Aguero ya ci Liverpool karo na 5 a jere a Premier a Ettihad

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Karo na biyar kenan Aguero ke cin Liverpool a Ettihad

Manchester City da Liverpool sun raba maki dai-daya a tsakaninsu, bayan da suka tashi wasa kunnen doki 1-1 a gasar Premier mako na 29 da suka yi a ranar Lahadi.

Liverpool ce ta fara cin kwallo ta hannun James Miller a bugun fenareti kuma kwallo na bakwai kenan da ya ci a bugun daga kai sai mai tsaron raga a kakar Premier nan.

Manchester City mai masaukin baki ta farke ta hannun Sergio Aguero, wanda karo na biyar kenan yana cin Liverpool a filin Ettihad.

Da wannan sakamakon Manchester City tana mataki na uku a kan teburin Premier da maki 57, yayin da Liverpool ke matsayi na hudu da maki 56.