Manchester United ta doke Sunderland da ci 3-0

Zlatan Ibrahimovic Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Zlatan Ibrahimovic ya ci kwallaye 17 a gasar ta Premier a bana, dai-dai da Diego Costa na Chelsea

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta yi nasarar doke Sunderland da ci 3-0 a karawar da suka yi ranar Lahadin nan, a gasar Premier ta Ingila.

Sunderland ta buga wasan ne da 'yan wasa goma har na tsawon minti 45, bayan an ba dan wasanta Sebastian Larsson jan kati mai cike da takaddama, sakamakon keta da yayi wa Ander Herrera.

Zlatan Ibrahimovic ne ya fara ci wa Manchester United kwallo kafin a tafi hutun rabin lokaci, yayin da Henrikh Mkhitaryan ya ci ta biyu, Marcus Rashford kuma ya ci ta uku bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Manchester United ta matsa mataki na biyar yanzu a teburin Premier, waanda hakan ya sa ta shiga gaban Arsenal.

Maki hudu ne ke tsakanin United da Manchester City wacce ke mataki na hudu a teburin.