Jurgen Klopp ne ya sa na zama yadda nake yanzu — Mkhitaryan

Henrikh Mkhitaryan Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Henrikh Mkhitaryan da Jurgen Klopp na tare a Borussia Dortmund

'Dan wasan Manchester United, Henrikh Mkhitarya ya yaba wa kocin Liverpool, Jurgen Klopp kan rawar da ya taka a kansa a lokacin da suke a Borussia Dortmund, a 2013.

A kakar bana, Mkhitaryan bai yi wasa na tsawon watanni 10 ba amma kuma yana tuna shawarwarin da Klopp ya ba shi cewa a har kullum ya zama mai kwazo da jajircewa.

Mkhitaryan mai shekara 28, ya ce "Ina matukar godiya ga Klopp. Ya taka rawa a yanayin tunanina''.

Dan wasan wanda dan Amurka ne, ya yi aiki a karkashin Klopp tsawon kakar wasanni biyu, a Jamus, kafin shi Jurgen din ya dawo Liverpool a watan Oktoban 2015.

A cikin watanni takwas, 'dan wasan na bin tsohon kocin shi zuwa gasar Premier, a inda kuma yake karbar labashin da yawansa ya kai Euro milliyan 26.3.