Fifa : Za mu yi maganin masu rikici

Wani daga cikin 'yan kungiyar da ke tayar da rikici a filin a wasa a Rasha
Image caption Tayar da hankali abin alfahari ne ga 'yan kungiyar Orel Butchers, masu rikici a filin wasa a Rasha

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, Gianni Infantino ya ce, ko alama bai damu da barazanar tayar da hankali a gasar cin Kofin Duniya ta shekara mai zuwa a Rasha ba.

Shugaban ya ce yana da cikakken kwarin guiwa a kan hukumomin Rasha cewa za su iya maganin duk wani rikici a lokacin gasar, yana mai karin bayani da cewa, duk da haka su ma sun dauki lamarin da muhimmanci sosai.

Shugaban, kusan yana mayar da martani kan wata magana da wani dan kallo na Rasha ya yi ne, a wani bangare na wani shirin BBC na talabijin, da za a nuna ranar Alhamis, inda mutumin yake cewa, '' tabbas ba makawa, za a yi rikici a gasar cin kofin duniya ta 2018.

A gasar cin kofin kasashen Turai ta 2016, an samu mummunan artabu tsakanin magoya bayan Rasha da na Ingila a birnin Marseille.

Infantino ya ce masu shirya gasar ta cin Kofin Duniya, tuni sun fara daukar matakan kare aukuwar duk wani rikici a gasar ta badi.

Kuma za su dauki darasi daga abin da ya faru a gasar cin Kofin Turai ta 2016.