Ka san dabarun samun tukuici mai yawa?

Hakkin mallakar hoto Getty

Masu aiki a otal da sauran masu ayyukan hidima da mu'amulla da jama'a za su iya gano dabarun samun tukuici mai yawa daga waɗanda suke yi wa hidima idan suka yi nazarin mujallun kimiyyar tunanin ɗan adam.

Claudia Hammond ta yi nazari

Wata rana na gamu da gamona a wani kantin cin abinci a Mahattan saboda na ba da tukuicin da a al'adar Burtaniya ba karamar kyautatawa ba ce, amma kuma a Amurka ba ta kai komai ba.

Abu ne fitacce cewa al'adar tukuici ta bambanta daga kasa zuwa kasa, amma anya kuwa idan da za a bincika mujallun kimiyyar tunanin dan adam ba za a gano dabarun yadda za ka sa mutane su ba ka tukuici mai yawa kan irin abin da suka saba bayarwa ba?

Kamata ya yi a ce ingancin abin da aka yi ko jin dadin abin da aka yi wa mutum ne zai sa ya bayar da tukuici mai yawa, to amma nazarin da aka yi a kan wasu kasidu na bincike guda 14 an gano cewa ba kasafai mutane ke ba da tukuici mai yawa saboda kawai jin dadin abin da aka yi musu ba.

Akwai wasu abubuwan da ke sa hakan. Wani nazari da aka yi a 1975 a kan wani gidan cin abinci ya nuna cewa idan mutanen da suka je cin abinci wurin tare suna da yawa to tukuicin da suke bayarwa ba shi da yawa.

Bibb Latane, masanin tunanin dan adam din da ya yi binciken nan da ke nuna yadda idan mutane suna da yawa a inda wani mummunan abu ya faru a kan wani mutum ba kasafai mutumin da abin ya faru a kansa wanda yana bukatar taimako ba, yake samun taimakon daga mutanen.

Saboda kowanne daga cikinsu na ganin ai wani daga cikinsu zai yi taimakon, shi ba sai ya yi ba, a karshe sai ka ga mutumin bai samu taimakon ba, domin kowanne yana ganin wani ya dauke masa wannan nauyi, sai mutumin ya tashi a tutar babu. Masanin ne ya sake yin wannan bincike.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kudin tukuici

Haka shi ma lamarin yake a gidan cin abinci, inda kowanne daga cikin mutanen da suka je cin abincin tare (idan suna da yawa), wannan zai ce ai dan uwansa zai bayar da tukuicin, a karshe sai ka ga wanda za a ba wa tukuicin ya tashi a tutar babu.

To sai kuma a wani lokacin abin yana dogara ne ga irin gidan abincin da mutum yake aiki. Wani bincike da aka yi a International House of Pancakes a Columbus da ke Ohio, masu cin abincin ba su bayar da tukuici mai yawa ba, inda suka bayar da kashi 11 cikin dari idan aka kwatanta da mutanen da suka je su kadai inda su kuma suka bayar da kashi 19 cikin dari.

Amma kuma a wani gidan cin abincin wanda ba shi da nisa da wannan mai suna Smuggler's Inn, mutanen da suka je a tare tukuicin da suka bayar ya kai na wanda daidaikun mutane da na mata da miji ko saurayi da budurwa suka bayar.

Sannan kuma akwai wani dalilin da ake ganin zai iya sa mutanen (masu yawa) da suka je gidan cin abinci tare ba sa bayar da tukuici mai yawa, wanda shi ne tunanin rarraba dawainiya a tsakaninsu. Wato wannan ya bayar wannan ma ya bayar, to amma kuma idan ka hada gaba daya sai ka ga ba shi da yawa.

Masu aikin ba da abinci a otal ko gidan cin abinci ba za su iya rage ko kara yawan mutanen da suke zuwa a tare domin cin abinci ba (domin idan 'yan kadan ne za su fi ba su tukuici), amma akwai dabarun da za su iya amfani da su ta yadda za su sa mutanen su ba su tukuici mai yawa.

Wani nazari da aka yi a wani otal a birnin Seattle na Amurka a 1978, an gano cewa yi wa mutumin da ya je cin abinci ko shan barasa ko wani abu murmushi kadai zai iya sa mutumin ya ba ka sama da linkin abin da ya yi niyyar ba ka tukuici. Amma fa idan har kana son wannan dabara ta yi aiki sai in har murmushin ya nuna na gaskiya ne.

Haka kuma a wani nazarin da aka yi a wani gidan cin abincin mai suna Charlie Brown's a kudancin birnin California na Amurka, inda aka sa rabin masu aikin kai wa baki abinci da su gabatar wa da baki kansu ta hanyar faden sunansu, rabin kuma ka da su fadi sunansu, an gano cewa wadanda suka gabatar da sunan nasu sun samu tukuici kashi 23 cikin dari su kuwa wadanda ba sa faden sunans sun samu tukuici 15 cikin dari.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Al'adar tukuici ta bambanta daga ƙasa zuwa ƙasa, amma akwai dabarun sa mutum ya bayar da tukuicin da yawa da ka iya tasiri a ko'ina

Yanayin biyan kudi ma a gidan abinci kan iya yin tasiri a yawan tukuicin saboda mutane sun fi bayar da tukuici da katin banki. Idan kana aiki a gidan a binci to kafin ka karfafa wa masu zuwa wurinku cin abinci guiwar yin hakan, sai ka tabbatar idan ya ba da tukuicin ta hanyar amfani da katin bankinsa wanda kudin zai je ga masu otal din, to sai ka tabbatar wadanda kake yi wa aikin suna ba wa ma'aikatan nasu kudin.

A 'yan shekarun nan an jarraba wasu dabaraun na samun karin tukuici. Wasu masana tunanin dan adam biy 'yan Faransa Nicolas Gueguen da Celine Jacob sun gudanar da da bincike da dama a kan tukuici.

A daya daga ciki sun gano cewa idan mace mai aikin kai abinci a otal ta sa rigar shat (shirt) mai launin ja, hakan ba ya haifar da wani bambanci ko tasiri a kan masu zuwa cin abinci mata wajen bayar da tukuici, amma kuma hakan yana sa maza su ba da tukuici mai yawa.

Wannan ba shi ne karon farko da ake ambato tasirin jinsi a kan nazari game da bayar da tukuici ba. Misali an yi amanna idan me aikin kai abincin mace ce, sai ta yi zanen fuskar mutum na murmushi a kan rasitin kudin abincin da mutum zai biya ko kuma ta rubuta na gode a bayan rasitin, hakan na sa mata ma'aikata su samu tukuici mai yawa, amma idan maza ne ba sa samu.

Farfesa Michael Lynn, (masani a kan dabi'un masu sayen abubuwa) wanda ya yi bincike da rubuce-rubuce da dama a wannan fage ya nuna cewa murmushi ba lalle ya yi tasiri wajen samun tukuici mai yawa ba a wurin masu zuwa cin abincin dare a otal.

Maimakon hakan ya bayar da shawarar yin zanen kaguwa (wadda wasu ke sha'awar ci sosai) a jikin rasitin biyan kudin abincin domin hakan zai fi sa mutum ya ba da tukuici mai yawa.

Ba shakka wannan ina ganin wani kalubale ne ga wani mai hidimar kai wa baki abinci a otal. Haka kuma za ka iya sanya kati dauke da wani rubutu na barkwanci a jikinsa tare da rasitin kudin abincin, wanna ma zai iya sa ka samu tukuici mai yawa.

Za kuma ka bar maganar amfani da rasitin ka mayar da hankalinka kan irin kwano ko tangaran din da za a zuba wa mutum abinci, ta yin amfani da mai siffar zuciya maimakon wata siffa, domin mai alamar zuciya ya fi jan hankali ka samu tukuici mai yawa.

Idan kana jin jarumta, Gueguen da Jacob sun gano cewa dan taba mutum a hannu zai iya sa mutum ya ba ka tukuici mai yawa. Wani bincike da aka yi a shekarun 1980 ya gano cewa idan ka nemi wani ya yi maka wani aiki, zai iya yarda ya yi idan ka dan taba shi a hannu.

Ko kudi kake son ya ba ka rance ko aron wani abu ko sanya maka hannu a wata takarda, za ka ga ba tare da wani bata lokaci ba mutumin ya amince.

Dan taba mutum da za ka yi na nuna cewa kai mutum ne mai kirki kuma ka mayar da hankalinka gaba daya a kansa

A binciken da aka yi a Faransa inda wasu mutane ke zaune su kadai a wata mashaya a garin Vannes, a gabar tekun Brittany. A wannan rana kashi goma cikin dari ne kawai na mashayan suka bayar da wani dan tukuici ga ma'aikatan wurin.

Amma kuma an gano cewa a yayin da ma'aikaciya ta dan taba hannun mutumin da ya zo mashayar a lokacin da take tambayarsa abin da yake bukata ya sha, yawan tukuicin an gano ya karu zuwa kusan kashi 25 cikin dari.

Ina ma a ce na san duka wadannan dabaru a lokacin da nake aikin bayar da abinci a otal.

Saboda haka idan ka je wani otal ko gidan cin abinci sai ka lura me kawo maka abincin tana sanye da riga mai launin ja sannan ta gabatar da kanta ta hanyar fada maka sunanta sannan ta kalle ka, kana ta dan taba ka a hannu lokacin da ta kawo maka rasitin kudin abin da ka sha ko ka ci a dan wani faranti mai siffar zuciya tana maka murmushi tare da wani dan barkwanci da ta rubuta a jikin rasitin, watakila ta yi nazarin wannan rahoton ne.

Ba shakka babu wani gwaji da aka yi na nazarin dukkanin wadannan dabaru a lokaci daya, ko za a ga tasirin karin yawan tukuici na kashi biyu bisa dari a nan da kashi hudu bisa dari a can.

Duk da cewa matsalar wadannan bincike-bincike an yi su ne a yanayi na gwaji kuma za a iya aiwatar da su a yanayi na gaske a gidajen sayar da abinci, to amma ba abu ne mai yuwuwa ba ka hana sanin ma'aiakatan gidan abincin sanin yanayin da suke ciki na gwajin da ake yi da su.

Saboda haka sun san abin da ake so su yi shi ne su yi wa mai sayen abincin murmushi ko su dan taba shi a hannu, wanda hakan zai iya jan hankalin wanda ya je sayen abincin, abin da zai sa me aikin otal din samun tukuici mai yawa.

Duk da haka na so ace na san wasu daga cikin wadannan dabaru a lokacin da nake aikin gidan sayar da abinci. Sau daya na taba samun tukuicin fan 20 saboda na ba wa wasu iyaye dan wani farfesu kadan su dan taba bayan da dansu ya ki yarda su sha nashi. To amma wannan ba abu ne da za a ce zan samu ba a kodayaushe.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa na. The mind tricks to get better tips