Akwai illa barin mai rauni a ka ya yi barci?

Hakkin mallakar hoto Getty

Yawanci ana gaya mana cewa barin mutumin da ya ji rauni a ka ya yi barci na iya sa shi ya gangare ya suma. Shin haka lamarin yake?

A yanzu fiye da da ana mayar da hankali sosai a kan raunin kai, inda ake muhawara a game da lokacin da ya kamata a bari dan wasan da ya bugu a ka sosai ya dawo fagen wasa ko kuma ya jinkirta dawowa.

Mutane da yawa har yanzu na kamfe domin ganin an dauki maganar jin rauni a ka da matukar muhimmanci. Sai dai wata bahaguwar fahimta da ake yi ita ce wai wanda ya samu mummunar buguwa a ka, ba za a bar shi ya yi barci ba domin kada ya suma. Sai dai wannan ba ita ce shawarar da kwararru a harkar lafiya suke bayarwa ba a yanzu domin ba ta da wata sheda ko madogara.

Ita wannan larura ta ka ana samunta ne ta hanyoyi da dama, kama daga mummunan bugu a ka, ko wani abu ya bugi kwakwalwar mutum kwatsam ba zato ba tsammani kamar a hatsarin mota.

Yana da kyau mutane su dauki rauni a ka abu mai muhimmanci ko hadarin gaske. Abu ne da zai iya kasancewa da illa sosai, kuma wata daga cikin matsalolinsa ita ce gano yawan illar da raunin ya haifar.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ƙwallon zari-ruga na ɗaya daga cikin wasannin da aka fi jin ciwo a ka

A Amurka kadai ana samun mutanen da ke jin rauni a ka mai tsanani kusan miliyan daya da dubu 600 a duk shekara. A yanzu sai dai likitoci sun yi amfani da wasu alamu, da suka hada da amai da rudewa da kasa tsayuwa daidai, da gani garara-garara ko ciwon kai ko dan kaikayi a kafa ko hannu domin su san girman illar raunin.

Akwai kyakkyawan fatan da ake yi cewa akwai wani gwajin jini mai sauki da ake sa ran zai iya zama wata hanya ta sanin illar raunin a can gaba, ta hanyar auna wasu abubuwan a cikin jinin.

A kwanan nan ne wasu kwararru a asibitin Florida na Orlando Regional Medical Centre a Amurka, suka gano cewa idan aka ga kwakwalwa ta saki wasu sinadarai biyu, idan aka bugi kai to lalle ta samu illa.

Zai dauki 'yan shekaru kafin a bullo da hanyar gwaji, amma a yanzu sai dai likitoci su dogara ga wasu alamu da za su iya gani.

Fargabar barin mutumin da ke da raunin na ka ya yi barci don gudun kada ya suma ta samo asali ne daga gurguwar fahimtar da ake yi wa lokacin da mutum ya farfado bayan ya suma, ake ganin kamar ya dawo hayyacinsa, amma kuma can a cikin kwakwalwarsa jini na zuba, wanda kuma hakan na takura wa kwakwalwar.

Idan wannan yanayin ya sake sa mutumin ya suma ko ya fita daga cikin hayyacinsa, to a lamarin na bukatar matakin gaggawa.

Ko da mutum ya ji raunin da kwakwalwarsa ta yi jini, wannan yanayi na farfadowa da mutum yake yi alhalin kuma can a cikin kwakwalwar tasa jini na zuba, ba kasafai abin yake faruwa ba.

Sai dai kuma yuwuwar jini ya zuba a kwakwakwar mutum shi ne dalilin da ya sa yake da kyau a duba wasu alamomi da na fada can a baya, idan kana tare da wanda kansa ya bugu.

Hukumomi da dama ne suka gabatar da wannan shawarar, wadanda suka hada da hukumar kwallon zari-ruga ta duniya da hukumar kula da tsarin inshorar lafiya ta Burtaniya.

Amma idan ya kasance, mutum bai rude ba ko ba ya amai, ko bai nuna matsalar gani garara-garara ba, ko kasa tsayuwa ko tafiya, ko tsananin ciwon kai ko wuya, wadannan shawarwari ba su hada da shawarar barin shi a farke ba. A gaskiya ma abin da ake bukata mutumin ya samu shi ne hutu, na jiki da kuma tunani (kwakwalwa).

Saboda haka dole ne 'yan wasa su dakatar da motsa jikinsu ko atisaye na wani lokaci, kuma su dakatar da dora wa kwakwalwarsu aiki.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana tashin yaron da ke jiyyar rauini a ka daga barci duk bayan 'yan sa'o'i

Idan ko mai raunin yaro ne, to shi kuwa ana so ya rage yawan aikin makaranta, har sai ya warke gaba daya. Kwakwalwar na bukatar ta warke ta hanyar samun hutu, kuma a wannan lokacin barci ne abin da ya fi dacewa da ita. Barcin ba illa ba ne. Abu ne mai kyawun gaske.

Wannan ita ce shawarar da ake amfani da ita a yanzu, ko da yake za a iya cewa, kafin yanzu gwajin da aka yi a kai ba me yawa ba ne, wanda wannan abu ne da ya damu wasu masu binciken.

Abin farin cikin shi ne cewa akwai hanyoyi daban-daban da ake gwajinsu yanzu, saboda haka nan ba da dadewa ba za a san hanyar da ta fi dacewa ta maganin raunin ka da kuma yadda za a kula da mai raunin.

Wasu hukumomi sun bayar da shawarar cewa idan yaro ya ji rauni a kansa, to ya kamata a rika tashinsa daga barci duk bayan sa'a daya ko biyu a daren farko da jin raunin, domin a duba a tabbatar ba wata matsala, kuma zai iya hira kafin a bar shi ya koma barci.

Saboda haka barci abu ne mai kyau da ake ba da shawara a sa wanda ya ji rauni a ka ya yi, amma hakan ba yana nufin abu ne mai sauki ba a ko da yaushe a samu yinsa.

Bincike ya nuna akwai matsaloli na barci iri-iri wadanda mutumin da ya yi rauni a ka zai iya fuskanta, misali kasa barcin shi kansa, da gajiya, da kamuwa da barci kwatsam kuma a lokacin da watakila bai dace ba da kuma minshari.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Should you let someone with concussion fall asleep?