Toure zai taimakawa wadanda harin Manchester ya shafa

Manchester City Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Manchester City ta kare a mataki na hudu a kan teburin Premier ta shekarar nan da aka kammala

Dan kwallon Manchester City Yaya Toure tare da mai kula da harkokin wasansa za su bayar da taimakon fam 100,000, domin taimakawa wadanda harin Manchester Arena ya rutsa da su.

Mutane 22 ne suka mutu sannan 64 suka yi rauni a lokacin da Salman Abedi ya tashi dam din da yake dauke da shi a yayin da Arande Girande ta gama kade-kade a ranar Litinin.

Dimitri Seluk ya shaida wa BBC cewar 'Suna son taimakawa iyalan wadanda suka mutu da wadanda ke yin jinya a asibiti.

Seluk ya kara da cewar "Za su yi aiki tare da kamfanin Manchester Evening News wanda zai taimaka musu wajen raba kudin ga wadanda suka dace".

Ya kuma ce za su yi hakan ne domin kudin ya kai ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su, ba tare da sun yi batan dabo ba.