Benzema ya ci wa Madrid kwallaye 119

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Benzama ya fara buga wa Real Madrid a ranar 29 ga watan Agustan 2009

Karim Benzema ya shiga jerin 'yan wasa 10 da suke kan gaba a yawan ci wa Real Madrid kwallaye.

Dan kasar Faransa ya ci kwallonsa na 119 a karawar da Real Madrid ta doke Athletic de Bilbao 2-1 a ranar Asabar a wasan gasar cin kofin La Liga mako na 28.

Benzema wanda ya buga wa Real wasannin League 237 ya yi kan-kan-kan da Amancio a yawan ci wa kungiyar kwallaye.

Dan kwallon ya fara yi wa Madrid wasa a ranar 29 ga watan Agustan 2009 a karawar da ta yi da Deportivo a fafatawar da suka yi a Bernabéu.

A cikin shekara takwas da Benzema ya yi a Real Madrid ya lashe kofunan zakarun turai biyu da kofin duniya na zakarun nahiyoyi biyu da UEFA Super Cup biyu.

Haka kuma dan wasan ya dauki La Liga daya da Copa del Rey da kuma Spanish Super Cup.

Ga jerin 'yan wasan Madrid da suke kan gaba a yawan cin kwallaye:

  1. Cristiano Ronaldo (280)
  2. Raúl (228)
  3. Di Stéfano (216)
  4. Santillana (186)
  5. Hugo Sánchez (164)
  6. Puskas (156)
  7. Gento (126)
  8. Butragueño da Pirri (123)
  9. Amancio Amaro da Karim Benzema (119)