Zakarun Turai: Tarihin haduwar PSG da Barcelona

Wata haduwa da PSG ta karbi bakuncin Barcelona a Paris, a gasar Zakarun Turai Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Barcelona ta doke PSG a wasa uku da suka yi na karshe a gasar Zakarun Turai

Paris St-Germain za ta karbi bakuncin Barcelona a ranar Talatar nan a wasan karon farko na zagayen kungiyoyi 16, na cin Kofin Zakarun Turai.

PSG ta samu karin kwarin guiwa na fuskantar wasan sakamakon dawowar dan wasanta na tsakiya Marco Verratti, wanda ya dawo daga jinya.

Dan wasan dan Italiya ya yi wasan sa'a daya a ranar Juma'a da suka doke Bordeaux 3-0.

Amma kuma dan wasansu na tsakiya Thiago Motta, ba zai yi wasa ba saboda an dakatar da shi, yayin da shi kuwa Javier Pastore ba zai buga wasan ba ne saboda rauni da ya yi.

Su kuwa Zakarun Spaniya, ana sa ran za su yi wasan da dan bayansu Gerard Pique, wanda ake ganin ya samu sauki daga jinyarsa, amma kuma sun rasa Aleix Vidal, wanda ya tafi jinyar wata biyar.

Kungiyoyin biyu sun hadu a wasan dab da na kusa da karshe a 2015, inda Barcelona ta yi nasara da jumullar kwallo 5-1, gida da waje.

Haka kuma Zakarun na La Liga sun yi nasara a kan Zakarun na Faransa a bisa tsarin bambancin kwallon da kungiya ta ci a waj, a shekara 2013.

Tarihin haduwar PSG da Barcelona

Barcelona ta doke PSG a wasa uku da suka yi na karshe, inda ta zura kwallo 8, aka jefa mata biyu a raga.

A duk haduwar da suka yi, sau tara, a kowace gasa sai Barcelona ta jefa kwallo a ragar Zakarun na Faransa.

Kungiyar ta Faransa ta yi rashin nasara ne a wasanta na gida daya kawai daga cikin 42 na karshe a gasar Kofin Zakarun Turai, inda ta yi nasara a 26, kuma ta yi canjaras a 15.

Wasan daya da aka ci ta a gidan shi ne, wanda Barcelona ta doke su 3-1 a wasan dab da na kusa da karshe, a watan Afrilun 2015.

Edinson Cavani ya ci wa PSG kwallo 6 a gasar Kofin Zakarun Turai a bana, wanda hakan ya zama daidai da yawan kwallon da ya ci a gasar a kakar 2014-15.

Sai dai kuma a duk wasan da ya buga jumullar minti 350, a haduwarsu daban-daban da Barcelona a gasar ta Zakarun Turai bai taba cin kwallo ba.

Lionel Messi ya ci kwallo 10 a gasar ta Zakarun Turai ta wannan kakar ta 2016-17, a wasannin rukuni-rukuni.

Hakan ya sa ya zama na biyu da ya fi cin kwallo a gasar a matakin rukuni-rukuni a tarihi, inda yake bayan Cristiano Ronaldo mai yawan kwallo 11 a bara.

Neymar ya zura kwallo biyar a wasa hudu da suka yi da PSG, wanda hakan shi ne lokacin da ya ci kwallo mafi yawa a gasar ta Kofin Turai.

Haka kuma shi ne dan wasan da ya fi taimakawa wajen bayar da kwallo a ci a bana, inda ya bayar aka ci kwallo sau bakwai.