David Moyes ya bai wa wakiliyar BBC hakuri

David Moyes, kociyan Sunderland Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kocin Sunderland David Moyes ya ce ya yi nadamar kalamansa ga wakiliyar BBC Vicki Sparks

Kocin Sunderland David Moyes, ya ce ya yi nadama matuka da kalaman da ya yi wa wata wakiliyar BBC, inda ya ce da ita za ta iya shan mari, idan bata yi a hankali ba.

Hakan ya biyo bayan wasan da Sunderland ta yi da Burnley ranar 18 ga watan Maris, wanda suka tashi kunnen doki, a inda wakiliyar BBC Vicki Sparks, ta tambayi Moyes ko zuwan da Ellis Short ya yi, mamallakin kulob din, ya kara sa shi cikin tsaka mai wuya?

Moyes ya amsa mata da a'a, amma kuma bayan sun kammala hirar tasu, sai ya ce da ita gara ta rika yi a hankali, ta bar ganin ita mace ce, don wataran za ta sha mari.

"Ina cikin wani yanayi na bacin rai ne a lokacin," in ji Moyes.

Tsohon kocin na Everton da Manchester United dai ya bai wa Misis Sparks hakuri daga baya, inda ya ce ya matukar da na sanin fadin wadannan kalaman nasa.

Labarai masu alaka