Kun san 'yan wasan da suka fi kwarewa a gasar Premier

Jerin 'yan wasan da suka fi kwarewa a gasar Premier ta bana
Image caption Jerin 'yan wasan da suka fi kwarewa a gasar Premier ta bana

Kungiyan kwararrun 'yan wasan gasar Premier ta zabi 'yan wasa huda daga Chelsea da Tottenham a don shiga jerin wadanda suka fi kwarewa a gasar ta bana.

An zabi Gary Cahill da David Luiz da N'Golo Kante da kuma Eden Hazard daga Chelsea.

A Tottenham kuwa an zabi Kyle Walker da Danny Rose da Dele Alli da kuma Harry Kane.

An kuma zabi David de Gea daga Manchester United da Sadio Mane daga Liverpool da kuma Romelu Lukaku daga Everton.

An kuma sanar da jerin gwarazan 'yan wasa na gasar League kafin bikin bayar da lambar yabo karo na 44 wanda za a gudanar a birnin London a ranar 23 ga watan Afrilu.

Za kuma a bayyana wanda ya samu lambar yabo ta gwarzon dan kwallon Premier na bana a taron.

Mambobin kungiyar kwararrun 'yan wasa 100 za su zabi wadanda za su samu lambar yabon daga gasar Premier da ta Football League da kuma gasar Supar League ta mata.

Labarai masu alaka