Adam Lallana zai yi jinyar wata daya

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Lallana ya buga wa tawagar kwallon kafa ta Ingila wasanni 31

Dan kwallon Liverpool, Adam Lallana, zai yi jinyar wata daya, sakamakon raunin da ya yi a lokacin da ya buga wa Ingila wasa.

Lallana mai shekara 28, shi ne ya bai wa Jamie Vardy kwallon da ya ci Lithuania ta biyu a karawar da Ingila ta ci 2-0 a wasan neman shiga gasar cin kofin duniya.

Dan wasan ya buga wa Liverpool wasa 27 daga 29 da ta buga a gasar cin kofin Premier ta shekarar nan.

Ba a sanar da ranar da Lallana zai murmure ba, watakila ba zai buga wa Liverpool karawa biyar ba.

Liverpool za ta karbi bakuncin Everton a wasan gasar Premier a ranar Asabar.