Ba za mu sayar da Aguero ba - Man City

Sergio Aguero Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sergio Aguero ya ci wa Manchester City kwallo 18 a bana

Manchester City ba ta da niyyar sayar da Sergio Aguero a bazara, duk da cewa kungiyar ba ta sanya dan wasan ba a wasanninta biyu da ta yi na karshe.

A farkon kakar wasannin da ake ciki ne dan wasan mai shekara 28 ya tsawaita kwantiraginsa da kungiyar zuwa karin wasu shekaru uku.

Bayan da aka yi canji aka sa shi a wasan da City ta ci Swansea 2-1, Aguero ya ce: ''Ba shakka ina son tsayawa a kungiyar.

''A wadannan watanni uku masu zuwa zan taimaka wa kungiyar, to daga nan sai su duba su gani, idan ina da gurbi ko ba ni da shi a kungiyar.''

Duk da cewa Aguero yana sa ran a yanke shawara a kansa a lokacin kasuwar saye da sayar da 'yan wasa ta bazara, manyan jami'an kungiyar ta Manchester City, a ranar Lahadi sun nuna cewa ba su da niyyar sayar da shi a lokacin.

A mintina bakwai na karshe ne na wasan da City ta ci Swansea, aka sanya dan wasan na Argentina.

Gabriel Jesus ne, wanda ya maye gurbin Aguero a cikin fitattun 'yan wasan kungiyar 11, ya ci wa City din kwallon da ta ba ta nasara a wasan, a cikin mintina na karshe na wasan da Swansea.

Sharhi:

A bana Aguero din shi ne dan wasan da ya fi ci wa Man City kwallo, inda ya ci mata 18, ya zarta Raheem Sterling na biyu, da kwallo 11.

Dan wasan ne na uku a cikin jerin wadanda suka fi ci mata kwallo a tarihi, inda yake da kwallo 154, kuma shi ne ya ci kyautar dan wasan da ya fi cin kwallo a Premier a kakar 2014-15.

Haka kuma shi ne ya fi ci wa City kwallo a kakar 2011-12, lokacin da suka dauki kofin Premier, inda ya ci kwallon da ta ba su nasara a kan Queens Park Rangers, dab da tashi daga wasan, wadda kwallo ce da ta yi fice a lokacin.