Kashi nawa na ƙwaƙwalwarmu muke amfani da shi?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Muna matukar ƙaunar jin bayanin cewa idan da za mu yi amfani da sauran sassan ƙwaƙwalwarmu da ba ma amfani da su, da za mu kasance masu basira fiye da yadda muke.

Sai dai abin takaici Claudia Hammond tana da wani bayani maras daɗin ji kan wannan magana

Abin sha'awa ne ka ga irin tarin maganganu irin na kunne ya girmi kaka a kan jikin mutum da za ka iya zaba, amma wani bangare da ya fi samun irin wadannan maganganu fiye da kima shi ne na kwakwalwa. Daya daga cikin labaran kanzan kuregen da na fi so a kan kwakwalwar shi ne na cewa kashi goma cikin dari kawai na kwakwalwarmu muke amfani da shi.

Wannan labari ne mai dadin ji, domin yana nuna cewa idan da za mu iya gano yadda za mu yi amfani da sauran kashi 90 din da ke zaman kawai to da mun zama masu basira da cigaba fiye da yadda muke a yanzu.

Wannan zai iya sa mu kara zage damtse, mu tashi tsaye, sai dai wannan ba yana nufin akwai kanshin gaskiya a kan maganar ba.

Da farko abu mafi muhimmanci da ya kamata a tambaya kashi goma cikin dari ko nawa? Idan kashi goma cikin dari ne na kwakwalwar to a kan wadanne nau'in mutane ake magana, wannan shi ne abu mai sauki da za a karyata.

Akwai hanyar da za a iya gwada aikin kwakwalwar mutum da na'ura a ga wane bangare ne da wane bangare suke aiki a lokacin da mutum yake tunani ko yin wani abu.

Aiki mai sauki kamar dunkule hannunka da ware shi ko furta 'yan kalmomi abu ne da ke bukatar aikin sama da kashi goma cikin dari na kwakwalwa.

Ko da kana jin ba ka yin wani aiki da jikinka, kwakwalwarka tana yin abubuwa da dama, kamar tafiyar da wasu ayyukan jikin naka kamar numfashi da bugun zuciyarka, ko tuna abubuwan da ka shirya yi a gabanka.

To amma kila kashi goma cikin darin ana maganar kwayoyin halittar da ke cikin kwakwalwar ne. To wannan ma ba mai yuwuwa ba ne, domin duk kwayar halittar da za ta tsaya da aiki ko dai ta mutu ko kuma wani fannin da ke kusa ya mallake ta.

A takaice ba ma barin kwayoyin halittar kwakwalwarmu su zauna haka ba sa aikin komai. Kima da darajarsu ta fi haka matuka. A gaskiya ma kwakwalwarmu na cin albarkatun jikinmu sosai, domin tabbatar da rayuwar kwayar halitta daya ta kwakwalwa na bukatar kashi 20 cikin dari na iskar da muke shaka kamar yadda masanin kimiyyar kwakwalwa Sergio Della Sala ya bayyana.

Gaskiya ne cewa wani lokaci halitta ka iya kasancewa da wani tsari ko siffa mai ban mamaki, amma a ce muna da kwakwalwa da ta linka wadda muke da ita sau goma abu ne da zai zama wani bambarakwai, idan girmanta ya zama matsala ga rayuwarmu, ya kan haifar da matsalar haihuwa da mutuwar uwa a lokacin haihuwa idan ba a samu agaji ba.

Duk da wannan mutane da dama sun kafe tare da yarda da maganar amfani da kashi goma cikin darin na kwakwalwarmu. Maganar ta yadu da kuma karbuwa sosai har ma ta kai lokacin da masaniya kan aikin kwakwalwa ta Jami'ar Landan Sophie Scott tana halartar karatun koyon aikin ba da ahgajin gaggawa, malamin da ke koyar da su ya ce rauni a ka ba shi da wani tsanani ko hadari saboda wannan magana ta kashi goma cikin dari.

Malamin ya yi kuskure ba a kan maganar cewa kashi goma cikin dari na kwakwalwarmu ne kadai muke aiki da shi ba, har ma maganar cewa raunin kwakwalwa ba shi da wani hadari. Domin hatta dan karamin rauni a kwakwalwa zai iya haddasa babbar matsala ga lafiyar mutum.

Malamin koyar da agajin farkon ga alama ba wai yana neman kalubalantar farfesar ta kimiyyar kwakwalwar ba ne, amma dai, Scott ta gyara masa wannan gurguwar fahimta.

Abin sanya tunani

To ta yaya abin da ba shi da wata kwakkwarar madogara a kimiyya ya samu yaduwa da karbuwa haka a duniya? Abu ne mai wuya a iya gano inda wannan fahimta ta samo asali.

Kwararren masanin kimiyyar tunanin dan adam kuma masanin falsafa dan Amurka William James ya bayyana a littafin 'The Energies of Men' a 1908 cewa, "muna amfani da dan wani karamin bangare ne kawai na kwakwalwarmu".

Yana da kwarin guiwar cewa mutane za su iya samun karin cigaba fiye da yadda muka samu a yanzu, to amma ba ya yi nuni da yawan bangaren kwakwalwarmu ba ne ko kwayoyin halittar kwakwalwar tamu ba ne da muke amfani da shi ba, bai kuma ce wani kashi na kwakwalwar tamu muke amfani da shi ba.

Maganar kashi 10 cikin darin da ake yi an ambace ta ne a sharar fagen littafin Dale Carnegie mai suna 'How to Win Friends and Influence People' na shekarar 1936, wani lokacin kuma mutane na cewa maganar ta faro ne daga fasihi Albert Einstein.

Amma kuma farfesa Della Sala ya yi kokarin gano inda fasihin ya taba yin wannan magana, kuma hatta wadanda suke aiki a wuraren ajiyar littattafan tarihi na Albert Einstein din ba su iya gano inda wannan magana take ba. Saboda haka ga alama maganar almara ce kawai.

Akwai kuma wasu mganganu guda biyu da ake ganin kila su suka haddasa wannan gurguwar fahimta. Kashi 90 cikin dari na kwayoyin halittar da ke kwakwalwa, wadanda suke sama wa kashi goma cikin dari na sauran kwayoyin halittar na kwakwalwa karfi da kuma abin da duk suke bukata domin su rayu.

To amma wadannan kwayoyin halitta ne na daban kacokan. Ba ta yadda za a yi su sauya kansu su zama masu aiwatar da ayyukan kwakwalwarmu, suna ba mu karin karfin kwakwalwa.

Akwai wani rukunin masu wata larura ta daban, wadanda hoton kwakwalwarsu ya nuna wani abu da ba a gani a kwakwalwar mutane. A shekarar 1980, wani likitan yara dan Burtaniya mai suna John Lorber ya fada a mujallar kimiyya ta 'science' cewa ya samu wasu marassa lafiya da ba su da wata jijiya a kwakwalwa, amma kuma duk da haka kwakwalwar tasu na aiki.

Ba shakka gaskiya ne idan muka dage za mu iya koyar wasu sabbin abubuwa, kuma akwai shedar kimiyya da ke nuna wannan na sauya kwakwalwarmu. Amma hakan ba yana nufin muna amfani da wani sabon bangare ne na kwakwalwarmu ba.

Muna kirkirar wasu sabbin hanyoyi ne tsakanin kwayoyin halittar da ke kwakwalwar ko kuma mu rabu da tsoffin hanyoyin da ba ma bukata.

Abin da ke ba ni mamaki sosai shi ne yadda mutane suke mamaki idan ka karyata maganar cewa kashi goma cikin dari na kwakwalwarmu ne muke aiki da shi kawai.

Watakila kashi 10 cikin darin ne ke daukar hankali saboda ya yi kadan sosai, ana ganin ana bukatar gagarumin gyara kan kiyasin. Dukkanninmu muna son cigaba, mu fi yadda muke a yanzu.

Kuma ba shakka za mu iya samun cigaban idan mun kokarta. Amma dai abin shi ne, ba ta hanyar maganar samun wani bangare na kwakwalwarmu da za a ce ba ma amfani da shi ba ne za mu kai ga wannan cigaba ba.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa na. Do we only use 10% of our brains?