Ka san yadda ake zama mace ko namiji?

Hakkin mallakar hoto Fijoy joseph
Image caption Ɗan-daudu

Kai namiji ne ko mace? Zai kasance kana jin kai namiji ne ko mace; ƙila yanayin da kake ji tun kana ɗan ƙanƙani kenan wanda kuma ya zo daidai da jinsin gabanka. Amma kuma ba lalle ba ne.

Wasu mutanen suna jin kamar ba a haife su da jinsin da suke so ba; wasu ba sa jin wannan yanayin har sai sun girma. Wasu ma a kan yi musu tiyata a sauya musu jiki ta yadda zai dace da yadda suke ji; Wasu sukan sauya kayansu lokaci zuwa lokaci misali su sa na mata, ko ma su hakura ba tare da sun yi komai ba.

Akwai kuma mutanen da ba sa jin komai, su maza ne ko mata ne, suna tsaka-tsaki. Sukan ce duniya ta kunshi komai, kuma haka lamarin yake a kan jinsi ma.

Amma daga ina wannan yanayi da mutum kan ji shi namiji ne ko mace yake zuwa? Kuma wane tasiri yake yi wajen sa mutum ya zama abin da yake zama a karshe?

Shekaru da dama ana ta muhawara a kan inda asalin dabi'ar namiji da mace ta samo asali. A shekarun 1970, masu fafutukar kare hakkin mata wadanda suke neman tabbatar da daidaito sun rika sanya wa maza kayan mata kuma suka rika karfafa wa mata guiwa kan su rika wasa da mota irin ta yara.

Sannan kuma a shekarun 1990 sai hankali ya karkata wajen gano bambancin da ke tsakanin kwakwalwar maza da ta mata, hakan kuwa ya samo asali ne a dalilin littafin nan da ya yi fice a duniya mai suna 'men Are from Mars, Women Are from Venus.

Hakkin mallakar hoto Emma Leslie
Image caption Ɗan-daudu

Har zuwa yau wannan muhawara na ci gaba da wanzuwa, misali a kan tattaunawar da ake yi kan ko kantunan sayar da kaya za su rika rarrabewa tsakanin kayan wasan yara maza da na mata daban, na mata ana cewa a rika yi musu launin ruwan hoda su kuma na maza a rika yinsu launin shudi.

Sai dai bincike-binciken kimiyya da ake ci gaba da yi a kan yadda wasu mutane kan ji yanayinsu daban da yadda suke so na jinsinsu, idan namiji ne ya rika jin shi kamar mace ne ita mace kuma ta rika ji namiji ce yana bayar da karin haske a kai.

Mutane sukan yi magana a kan bambancin kwakwalwar maza da ta mata, gaskiya ne akwai bambanci tsakaninsu amma kuma ba wanda ya taka kara ya karya ba ne.Yawanci yawan kwakwalwar maza ya fi na kwakwalwar mata, akwai kuma bambancin girma na sassan kwakwalwar.

Sai dai Lise Eliot, farfesa a jami'ar Rosalind Franklin da ke Chicago kuma marubuciyar littafin 'Pink Brain, Blue Brain,' ta ce, ''ba za ka iya kaloon kwakwalwar wani ka ce wannan ta mace ce ko ta namiji ba, akwai bambance-bambance na kididdiga amma kuma ba wadanda za su nuna cewa wannan shi ne irin mutum kaza ko kaza ba. Ana samun kamanni sosai da sosai.''

Kwakwalwar manya masu jin sauyin jinsinsu kusan ba ta zama kusan a rukuni daya da ta maza ko mata. ''Ba magana ce ta girma ba, magana ce ta yanayi ko kuma yadda aka gina kwakwalwar,'' in ji Antonio Guillamon na jami'ar Uned a Madrid, wanda yana daga cikin masu nazari a kan lamarin.

Hakkin mallakar hoto Emma Leslie
Image caption Briella da ƙanwarta Emma Leslie yaran da suke jin kamar su maza ne

A matan da suke daukar kansu a matsayin maza wasu bangarorin kwakwalwar tasu na kamanni da na maza yayin da ta maza masu jin kansu kamar mata ('yan daudu) yanayin halittar wadannan bangarorin rabi ya yi kama da ta maza rabi kuma kama da ta mata.

Ya ce,''kwakwalwar mazan da ke jin kansu kamar mata ba ta yi kama da ta maza ba gaba dayanta, haka kuma kawakawlwar matan da ke jin kansu kamar maza ita ma ba ta yi kama da ta mata ba gaba daya.'' Sai dai masanin ya kara da cewa ya yi wuri yanzu a ce ko wadannan su ne bambance-bambancen da ke bayyana abin da ya sa mutane ke jin su maza ne ko mata.

Amma kuma duk da haka wasu sun gano sabanin hakan a yanyin kwakwalwar maza da mata masu jin yanayin jinsinsu daban da yadda suke. Daya daga cikinsu shi ne bambanci a dan wani wuri da yake tafiyar da dabi'ar jima'i ta beraye.

A kan hakan ne wasu ke ganin wannan a matsayin shedar da ke nuna wannan yanayi da mutum kan ji cewa shi wani jinsin ne; mace ta ji ita namiji ce ko namiji ya ji shi mace ne kusan yana da asali a halitta, ba zabi ba ne, amma kuma ba kowa ba ne ya yarda da hakan.

Eliot ta ce, ''lalle kam za a iya samun 'yan bambance-bambance a mutanen da ke irin wannan yanayi na jin sauyin jinsi, to amma daman abu ne da za ka yi tsammani saboda rayuwarsu daman daban take.''

''Tsawon wana lokaci mutum yake jin shi mace ne ko mace take jin namiji ce; lokacin da suke yara da wa suke wasa; wadanna irin ayyuka suke yi, duka wadannan za su iya shafar wadannan wurare na kwakwalwa ta wasu hanyoyi.

Hakkin mallakar hoto Emma Leslie
Image caption Georgie ɗan shekara 15 yana alfahari da kuma jin cewa shi mace ne

Ba shakka babu alamar da ke tabbatar da magana ko nazariyyar Lady Gaga ta cewa ('I was 'Born This Way'), ''Haka aka haife ni''. Amma wannan ba shi ne zai hana mutum tunanin cewa kwakwalwar da ke kansa ba wadda ta dace da shi ba ce, in ji masaniyar. Amma ga alama idan ana neman inda za a gano inda wannan tasiri yake a jikin dan adam kila sai dai a nemi wani wurin amma ba kwakwalwa ba.

To ya lamarin yake a kan jarirai?

Tsawon lokaci ana daukar jarirai cewa ba su da jinsi na namiji ko mace, ''a shekarun 1970 ana ganin muhallin da suke ne ke sa su zama suna jin cewa su mace ko namiji ne,'' in ji Dick Swaab, farfesa a jami'ar Amsterdam.

To amma mutane irin su David Reimer wanda ya rasa azzakarinsa a yayin wata tiyatar asibiti da ba ta yi nasara ba, lokacin yana dan wata takwas, wanda a dalilin hakan likitoci suka ce zai fi dacewa ya tashi a matsayin mace, sun kalubalanci wannan tunani.

Bayan da Reimer ya kai watanni 17 ne likitocin suka cire masa marena, sannan lokacin da ya kai shekarun balaga sai ana sanya masa kwayoyin halitta na mace, aka kuma sa masa sauya masa suna zuwa Brenda, ana kuma sanya masa kayan mata.

Sai dai kuma a tsawon wannan lokaci Brenda a ko da yaushe yana ko kuma tana rika jin ita namiji ce, ya koma yadda aka haife shi kenan a kokacin da ya girma.

Wannan ya kara tabbatar da maganar cewa yanayin yadda mutum ke daukar jinsinsa na samunsa ne tun yana dan karami. Swaab da sauran masana na ganin tun ma kafin a haifi jariri ake yi masa jinsinsa a yayin halitta.

Sai dai abin takaicin shi ne ba za mu iya tambayar jarirai yadda suke ji ko jinsin mace ko namiji ba, kuma abu ne mai wuy a iya daukar hoton yanayin aikin kwakwalwarsu saboda suna motsi da yawa.

Babban abin da za a yi shi ne a duba kayan wasan da suka fi son su yi wasa da su, ''domin yanayin wasa na nuna bambancin jinsi sosai,'' in ji Melissa Hines, ta jami'ar Cambridge.

Hakkin mallakar hoto Emma Leslie
Image caption Taleem ɗan shekara tara da ƙanwarsa Nim

Mu mutane muna da yanayi na daukar abu a matsayin baki ko fari, amma yanayin halittarmu na fili yana saba yadda kwakwalwarmu take. Jinsi zai iya kasancewa gamayya ta abubuwa da dama da aka rubuta ta fannoni masu yawa. Ba mata ko maza muke ba kawai, mun hada duk wata siga da yanayi da ke sa mutum ya kasance mace ko namiji.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The complex circumstances that defined your gender