurar wata da yin wata lema ta wani mudubi na waya mai gida-gida guda 55,000.

Idan kana tunanin sun ci da zuci a wadannan dabaru, to ina kuma maganar matsar da duniyar gaba kadan daga rana, ta hanyar haddasa wata fashewa da ta kai ta bama-baman kare dangi na hydrogen fashewar da ta kai miliyan sau miliyan dubu biyar.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hayaƙin masana'antu da sauran ayyukan mutane na haifar da sauyin yanayi.

Kalubale mafi wahala a kan wannan dabara yanzu shi ne yadda za a samar da wannan inuwa ko rumfa a wajen duniyarmu. A yanzu za a kashe akalla dala dubu goma a kaddamar da abin da zai yi dakon kayan guda daya zuwa sararin samaniya, kuma gas shi rabonmu da kai mutum duniyar wata tun 1972.

Ana ganin dabarar tabbatar da wannan hanya sai dai a hada abin da za a yi amfani da shi a nan duniya. Dan sama jannati Roger Angel yana ganin ya san mafita a kan wannan tunani, inda yake ganin mutum-mutumi mai tashi kamar tsuntsu guda miliyan dubu sau dubu 16 za a samar domin yin wannan aiki.

Kowannensu zai kasance mai nauyin gram daya kamar dai babban kwaron malam-buda-mana-littafi, wanda zai kare hasken rana da wani abu kamar ziri me 'yan kofofi kanana.

Domin saukaka abin zirin zai kasance kasa da kaurin silin gashin mutum da kashi daya bisa dari. Masanin ya ce ba za ka iya kare hasken rana da abin da bai kai wannan kauri ba.

Wadannan mutum-mutumi za su kawanya da kansu ta hanyar amfani da hasken rana, wanda wannan fasaha ce da tuni hukumar kula da sararin samaniya ta Turai ta yi amfani da fasahar a tauraronta mai kewaya duniyar wata, domin yin wani hadari mai fadin mil dubu sittin.

Daga nan kuma sai a samar da wasu taurarin dan adam da za su rika kula da mutum-mutumin domin kare su daga karo da juna kuma kada hasken ranar da suke karewa ya lalata su.

Wannan na nufin kamar makiyayi da dabbobinsa. Angel ya ce, ''idan ka bar su su kadai ba wani da zai rika kulawa da su, sai su kauce hanya su rika karo da juna, har ma su fado doron duniya.''

Wadannan dai na daga cikin tarin dabarun kimiyya da fasaha da kwararru suke ganin za a iya samar da inuwa a ta bai daya a fadin duniya ta hanyar girka katafariyar lema ko wani abu a can sararin samaniya wadanda zai kare hasken ranar.

Sai dai duka wadannan dabaru da makamantansu, ana maganarsu ne kawai ba a tabbatar ko za su yi aiki yadda ake hasashe ba.

Bisa la'akari da rashin tabbas din da ke tattare da duka wadannan dabaru na rage zafin ranar ta hanyar samar da katafariyar inuwa, Dan Lunt na jami'ar Bristol a Burtaniya, da abokan aikinsa sun yi wani gwaji na yanayi domin hasashen tasirin inuwar da za a yi wa hasken ranar.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Duwatsun da ke aman wuta ka iya haifar da yanayi mai sanyi

Masanin yanayi Ben Kravitz wanda ba ya cikin nazarin, ya ce, idan ka rage zafin duniya ya koma kamar na shekarun baya, kafin zuwan masana'antu, to za ka busara da duniya kenan. Masanin ya ce hanya daya da za ka rage hakan, sai ka bar dan zafin da zai rika dumama duniya.

A duniyar da aka gina ko tsara ta da kyau, wasu kasasahen za su fi wasu amfana da wannan inuwa ta duniya, domin rumfar ko lemar za ta kare wasu yankunan daga samun amabaliya, wasu kuwa ta sa musu fari.

Lunt ya ce, ''idan har ana son girka wannan lema ko rumfa a sama sai an samu hadin guiwa na kasashe, ko da yake kasashe daban-daban za su yi ta kawo ra'ayoyinsu. Za a yi ta siyasa a kai.'' in ji Lunt.

To ana ganin cewa samar da wannan inuwa a sararin samaniya zai iya dakatar da dumamar yanayi a duniya? Kokarin fitar da kanmu daga cikin matsalar dumamar yanayi zai iya kai mu ga karin dumamamar yanayin. Kravitz ya yarda da haka.

Ya ce, ''akwai abubuwan da ba za mu taba sani ba, kafin mu fara yin aikin. Har yanzu akwai abubuwa da yawa da ya kamata mu yi kafin mu fahimci abin da wannan fasaha za ta iya yi da wanda ba za ta iya yi ba.''

Watson na ganin magana ce ta auna hadarin da ke tattare da aikin. '' Shekara goma da ta wuce dumin maki takwas da rabi na ma'aunin selshiyas (8.5C), wanda kamar dumamar yanayi ce da za ta kawo karshen duniya, an dauke ta wani abu. Amma yau ba komai ba ce.''

Zai yuwu a ce a yanayi irin wannan mun dauki wani mataki? ''Ina ganin za mu dauka. Ya kamata a ce mun yi duk abin da zamu iya mu tabbatar ba mu kai wannan mataki ba (dumamar yanayi mai yawa)? Wajibi ne.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. How a giant space umbrella could stop global warming