Ka san amfanin hawa keke kuwa?

Hakkin mallakar hoto Getty

Galibin zirga-zirgar da ake yi a birane a na yinta ne a motoci, duk da tarin alfanun da ke tattare da hawa keke. Ta yaya za a sa al'ummomin birane su rika amfani da keke?

Katia Moskvitch ta yi mana nazari

Tunanin kirkirar shi kansa ainahin wani abu da a yau ya juye ya zama abin da aka sani da keke ya fara ne tun lokacin da aka samu annobar mutuwar dawakai lokacin 1816, shekarar da ake cewa ba ta yi bazara ba.

A wannan shekara an sha tsananin zafi a kasashen duniya saboda bala'in aman wuta da aka samu a duwatsun tsaunin Mount Tambora na Indonesia a shekarar 1815.

Wannan wutar duwatsu na daya daga cikin irinta mafi tsanani da aka taba gani a tarihin duniya, inda ta haifar da kurar toka da kuma sinadarin farar wuta (sulphur), abin da ya sa gonaki suka yi fari a fadin Turai.

Wannan yanayi ya sa dawakai sun gamu da yunwa domin ba a samu abinci ba, wanda a sanadiyyar hakan suka yi ta mutuwa, shi kuwa wani dan kasar Jamus Karl von Drais, ya kirkiro abin da zai maye gurbin dawakai, abin da ya kai shi ga samar da abu mai kama da keke na zamanin yau amma kuma ba shi da abin tuki (feda).

A wancan zamanin ana kiran wannan abu (keke) da sunan 'draisine' ko 'velocipede' a Faransanci. Daga baya ne aka kirkiro masa da feda, kuma nan da nan sai wannan abun hawa (keke a yau) ya zama abin hawa na yawancin jama'a.

A yau keke shi ne fitaccen abin hawar da mutum ke tuka shi da kansa fiye da kowane abu, ba wanda wata na'ura ko in ji ke motsawa.

Hakkin mallakar hoto Getty

Duk da yadda keke yake ba ya fitar da wani hayaki ko wani abu da zai gurbata muhalli,a kasashe kadan ne yawancin jama'a ke amfani da shi.

Gudun hadari da rashin hanyoyi na musamma da ake ware wa masu keke da matsalar ruwan sama da sanyi su ke hana mutane da dama amfani da keke.

A Burtaniya da Amurka da Ausrtaliya kashi daya bisa dari ne kawai na tafiye-tafiye ake yi a kan keke. Amma kuma akwai kasashen da suka fita zakka, inda a Holland zirga-zirga a keke ta kai kashi 27 cikin dari, kuma a babban birnin Denmark Copenhagen sama da rabin al'ummar kasar suna hawan keke.

Karancin masu hawa keke ba yana nufin karancin hadari ba kenan, sai ma dai yawansa. Kamar yadda kididdiga ta nuna, yawan mutuwar da aka samu a tafiyar kilomita miliyan 100 da aka yi a keke a Amurka ta kai biyar da digo takwas, a Burtaniya kuwa uku da digo shida ce.

Sabanin haka a kasar da ake da sha'awar hawa keke kamar Jamus tana da yawan mutuwar 1.7, kuma a Denmark ana da 1.5.

Kuma an fi rashin hadari a keke a Holland inda suke da mace-mace kashi 1.1 a zirga-zirga ta kilomita miliyan 100 a keke.

Bincike ya nuna cewa yawan karfafa wa jama'a guiwa a amfani da keke kuma mutane suka lamunta da shi hakan na kara rage hadarinsa.

Fargabar hawa titi

To amma za a iya karbar wannan al'ada ta amfani da keke a ko'ina kamar yadda aka rungume ta a Holland?

Kuma wana irin sauyi za a yi a titunan birananmu ta yadda za a shawo kan mutane su yi watsi da motocinsu da ke bulbular da hayaki su koma amfani da keke, musamman ma a lokacin sanyi da damuna? Kuma fasaha za ta iya sa mu zamanantar da yadda ake hawa keke?

Babban abin da ke sa ba a hawa keke sosai a birane da dama na duniya shi ne yawancin mutane ba sa jin dadin yadda za su hau keke kuma su hada hanya da motoci da ke dan-karen gudu da kuma manyan motoci a titunan, in ji Mark Vallianatos na kwalejin Occidental da ke Los Angeles a Californita ta Amurka.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Daliban jami'ar Taiwan National University a kan kekuna a Taipei

Yawancin biranen zamani an tsara su ne domin kanan motoci in ji Ralph Buehler na jami'ar Virginia Tech a Askandriya ta Masar.

A ko'ina idan ka duba a birane, walau a hanyoyin shiga gidajenmu ne ko a wurin tsayawa da motoci ne a gefen tituna za ka ga an tsara su ne domin motoci ba tare da an damu da kekuna ba.

A yawancin birane za ka ga babu wasu tituna na keke na musamman da aka ware, ballantana ma a yi maganar hanyoyi na musamman irin na zamani da aka yi domin kekuna kamar yadda za ka iya gani idan ka ziyarci birnin Groningen a kasar Holland (netherlands).

Hakkin mallakar hoto Getty

Za ka daruruwan hanyoyin kekuna suka rarratsa juna a birnin, yayin da masu kekuna sai sun rika kaucewa domin gudun taba motocin da aka ajiye a gefen titi, wasu motocin kuma na wuce su ta gefe da gudu.

A biranen ma da ake da titunan keke za ka ga ba su da fadi yawanci.

''Za ka ga mutanen da ke tafiya a mota, ko a safa ko jirgin kasa na jama'a ko a gefen hanya suna tuki kusa da kusa suna hira, amma titin kekuna na birnin Landan wanda ba shi da fadi ya sa wanda ke kan keke ba shi da abokin hira.'' In ji Anne Lusk mai bincike kan tsara birane a jami'ar Harvard da ke Boston a massachusetts ta Amurka.

Iyakar bishiyoyi

Yawanci rabin tafiyar da masu motoci ke yi a biranen Turai ba su kai ta nisan kilomita biyar ba. ''Duk wani mai tsara birane da ke da basira babban abin da zai mayar da hankali a kansa shi ne masu keke da tafiya a kafa da kuma motocin bus da jiragen kasa na cikin gari na jama'a,

idan yana tunanin yadda zai bullo wa matsalar amfani da abubuwan sufuri masu gurbata muhalli kamar kananan motoci na jama'a,'' in ji Ceri Woolsgroove kwararre kan kiyaye hadura a hukumar tseren keke ta Turai.

A bisa wannan tsari za a kirkiri hanyoyin kekuna da sauran wurare nasu daban in ji Vallianatos. A shekarar 1998 birnin Bogota na Colombia ya gina titina na tsawon kilomita sama da 300 wanda gefensu duk bishiyoyi sun yi iyaka da titunan motoci.

Enrique Penalosa magajin garin Bogota a lokacin da aka yi titunan a wata hira da aka yi da shi kwanan nan ya ce wanna aiki ba wata kirkira ba ce ta wani kwararren mai tsara hanyoyi, illa dai su sun dauki duk dan kasar da yake kan keken dala 30 daidai da mai motar dala dubu 30.

Hakkin mallakar hoto AirbeteWikipediaCC BYSA 3.0
Image caption Wani katafaren wurin ajiye kekuna a birnin Amsterdam na Holland

Samar da yanayi na amfani da keke ba ya tsaya ga gina tituna ko hanyoyin keke ba ne kadai. Tsare-tsaren hayar kekuna a kasashen duniya sun yi nasarar jawo mutane da 'yan yawon bude idanu da dama wajen amfani da keke.

A birnin Hangzhou na China, inda ake da tsarin hayar keke mafi girma a duniya, sa'ar farko a kyauta take idan ka dauki hayar kekensu.

Domin yaki da matsalar dumamar yanayi da gurbati muhalli, hukumomin birnin sun hana amfani da wasu motoci masu wasu lambobi a wasu ranaku.

Sai dai irin wannan tsari ya gamu da kalubale a birane irinsu Milan da kuma Mexico City a kwanan nan, mai makon mutane su koma amfani da kekuna ko motocin haya kamar su safa sai suka rika musayar motoci ko kuma su kara wata motar da wata lambar.

Wata matsalar kuma ita ce ta wurin ajiyar kekuna musamman a tashoshin jiragen kasa da na motocin safa. Misali a Amsterdam an gina wurin ajiye kekuna mai hawa-hawa da zai dauki kekuna 6,000.

A kwanan nan kuma babbar tashar Ultrech ita ma a Holland din za ta kasance da wurin ajiye kekuan mafi girma a duniya, inda za a iya ajiye kekuna 12,500.

Wani tsarin kuma shi ne na yin motocin safa na jama'a masu wurin adana kekuna, abin da zai iya ba masu keke damar tafiyar dogon zango, in ji Lusk. A wurare kamar Lake District da ke Burtaniya wasu motocin tuni an yi musu wurin ajiye kekuna.

Taimako a hawa tudu

Kamata yayi a tituna a samar wa da masu kekuna da kuma masu tafiya a kafa tsarin da fitilar bayar da hannu za ta rika ba su damar wucewa kafin masu motoci.Kuma a yi yadda idan har masu kekuna za su tsaya akwai wani abu da za su dora kafarsu su huta.

Haka kuma a birnin Trondheim na Norway, an yi wata hanya ta taimaka wa masu keke a tudu mai hawa sosai, inda a farkon titun masu keke na Trampe aka sa wata na'ura wadda idan mutumin da ke kan keke ya zo wurin zai danna ta ta rika tura shi ba sai ya yi tuki ba.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Akwai na'urar da ke taimaka wa masu keke wajen hawa tudu a birnin Trondheim na Norway

Domin bayar samar da isassun wuraren ajiye kekuna, ana dauke motoci a kai su wasu wuraren na musamman a cikin unguwanni.

Hular kwano mai iska

Yayin da kokarin samar da hanyoyi da sauran wurare na masu kekuna ya kasance abu mai sauki, masu fasahar kirkire-kirkire na fatan yin abubuwan da za su rage hadarin da ke tattare da hawa keke da kuma kayutata dadin amfani da shi.

Daman tuni akwai na'urorin zamani irin na komai-da-ruwanka da ke taimaka wa masu keke, inda wasu ke nuna wa mai keke hanya mafi sauki da sauri wadda ta fi dacewa da keke zuwa inda za su.

Wasu kuma na nuna maka inda ramuka suke a hanya, da kuma na hana sace keken. Bayan fasahohi irin wadannan, yanzu an yi ta hular kwano da masu hawa keken za su wadda ke da hular kwano wadda za ta fitar da wata jaka mai iska da za ta kare kanka idan bukatar hakan ta taso, misali a sanadin faduwa domin kada kanka ya yi rauni.

Motoci da dama a yanzu suna da na'urori da suke ankarar da direba idan akwai me keke ko mutumin da ke tafiya a kasa a kusa da su domin kare hadari.

Hakkin mallakar hoto Hovding
Image caption Hular kwano me iska ta hawa keke

Haka kuma ana cigaba da kirkiro kekuna masu fasahohi daban-daban. Kamfanin fasaha na Baidu wanda ya yi fice a China ya hada hannu da jami'ar Tsinghua da ke Beijing domin kirkiro wani keke me dauke da fasahohi iri-iri mai suna Dubike.

Keken yana dauke da na'urori da za su rika tattara bayanai na tafiya ko gudunka har ma da bugun zuciyarka. Zai rika nuna maka hanyar da ya kamat ka bi.

Kuma a tafiyar da yake yi yake chajin na'urorin da ke jikinsa, sannan zai rika mika bayanan da yake tattarawa zuwa wayar salularka wadda ita kuma za ta mika bayanan a shafukanka na sada zumunta da muhawara na intanet.

Keke mai magana

Masu bincike a kasashen tarayyara Turai suna wani aiki na kokarin ganin yadda kekuna za su rika sadarwa tsakaninsu da motoci da sauran na'urorin kare hadari da inganta tafiya a tituna, kamar fitilar ba ababan hawa hannu. Akwai gwajin da ake yi a birnin Helmond na Holland, a ga yadda keke da mota za su iya magana da junansu idan sun kusa karo domin kauce wa hadari.

Hakkin mallakar hoto NorthboerWikipediaCC BYSA 3.0

Shin duk wadannan cigaba da keke ke samu za su iya sa ka, ka yi watsi da dadin cikin motarka ka kama hawa keke, musamman ma idan ana cikin huturu ko ruwan sama?

Woolsgrove ya ce shi yana ganin magana ce kawai ta dabi'a, ''da zarar dabi'ar hawa keke ta kama ka shikenan, za ka ga ba karamin sauyin yanayi ba ne zai sa ka yi watsi da keken.''

Benedicte Swennen ta hukumar kula da sufurin keke a Turai ta ce, ''masu gudu (motsa jiki) da hawa keke ne kawai suke lura cewa a ko da yaushe ne ake ruwa ba".

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. How to get a city cycling