Deportivo ta nada Pep Mel kocinta

Pepe Mel Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Pepe Mel ya yi wa West Brom koci daga watan Janairu zuwa Mayu na 2014

Kungiyar Deportivo La Coruna da ke neman tsira a gasar La Liga ta Spaniya ta nada tsohon kocin West Brom Pepe Mel a matsayin kocinta.

A ranar Asabar ne kungiyar ta kori kocinta Gaizka Garitano bayan da kungiyar ta sha kashi a karo na hudu a jere a gasar ta Sapaniya.

Mel, mai shekara 54, ya jagoranci West Brom ne a wasanni 17 kadai a shekara ta 2014, kuma tun lokacin da Real Betis ta kore shi a watan Janairun 2016 bai sake yin wani aiki ba.

Yanzu dai maki biyu ne tsakanin Deportivo, wadda ta dauki kofin La Liga a 2000, daga rukunin faduwa daga gasar, kasancewar rabonta da cin wasa tun watan Disamba.

Pepe Mel shi ne koci na bakwai da kungiyar ta yi a shekara shida, kuma zai jagorance ta ne zuwa karshen kakar wasan da ake ciki kawai.