Swansea na zawarcin John Terry

John Terry a wasan Chelsea Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tsohon dan wasan bayan na Ingila John Terry zai bar Chelsea a karshen kakar nan

Kociyan Swansea City Paul Clement ya ce zai tattauna da kyaftin din Chelsea John Terry, ko zai amince su dauke shi idan ya kammala zamansa a kungiyar a bana.

Tsohon kyafin din Ingila Terry, mai shekara 36, zai bar zakarun na Premier a karshen kakar nan.

Terry yana kyaftin ya jagoranci Chelsea ta dauki kofin FA da na Premier duka biyu a kakar farko da Clement ya je kungiyar a matsayin mataimakin tsohon kocinta Carlo Ancelotti a kakar 2008-09.

Clement ya ce bai san abin da Terryn ya tsara ba ko zai ci gaba da taka leda ko zai yi ritaya gaba daya, amma zai zai tattauna da shi, domin ya san shi da dadewa.

A shekarar 1998 Terry ya fara buga wa babbar kungiyar Chelsea wasa, kuma wasan Lahadi da za su yi a gida da Sunderland ka iya kasancewa wasansa na karshe a kungiyar.

Abokan hamayyar Swansean a Premier Bournemouth suma wasu rahotanni na cewa suna sha'awar dan wasan idan har zai ci gaba da wasa.

A wani labarin kuma tsohon dan wasan tsakiya na Faransa da Chelsean Claude Makelele zai kulla yarjejeniyar zama daya daga cikin masu horad da 'yan wasan Swansean na dindindin.

Kungiyar ta dauko tsohon dan wasan mai shekara 44 ne ya yi aiki da ita zuwa karshen kakar nan, bayan da ta kawo Clement a watan Janairu, amma kuma yanzu za ta kulla yarjejeniyar tsawon lokaci da shi.