Me ya sa muke buƙatar barci?

Wannan tambaya har yanzu tana ci wa masana kimiyya tuwo a ƙwarya, inda take ba su mamaki, to amma yanzu akwai bayanai masu yawa kuma masu ɗaure kai waɗanda ke bayyana dalilin bukatarmu ta yau da kullum kan barci.

Ga nazarin Tom Stafford

Wasu mutanen suna bukatar barcin sa'a takwas yayin da wasu za su iya rayuwa da na awa hudu. Amma dai abu mafi muhimmanci shi ne kowa na bukatar barci, kamar yadda yake bukatar numfashi da kuma abinci. Amma kuma duk da nazarce-nazarce na tsawon gomman shekaru har yanzu masana kimiyya ba su san dalilin da ya sa muke yin barci ba.

Amma kuma akwai wasu alamu da bayanai da za su iya bayar da haske a kan wannan matsala. Wata alama ita ce, dukkanmu mun fi jin dadin kanmu bayan mun yi kyakkyawan barci da daddare, kuma mun fi jin rashin dadi idan ba mu yi barci ba da almurun.

Mutane kan ji bukatar yin barci sosai bayan sun yi kwanaki ba tare da sun samu damar yinsa ba, inda ma har ake samun rahotannin da ke nuna cewa mutanen da suka ci bashin barci sosai har ya kan sa su fadi idan suna tsaye, kuma ko da ana bugunsu ko kunna musu wani kida mai karar gaske, barcin yana daukarsu.

Mutanen da suka yi kwanaki ba su yi barci ba su kan ce suna jin suna rudewa da mantuwa da dimuwa. A tarihi tsawon kwanaki 11 ne mafi tsawon lokacin da wani mutum ya kai ba tare da barci ba.

Amma maganar cewa muna yin barci ne saboda mun gaji kamar ka ce muna cin abinci ne domin muna jin yunwa- lalle gajiya na sa mu barci amma hakan ba yana nufin lalle gajiya ce ke sa mu bukaci barci ba.

Taimaka wa kwakwalwa.

Wani bayani da ya bayyana a shekarun nan shi ne cewa barci na taimaka mana haddace sabbin bayanai. Kwakwalwarmu wata aba ce mai mamaki ta , kuma bincike da dama na nuna cewa ga alama barci na taimakawa wajen gyara kwakwalwa.

Misali Matthew Walker da abokan aikinsa daga jami'ar California sun ba wa wasu mutane jarrabawa kamar tuna yadda wani tsari yake na wani zane da aka dan nuno musu ta kwamfuta.

Rabin yawan mutanen an nuna musu abin ne da safe, sauran rabin kuwa da yamma. Domin jarraba karfin kwakwalwarsu sai ya shiga da su dakin gwajin kimiyya, inda wadanda aka nuna wa abin da safe suka dawo bayan ba su yi barci ba duk tsawon rana, su kuwa adanda aka nuna wa zanen da yammam suka dawo bayan sun yi barci da dare.

Kamar yadda aka yi tsammani wadanda suka runtsa da daddare sun fi tuna yadda zanen yake­. Bayan wannan ma akwai kyakkyawan labari ga masu kailula (barcin rana).

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wani fasinja na barci a filin jirgin saman Japan

Irin wannan binciken ya nuna kwakwalwarka za ta fi aiki idan ka yi barcin rana. Saboda haka idan ka dade kana aiki ko karatu da rana, kana ka ki runtsawa idan har ka ji kana bukatar yin hakan ko da na dan lokaci ne.

Hutu (barci) zai iya taimakawa wajen kawar wa da mutum wani mummunan tunani ko wani abu maras kyau da ya faru.

Mafarki

Daga wannan nazarin mun samu muhimmin ilimi a kan abin da ya shafi barci. Abubuwan da zuciyarmu ke yi na ban mamaki a lokacin barci (mafarki), suna iya kasancewa a dalilin sake shiri da kwakwalwarmu ke yi domin ta dawo kamar sabuwa, da kuma abin da zuciyar tamu ke yi na kokarin gano dangantaka tsakanin dukkanin abubuwan da suka faru da mu a baya-bayan nan.

Wannan kila shi ne zai bayyana mana dalilin da ya sa mutum ke dimuwa ko rikicewa idan bai samu damar yin barci ba na tsawon lokaci, inda yake kasa bambance abin da ke zuciyarsa da kuma na zahiri.

Yawancin irin wannan shi ne ke haifar da hasashe na ilimi. Zai iya kasancewa bayan daidaita aikin kwakwalwar, jikinmu na amfani da lokacin da muke barci ya gyara kansa misali kwayoyin halitta da suka lalace ko suka jikkata.

Amma wasu masana kimiyya suna ganin ba lalle ba ne dalilin barci ya ksanace gyara jiki. Hasali ma sun ce maganar cewa ''me ma ya sa muke barci?'' ita kanta gurguwar fahimta ce, abin da ya kamata a tambaya shi ne ''me ya sa muke kasancewa a farke?''.

Su masanan suna ma ganin cewa idan kana cikin koshin lafiya, bata jikinka ne ma ka kasance a farke kana ta yawace-yawace (har ma ka jefa kanka cikin wata matsala).

Masanan sun kara jan wannan magana da cewa za ka kasance ne a farke idan har ya zamar maka dole, sannan kuma za ka yi barci ne idan kana jin ya dace ka yi shi.

Hakkin mallakar hoto Getty

Wani abu daya da yake tabbas shi ne, ba wai dole ne mu yi barci ba, abu ne da ke da muhimmanci da kyau ga jikinmu da kuma zuciya.

Kodayake kowane mutum na da yawan barcin da jikinsa ke bukata, yawanci ana bukatar na tsawon sa'a bakwai ne, kuma wadanda suke kasa da haka sosai suna cikin hadarin kamuwa da cutuka iri daban-daban, kamar cutar zuciya da takaitacciyar rayuwa.

Saboda haka nan gaba maimakon ka yi dari-darin barci idan har kana bukatarsa, ka yi tunanin amfanin da jikinka zai samu.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Why do we need to sleep?