Ina jin dadin zuwana China— Mikel Obi

John Mikel Obi
Image caption John Mikel Obi zai rika karbar albashin sama da naira miliyan 55 a duk sati, tsawon shekara uku

Tsohon dan wasan Chelsea, John Mikel Obi ya ce tuni har ya fara jin dadin wasansa a kungiyar da ya koma ta China.

Kyafitin din na tawagar Super Eagles ta Najeriya, ya ce a yanzu ya saki jikinsa kuma ya mike kafarsa a kungiyar ta Tianjin TEDA.

Mikel, wanda a watan Janairu ya kulla yarjejeniyar shekara uku kan albashin fan dubu 140 (naira miliyan 55 da dubu 440) a duk sati da kungiyar ta babbar gasar China ya ce ya gamsu da yadda kungiyar take.

Kuma ya ce kusan yanayin atisaye da horon da ake yi a kungiyar daidai yake da wanda ya baro a Stamford Bridge.

Mikel mai sheakara 29, ya tafi kungiyar Tianjin din ne bayan shekara 10 a Chelsea, domin bunkasa kungiyar wadda, tsohon dan wasan Portugal, Jaime (Jaimi Paaceko) Pacheco ke yi wa koci.

Obi wanda tsohon dan wasan kungiyar Lyn ta Oslo a Norway ne ya yaba da irin kokarin kocin wanda ya ce yana da basira, kuma kwararren dan wasa ne.