Armstrong zai fuskanci tuhumar dala miliyan 100

Lance Armstrong ya shiga tsaka-mai-wuya, saboda samunsa da laifin amfani da abubuwan kara kuzari Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A 2012 aka karbe lambobin bajinta 7 da Lance Armstrong ya ci a gasar tseren keke ta Faransa

Zakaran tseren keke na duniya wanda aka haramta wa wasa har abada, Lance Armstrong, ya yi rashin nasarar hana gwamnatin Amurka gurfanar da shi gaban shari'ar tuhumarsa dala miliyan 100.

A tuhumar, gwamnatin Amurka ta zargi tsohon dan tseren da zambatarta, saboda ya yi amfani da abubuwan kara kuzari, a lokacin da yake yi wa gidan wasika na Amurka, tsere.

Tsohon abokin tseren Armstrong Floyd Landis, shi ne ya shigar da karar, kafin daga bisani gwamnatin Amurka, ita ma ta mara masa baya, a 2013.

Wani alkalin tarayya ne ya ki dakatar da karar a ranar Litinin, wanda hakan ya bayar da damar a cigaba da ita.

A watan Agusta na 2012 ne, aka kwace lambobin bajinta 7 da Armstrong ya ci na gasar tseren keke ta Faransa, kuma aka haramta masa shiga tseren keke har abada.

Armstrong mai shekara 45, ya ci lambobin ne tsakanin 1999 da 2005.

Hukumar gidan wasikar Amurkan ta dauki nauyin tawagar tseren keken da Armstrong ke ciki ne tsakanin 1996 da 2004.

A watan Janairu na 2013 ne Armstrong ya amsa cewa ya yi amfani da abubuwan kara kuzari a dukkanin gasar da ya ci ta Faransa 7.

Shi kuwa Landis an karbe masa lambar da ya ci ta tseren gasar Faransa ta 2006 ne, saboda shi ma, an gano ya yi amfani da abubuwan kara kuzari.