Conte ne kocin da yafi yin fice a bana

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Chelsea za ta kara da Arsenal a gasar cin kofin FA a ranar Asabar

Kocin Chelsea Antonio Conte ne ya lashe kyautar gwarzon mai horar da tamaula da yafi fice a kakar bana.

Conte dan kasar Italiya ya lashe kyautar da kungiyar masu horar da tamaula a Ingila ta ba shi, bayan da ya lashe kofin Premier a kakar farko da ya ja ragamar Chelsea.

Chelsea wadda ta lashe kofin Premier da bajintar cin wasa 30 za ta fafata da Arsenal a wasan karshe a kofin FA a Wembley.

Kocin Brighton, Chris Hughton shi ne aka zaba wanda babu kamarsa a Championship, bayan da ya kai kungiyar gasar Premier da za a yi a badi.